Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/10 p. 4
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Abin da Za a Ce Game da Mujallun
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 10/10 p. 4

Abin da Za a Ce Game da Mujallun

Oktoba-Disamba

Ka faɗa wani labari da ya faru a yankin. Sai ka ce: “Ka taɓa tunanin dalilin da ya sa mutane suke yin irin wannan mugunta kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya ba mu dalilin yin bege. [Karanta 2 Bitrus 3:13.] Wannan mujallar ta nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da sanadin mugunta da kuma yadda Allah zai kawo ƙarshen mugunta ba da daɗewa ba.”

Oktoba

“Wasu suna ɗaukan Allah kamar marar ƙauna. Wasu kuma suna ɗaukansa kamar mai ƙauna sosai. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da wannan kalami mai daɗaɗawa. [Karanta 1 Bitrus 5:6, 7.] Talifin da ya soma daga shafi na 29 ya ba da amsa da ke bisa Littafi Mai Tsarki, ga tambayar nan, Shin Allah yana wanzuwa da gaske?”

Oktoba-Disamba

“Mutane da yawa suna da nasu Littafi Mai Tsarki domin sun amince cewa Kalmar Allah ce. Amma dai, yana wa wasu wuya su karanta Littafi Mai Tsarki. Kai kuma fa? [Ka bari ya ba da amsa.] Don Allah ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a wannan ayar. [Karanta Joshua 1:8.] Wannan talifin da ya soma daga shafi na 29 ya tattauna matakai bakwai da za ka iya ɗauka don ka amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki.”

Nuwamba

“Wasu da ba su amince da wanzuwar Allah ba suna nuni ga miyagun abubuwan da ake yi da sunan Allah kuma suna jin cewa duniya za ta kasance wuri mai kyau idan babu addini. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga dalili ɗaya da ya sa addinin ƙarya ya jawo wahala. [Karanta 2 Timotawus 4:3, 4.] Wannan mujallar ta yi magana a kan wasu kurakure a tunanin waɗanda ba su amince da wanzuwar Allah ba.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba