Tsarin Ayyuka na Makon 18 ga Oktoba
MAKON 18 GA OKTOBA
Waƙa ta 45
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 9 sakin layi na 10-18 da akwati
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Labarbaru 8-11
Na 1: 1 Labarbaru 11:1-14
Na 2: A Waɗanne Hanyoyi Ne Ruhu da Amarya Suke Cewa, “Zo”? (R. Yoh. 22:17)
Na 3: Ya Kamata Kiristoci Su Yi Amfani da Sunan Allah (td 23A)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 65
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Muhimmancin Kallon Fuskar Mutane a Hidima. Tattaunawa da masu sauraro da aka ɗauko daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 124, sakin layi na 1, zuwa shafi na 125, sakin layi na 4.
Minti 20: “Sabuwar Mujalla da Za a Ba Da!” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Sa’ad da kake tattauna sakin layi na ɗaya, ka ɗan taƙaita abubuwa da ke cikin mujallar. Bayan ka tattauna sakin layi na 2 da 3, ka sa a yi amfani da gabatarwa da ke cikin talifin don a gwada yadda za a ba da mujallar. Bayan ka tattauna sakin layi na 4, ka sa a gwada yadda za a soma nazarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da aka koma ziyara.
Waƙa ta 114