Umurni ga Waɗanda Suke Yin Aiki a Taron Hidima
Somawa da fitowar Hidimarmu Ta Mulkin nan, an sauƙaƙa kalmomin da ake amfani da su a tsarin ayyuka na Taron Hidima. Waɗannan umurni da tunasarwa za su daɗa bayyana abin da aka rubuta a talifin nan “Yadda Za Ka Yi Shiri Don Taron Hidima,” wanda ya fito a Hidimarmu Ta Mulki ta Mayu 2009.
◼ Jawabi: Wannan yana nufin tattauna littafin bincike da aka ba da ba tare da yi wa masu sauraro tambayoyi ba. Mai ba da jawabin ya mai da hankali ga abin da zai taimaki ikilisiyar sosai.
◼ Tambayoyi Ana Ba da Amsoshi: Za a gabatar da wannan sashin kamar yadda ake yi da nazarin Hasumiyar Tsaro, za a ba da gajeriyar gabatarwa da kalaman rufewa, kuma za a yi tambayoyi a dukan sakin layin. Mai gudanar da taron ya guji ba da kalamai da yawa. Za a iya karanta fitattun nassosi idan da lokaci. Kada a karanta sakin layin sai dai in an ce a yi hakan.
◼ Tattaunawa: Wannan jawabi ne da ya haɗa da yi wa masu sauraro tambayoyi. Ba jawabi kaɗai ba ne, kuma ba tambayoyi ana ba da amsoshi kaɗai ba ne.
◼ Gwaji da Ganawa: Umurnin nan gwada yana nufin cewa ɗan’uwan da yake da wannan aikin yana da hakkin shirya don a yi gwaji, ba ya bukatan ya yi gwajin da kansa. Waɗanda ya zaɓa su yi gwajin su kasance waɗanda suka ƙware da kuma masu misali mai kyau, kuma ya sa su yi shiri tun da wuri idan zai yiwu. Ba zai dace ba a sa sababbin masu shela da kuma waɗanda ba su ƙware ba sosai su yi gwajin don dai a ba su zarafin hawan dakalin yin magana, ko da yake za a iya yin amfani da su a matsayin masu gida. Masu shela da suke yin gwaji su zauna inda masu sauraro za su riƙa ganin fuskarsu. Waɗanda ake ganawa da su su yi hakan a kan dakalin yin magana ba daga wurin zamansu ba. A maimaita gwajin da ganawan sosai tun da wuri. Idan lokaci ya kusan ƙurewa kuma ya zama wajibi cewa ɗan’uwan da ke gabatar da sashen zai gajertar da sashensa, kada ya soke ganawa da gwaji. Bayi masu hidima su tambayi mai tsara ayyukan rukunin dattawa ko kuma wani dattijo kafin su zaɓi waɗanda za su ba gwaji ko ganawa.
Idan wani fitaccen sashe yana da umurni na musamman, a bi hakan sosai. Ta wurin yin aiki na Taron Hidima kamar yadda aka ambata a sama, ’yan’uwa za su sa Taron Hidima ya kasance da “hankali bisa ga ƙa’ida kuma.”—1 Kor. 14:40.