Rahotannin Hidimar Fage
Muna farin cikin sanin cewa masu shela 65,456 ne suka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Afrilu. Idan an daɗa majagaba na kullum guda 31,488 da majagaba na musamman guda 810 da suka ba da rahotonsu a watan da adadin da aka ambata a sama, za mu lura cewa kashi 32 cikin ɗari na masu shela ne suka yi hidimar majagaba. Hakan yana da ban sha’awa sosai! Wannan ya nuna cewa Jehobah yana yi wa mutanensa albarka yayin da suke saka hannu a cika annabce-annabce kamar wanda ke littafin Ishaya 12:3-5.