Kana Shirye Ka Yi Waƙa Ga Jehobah a Taronmu?
1 Shirya yin rabo a taronmu ya haɗa da shirya rera waƙar yabo. Ka yi la’akari da waɗannan shawarwari.
2 Ku Fahimci Kalmomin: Jigon nassi da ƙarin nassosi da aka lissafa a ƙarshen kowacce waƙar ta taimaka wajen nanata inda aka ɗauko waƙar a cikin nassi.
3 Koyo: Za ku iya yin amfani da ɗan lokaci na Bautar Iyali da Yamma a kowanne mako don koyon sababbin waƙoƙin sosai. Ku rera ta tare da wanda aka buga da garaya da za a yi amfani da ita a taronmu. Za ku iya koyan rera waƙar da wasu kalmomi na sababbin waƙoƙi ta wajen saurarar Sing to Jehovah—Vocal Renditions, Faifai na 1.
4 Za ku kasance a shirye sa’ad da muka soma yin amfani da Sing to Jehovah a taronmu a farkon makon 5 ga Afrilu, 2010? Za ku yi hakan idan kun ɗauki lokaci don ku fahimci ma’anar waƙoƙin kuma ku koya rera su.