Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Agusta: Kowacce ƙasida da mutanen yankinku za su so: Allah Yana Kula Da Mu Kuwa da Gaske? da Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa (don Musulmai), da Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske? da The Divine Name That Will Endure Forever da Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa? da Was Life Created? da Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu? da Minene Ma’anar Rai? Ina Yadda Zaka Same Shi? da kuma Yayinda Wani Wanda Ka ke Ƙauna ya Mutu. Satumba: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a ziyara ta fari. Idan masu gidan sun riga sun samu littafin kuma ba su amince da nazarin Littafi Mai Tsarki ba, masu shela suna iya ba da tsofaffin mujallu ko kowacce ƙasida da ke tattauna abin da mai gidan ke so. Oktoba: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Ku ba da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? a inda ake son saƙonmu kuma ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da masu gida. Nuwamba: Ƙari ga ko maimakon ƙasidar nan Littafi Mai Tsarki —Wane Saƙo ne Ke Cikinsa? Za ku iya ba da kowace ƙasida mai shafi 32 da aka ambata a baya da za a gabatar a watan Agusta 2011.
◼ A taron hidima na gaba, za a tattauna waɗannan bidiyo biyu Jehovah’s Witnesses—Faith in Action, Part 1: Out of Darkness da kuma The Wonders of Creation Reveal God’s Glory. Idan ana bukata, za a iya yin odar su ta hanyar ikilisiya tun da wuri.