Ayyuka na Makon 2 ga Agusta
MAKON 2 GA AGUSTA
Waƙa ta 97
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh babi na 6 sakin layi na 9-20 da akwati
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sarakuna 18-20
Na 1: 1 Sarakuna 18:21-29
Na 2: A Wane Azanci Ne Sama da Duniya Za Su Shuɗe? (R. Yoh 21:1)
Na 3: Su Waye Za Su Je Sama (td 38A)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 110
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Hanyoyin da Za Ka Iya Faɗaɗa Hidimarka—Sashe na 4. Jawabin da aka ɗauko daga littafin nan Organized To Do Jehovah’s Will, shafi na 116, sakin layi na 1, zuwa shafi na 117, sakin layi na 1. Ka gana da mai shela ɗaya ko biyu da yake taimakawa wajen gina Majami’ar Mulki ko Majami’ar Babban Taro game da yadda yake more wannan gatar hidima.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Labarai Game da Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki. Tattaunawa da masu sauraro. Ka faɗi abin da aka cim ma a yankin a rana ta musamman na gabatar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Ka gayyaci masu sauraro su faɗi labaran da suka shaida. Za a iya gwada fitaccen labari guda ɗaya ko biyu. Ka kammala ta wajen gwada yadda za a soma nazarin Littafi Mai Tsarki a ziyara na farko.
Waƙa ta 24