Tsarin Ayyuka na Makon 10 ga Oktoba
MAKON 10 GA OKTOBA
Waƙa ta 44 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 67 zuwa 70 (minti 25)
□ Makarantar Hidima Ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Misalai 7-11 (minti 10)
Na 1: Misalai 8:1-21 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Za Ka Iya Gane Annabawan Ƙarya?—td 4A (minti 5)
Na 3: Dalilin da Ya Sa Nassosi Suka Yi Gargaɗi Game da “Cika Yin Adalci”—M. Wa. 7:16 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 134
Minti 5: Sanarwa. Ka tattauna “Rahotannin Hidimar Fage” da ke shafi na 8. Ka yaba wa ikilisiyar don ƙwazonsu a hidimar fage a watan Afrilu.
Minti 15: Ka Taɓa Gwada Su Kuwa? Tattaunawa. Ta wajen ba da jawabi, ka ɗan taƙaita bayanai da suke cikin waɗannan talifofin Hidimarmu Ta Mulki: “Za Ka Iya Fita Wa’azi a Ranar Lahadi Kuwa?” (km 5/11) da “Wa’azi a Kan Titi Mai Ba da Amfani” (km 6/11). Ka gayyaci masu sauraro su yi kalami a kan yadda suka yi amfani da shawarwari da ke cikin waɗannan talifofin da kuma yadda suka amfana.
Minti 15: “Ka Taimaki Mai Gidan Ya Yi Tunani.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Bayan ka tattauna sakin layi na 3, ka sa a yi gwajin da ya nuna yadda mai shela yake amfani da baƙar magana don amsa tambayar da aka masa. Ka kuma sa a gwada yadda ya amsa tambayar cikin basira.
Waƙa ta 102 da Addu’a