Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/10 p. 3
  • Akwatin Tambaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwatin Tambaya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ku Yi Amfani da Sauti
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 4/10 p. 3

Akwatin Tambaya

◼ Shin ya dace Shaidun Jehobah su rarraba jawabi da aka ɗauka a faifai ko kuma a rubuce?

Muna samun ƙarfafawa sa’ad da muka saurari jawaban Littafi Mai Tsarki. (A. M. 15:32) Saboda haka, daidai ne mu so gaya wa waɗanda ba su halarci wannan taron ba waɗannan bayanan masu ƙarfafawa. Tun da akwai na’urori iri-iri na ɗaukan muryoyi a yau, ɗaukan jawabi da kuma rarraba su ga mutane bai da wuya. Wasu suna da tarin jawabai da yawa da aka ɗauka, har da jawaban da aka ba da shekaru da yawa da suka shige, kuma da manufa mai kyau suna ba da aron waɗannan jawaban ko kuma su sake ɗaukansu su ba abokansu. Wasu sun buɗe Duniyar gizo kuma sun saka waɗannan jawaban don wasu su kofa.

Babu shakka, ba laifi ba ne idan muka ɗauki jawabi domin amfanin kanmu ko kuma don waɗanda suke cikin iyalinmu. Ƙari ga hakan, dattawa za su iya sa a ɗauki jawabai domin ’yan’uwa marar lafiya da ke ikilisiyar da ba su samu halartar taron ba. Amma dai, akwai dalilai masu kyau da ya sa bai kamata mu rarraba jawabai da aka ɗauka a faifai ko a rubuce ba.

Domin akan ba da jawabai ne bisa ga bukatun yanki, za mu iya samun mummunar fahimta daga jawaban da aka rarraba, tun da ba za mu fahimci dalilin da ya sa aka ba da jawabin ba. Ƙari ga hakan, sanin wanda ya ba da jawabin da kuma lokacin da aka ba da jawabin zai yi wuya, don mu samu tabbaci cewa abin da aka faɗa daidai ne da kuma gaskiya. (Luk. 1:1-4) Bayan hakan, rarraba jawabai da aka ɗauka a faifai ko a rubuce zai iya sa wasu su ba da ko kuma su karɓi yabon da bai dace ba.—1 Kor. 3:5-7.

Bawan nan mai aminci, mai hikima sun yi aiki tuƙuru don yin tanadin abinci na ruhaniya a “lotonsa.” (Luk. 12:42) Wannan ya haɗa da shirin ba da jawabi a ikilisiyoyin Shaidun Jehobah da kuma sautin da aka ɗauka da za a iya kofa daga Duniyar gizo na jw.org. Muna da tabbaci cewa bawa mai-aminci, mai-hikima da Hukumar Mulkinsa za su ba mu abin da muke bukata don mu ƙarfafa bangaskiyarmu.—A. M. 16:4, 5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba