Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Maris: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙari don soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Afrilu da Mayu: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Sa’ad da kuke koma ziyara wurin masu son saƙonmu, har da waɗanda suka halarci Tuna Mutuwar Yesu ko kuma wasu tarurruka na tsarin Allah amma ba sa tarayya da ikilisiyar, ku mai da hankali ga soma nazarin Littafi Mai Tsarki da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Yuni: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Idan masu gida sun riga sun samu wannan littafin, masu shela za su iya ba da tsofaffin littattafai da ikilisiyar take da su a ajiye. Ko kuma ku ba da littafin nan, Ka Bauta wa Allah Makaɗaici na Gaskiya.
◼ Za a ba da jawabi na musamman na lokacin Tuna Mutuwar Yesu na shekara ta 2011 a makon 25 ga Afrilu 2011. Jigon shi ne “Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, Za Su Iya Taimaka Mana Mu Jimre Matsalolin da ke Faruwa a Yau Kuwa?” Ikilisiyoyin da suke da ziyarar mai kula da da’ira ko kuma taro na musamman da na da’ira a ƙarshen makon za su saurari jawabi na musamman a mako na gaba. Kada kowace ikilisiya ta ba da jawabi na musamman kafin ranar 25 ga Afrilu.
◼ Za a tattauna bidiyon nan Jehovah’s Witnesses—Organized to Share the Good News a Taron Hidima a watan Agusta. Idan kuna bukatar kofofi, za ku iya yin odarsu ta hanyar ikilisiya ba tare da ɓata lokaci ba.