Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
Za a amsa waɗannan tambayoyi na gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 29 ga Agusta, 2011.
1. Ta yaya za mu cika alkawarin keɓe kai da muka yi? (Zab. 61:5, 8) [w10 1/15 shafi na 21 sakin layi na 4-6]
2. Mene ne Zabura sura 70 ta nuna game da Dauda? [w08 9/15 shafi na 4 sakin layi na 4]
3. Wane gargaɗi ne Zabura 75:5 ya yi mana? [w06 8/1 shafi na 29 sakin layi na 2]
4. A wane lokaci ne musamman za mu iya zata Jehobah ya amsa addu’o’inmu? (Zab. 79:9) [w06 8/1 shafi na 30 sakin layi na 5]
5. Waɗanne ‘abubuwa na ɓoye’ ne aka yi maganarsu a Zabura 90:7, 8? [w01 12/1 shafi na 10 sakin layi na 14-16]
6. Kamar yadda Zabura 92:12, 15 ta nuna, wane hakki mai muhimmanci ne aka ba wa tsofaffin da ke cikin ikilisiya? [w04 6/1 shafuffuka na 9-10 sakin layi na 14-18]
7. Yaushe muke bukatar umurnin Jehobah? (Zab. 102:17) [w08 4/15 shafi na 8 sakin layi na 6, 7]
8. Waɗanne batutuwa ne za su iya taimakawa sa’ad da ake ƙoƙarin taimaka wa mutumin da ke da wata fahimi dabam game da wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki? (Zabura 106:13) [w08 11/15 shafi na 14 sakin layi na 10-11]
9. In ji Zabura ta 110:1, 4, wane alkawari ne Jehobah ya yi game da Zuriyar da aka yi alkawarinta, ko kuma Almasihu, kuma yaya hakan zai kawo albarka ga dukan ’yan Adam? [cl shafi na 194 sakin layi na 13]
10. Ta yaya bimbinin da marubucin zabura ya yi a kan amfanin hidimarsa ga Allah ya shafe shi? (Zab. 116:12, 14) [w09 7/15 shafi na 29 sakin layi na 4-5]