Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/10 p. 4
  • Akwatin Tambaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwatin Tambaya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Tuna da Masu Hidima ta Cikakken Lokaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Matasa​—Ku Zama “da Kwazon Yin Ayyukan Kirki”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 11/10 p. 4

Akwatin Tambaya

◼ A waɗanne hanyoyi ne za mu iya taimaka wa majagaba?

Kusan ’yan’uwa dubu ɗari takwas ne suka yi hidimar majagaba na kullum da na musamman a shekarar hidima ta 2009 a dukan duniya. Waɗannan bayi masu hidima ta cikakken lokaci sun sadaukar da nunan fari na lokacinsu, ƙarfinsu, da kuma dukiyarsu don yaɗa bisharar Mulki. (Mis. 3:9) Babu shakka, ƙoƙarce-ƙoƙarcensu yana faranta wa Jehobah rai sosai! A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ra’ayin Jehobah kuma mu saka hannu wajen sa majagabanmu su yi farin ciki kuma su jimre a hidimarsu?

Babu shakka, kalamanmu masu daɗi za su iya ƙarfafa su su ci gaba da yin hidimar majagaba. (Mis. 25:11) Shin za mu iya yin gyara a tsarin ayyukanmu na duk mako don mu fita hidimar fage tare da su? Idan zai yiwu, za mu iya ɗaukansu da motarmu ko kuma mu biya musu kuɗin motar da suka shiga? (1 Kor. 13:5; Filib. 2:4) Za mu kuma nuna tallafawarmu ta samun halin karɓin baƙi da kuma gayyatar majagaba zuwa gidanmu don su ci abinci.—1 Bit. 4:8, 9.

Nassosi sun tabbatar cewa Jehobah zai yi tanadin bukatun duk waɗanda suke biɗan Mulkinsa farko a rayuwarsu. (Zab. 37:25; Mat. 6:33) Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta ƙaunataccen ’yan’uwancinmu na Kirista. (1 Yoh. 3:16-18) Hakika, majagaba ba sa sa rai cewa mutane za su ɗauki nauyin bukatunsu na kuɗi. Kuma wataƙila ba za su faɗa wa mutane cewa suna bukatan wani abu ba. Amma dai, za mu iya taimaka wa amintattun majagaba kuma mu biya ‘bukatansu’ a hanyoyi masu kyau ta kasancewa a faɗake da kuma yin lura.—2 Kor. 8:14, 15.

Sa’ad da Fibi, wata mai wa’azin bishara mai ƙwazo a ƙarni na farko a ikilisiyar Kankriya, ta yi tafiya zuwa ƙasar Roma, sai Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwa a ƙasar Roma: “Ku karɓe ta cikin Ubangiji yadda ya cancanta a wajen tsarkaka, ku taimake ta a cikin iyakar matsala inda za ta bukace ku.” (Rom. 16:1, 2) Muna da zarafin yin irin wannan tallafawa na ƙauna ga waɗanda suke shelarta bishara ba fasawa a matsayin majagaba na kullum da na musamman a cikin ikilisiyarmu.—A. M. 5:42.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba