Tsarin Ayyuka na Makon 8 ga Fabrairu
MAKON 8 GA FABRAIRU
Waƙa ta 47
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
lv babi na 16 sakin layi na 15 zuwa 22, da akwatin da ke shafi na 194
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Alƙalawa 11 zuwa 14
Na 1: Alƙalawa 13:1-14
Na 2: Menene Za Mu Iya Koya Daga Kalaman Yesu da ke Rubuce a Luka 16:9-13?
Na 3: Ƙarin Jini Yana Ɓata Tsarkin Jini (td 24A)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 67
Minti 5: Sanarwa.
Minti 10: Amsa Tambayoyi Game da Ranakun Hutu. Tattaunawa da masu sauraro daga littafin nan Reasoning from the Scriptures, ƙarƙashin kan magana biyu da ke shafi na 178 da 179. Waɗanne bukukuwa ne wataƙila mutanen da ke yankinku za su yi? A wane yanayi ne wataƙila za ka iya ba da shaida game da ɗaya daga cikin ranakun hutun? Ka haɗa da gwaji da ya nuna yadda uba yake shirya ɗansa ko ’yarsa ta mai da martani ga wannan tambayar, Me ya sa ba ka yin bikin Easter?
Minti 20: “Takardun Gayyata na Tuna Mutuwar Yesu Wanda Za a Rarraba a Dukan Duniya!” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Kafin ka tattauna sakin layi na 2, ka ba kowa kofi ɗaya na takardar gayyatar, idan akwai, kuma ka jawo hankalinsu ga fasaloli dabam-dabam na takardar. Bayan ka tattauna sakin layi na 2, ka sa mai shela ya gwada yadda za a yi amfani da takardar gayyatar. Ta gana da mai kula da hidima ko kuma wani dattijo don ya bayyana ƙarin shirye-shiryen fita hidimar fage da aka yi don kamfen ɗin da ke tafe na Tuna Mutuwar Yesu da za a yi.
Waƙa ta 114