Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Yuni: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Idan masu gida suna da littafin, masu shela suna iya ba da tsofaffin littafin da ikilisiyar take da su a ajiye. Yuli da Agusta: Masu shela za su iya yin amfani da kowanne cikin waɗannan mujallu masu shafuffuka 32 da ke a ajiye: Allah Yana Kula Da Mu Kuwa da Gaske?, Ka More Rayuwa a Duniya Har Abada!, Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?, The Divine Name That Will Endure Forever, Hanyar Rai Madawwami—Ka Same ta Kuwa? Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu?, Minene Ma’anar Rai? Ina Yadda Zaka Same Shi?, Yayinda Wani Wanda Ka ke Ƙauna ya Mutu da kuma Za Ka Iya Zama Abokin Allah! Kuna iya ba da duk wata tsohuwar mujallar da ke ajiye a ikilisiya. Satumba: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a haɗuwa na farko.
◼ Za a tattauna bidiyon nan The Bible—Its Power in Your life da The Bible—Accurate History, Reliable Prophecy a Taron Hidima farawa daga watan Satumba. Idan da bukata, kuna iya yin odar ɗin FAIFAN DVD nan The Bible—A Book of Fact and Prophecy—On DVD, wanda ke ɗauke da waɗannan tsarin, ta hanyar ikilisiya ban da ɓata lokaci.