Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 9/11 p. 4
  • Sanarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sanarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 9/11 p. 4

Sanarwa

◼ Littafin da za a ba da a watan Satumba: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a ziyara ta fari. Idan masu gidan sun riga sun samu littafin kuma ba su amince da nazarin Littafi Mai Tsarki ba, masu shela suna iya ba da tsofaffin mujallu ko kowacce ƙasida da ke tattauna abin da mai gidan ke so. Oktoba: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Ku ba da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? a inda ake son saƙonmu kuma ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da masu gida. Nuwamba: Ƙari ga ko maimakon ƙasidar nan Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo ne Ke Cikinsa? Za ku iya ba da kowace ƙasida mai shafi 32 da aka ambata a Hidimarmu Ta Mulki ta watan Agusta 2011. Disamba: The Greatest Man Who Ever Lived. Idan akwai yara a gidan, ku ba da littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami ko Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki.

◼ Za a ba da jawabi na musamman na Tuna Mutuwar Yesu na 2012 a makon 2 ga Afrilu. Za a sanar da jigon jawabin a nan gaba. Kada kowacce ikilisiya ta ba da jawabin kafin ranar Tuna Mutuwar Yesu.

◼ Masu shela da suke hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Maris 2012 za su zaɓa ko za su ba da rahoton sa’o’i 30 ko 50 a watan. Ƙari ga hakan, idan mai kula da da’ira zai ziyarce ikilisiyar ku a watan Maris, dukan waɗanda suke hidimar majagaba na ɗan lokaci, ko na sa’o’i 30 ko na 50, za su halarci gabaki ɗaya sashen taro da mai kula da da’ira zai yi da majagaba na kullum.

◼ A watan Satumba, masu kula da da’ira sun soma ba da wannan jawabi ga jama’a mai jigo “Ka Haɗa Kai da Mutanen Allah Masu Farin Ciki.”

◼ Muna son mu tunasar da ku cewa, kada ku taɓa yin amfani da adireshin ofishin reshe sa’ad da kuke rubuta wasiƙa ta kanku. Wannan ya haɗa da dukan wasiƙu da littattafai da aka aika don ba da shaida ga masu son saƙonmu ko waɗanda ba sa gida ko kuma waɗanda suke zama a wuraren da mutane ba sa iya shiga. Mai shela zai iya yin amfani da adireshinsa, tun da hidimarsa ta ƙunshi ibadarsa ga Allah. (Mat. 28:19, 20; Rom. 10:14, 15) Amma dai, idan mutum yana ji cewa ba zai dace ya yi amfani da adireshinsa ba sa’ad da yake ba da shaida ta wasiƙa, zai iya yin amfani da sunansa da kuma adireshin Majami’ar Mulki.—Ka duba Akwatin Tambaya a Hidimarmu Ta Mulki ta Mayu 2002 na Turanci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba