Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w19 Disamba p. 15
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Tawaye a Cikin Lardi na Ruhu
    Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?
  • Ƙage Na 1: Kurwa Ba Ta Mutuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
w19 Disamba p. 15

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Sa’ad da Shaiɗan ya gaya wa Hauwa’u cewa idan ta ci ’ya’yan itacen sanin nagarta da mugunta ba za ta mutu ba, shin yana so ya koya mata cewa kurwa ba ta mutuwa ne?

Shaidan ya yi amfani da maciji wajen jarabtar Hauwa’u

A’a. Shaiɗan bai gaya wa Hauwa’u cewa idan ta ci ’ya’yan itacen da Allah ya haramta, za ta zama kamar mutum da ya mutu amma kurwarta za ta ci gaba da rayuwa a wani wuri ba. Sa’ad da Shaiɗan ya yi amfani da maciji ya yi magana da Hauwa’u, ya yi da’awa cewa idan ta ci ’ya’yan itacen, ‘ko kaɗan, ba za ta mutu ba.’ Shaiɗan yana nufin cewa Hauwa’u za ta ci gaba da more rayuwa a duniya kuma za ta sami ’yanci daga wurin Allah.​—Far. 2:17; 3:​3-5.

Idan koyarwar kurwa marar mutuwa ba ta samo asali a lambun Adnin ba, yaushe ne aka soma wannan koyarwar? Ba mu sani ba. Mun san cewa an hallaka dukan addinan ƙarya sa’ad da aka yi Ambaliya a zamanin Nuhu. Allah ya yi amfani da ambaliyar wajen hallaka dukan mabiyan addinan ƙarya, Nuhu da iyalinsa ne kaɗai suka tsira kuma suna bauta wa Jehobah.

Koyarwar kurwa marar mutuwa ta samo asali ne bayan Ambaliya a zamanin Nuhu. A lokacin da Allah ya dagula yaren da ake yi a Babel kuma mutanen suka ‘warwatsa ko’ina a fuskar duniya,’ babu shakka, sun kai koyarwar nan cewa kurwa ba ta mutuwa zuwa wuraren. (Far. 11:​8, 9) Ko da daga ina ne wannan koyarwar ta samo asali, muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Shaiɗan, wanda shi “uban ƙarya” ne ya yaɗa wannan koyarwa.​—Yoh. 8:44.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba