Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 p. 10
  • Ƙage Na 1: Kurwa Ba Ta Mutuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙage Na 1: Kurwa Ba Ta Mutuwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 p. 10

Ƙage Na 1: Kurwa Ba Ta Mutuwa

Menene tushen wannan ƙagen? “Kiristocin ƙarni na farko masu ussan ilimi sun samo koyarwar Hellenanci na kurwa marar mutuwa kuma sun yarda cewa Allah ne yake halittan kurwa kuma ya saka ta cikin jikin mutum sa’ad da yake cikin mahaifiyarsa.”—The New Encyclopædia Britannica (1988), Volume 11, shafi na 25.

Menene Littafi Mai Tsarki ya ce? “Mai-rai [kurwa] da ya yi zunubi, shi za ya mutu.”—Ezekiel 18:4.

Game da mutum ko kurwa na farko da aka halitta, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji Allah kuwa ya sifanta mutum daga turɓayar ƙasa, ya hura masa lumfashin rai cikin hancinsa; mutum kuma ya zama rayayyen mai-rai [Ibraniyanci, ne’phesh].”—Farawa 2:7.

Kalmar nan na Ibrananci ne’phesh, wanda aka fassara shi “kurwa,” tana nufin ‘halitta mai numfashi.’ Sa’ad da Allah ya halicci mutum na farko, Adamu, bai hura masa rai marar mutuwa ba amma ya ba shi rai da zai ci gaba da rayuwa ta yin numfashi. Saboda haka, “kurwa” a cikin Littafi Mai Tsarki tana nufin gabaki ɗayan abu mai rai. Idan an raba shi daga ainihin rai da Allah ya ba shi, kurwar zai mutu.—Farawa 3:19; Ezekiel 18:20.

Koyarwar kurwa marar mutuwa ta tayar da tambayoyi: Ina kurwa suke zuwa bayan mutuwa? Menene ke faru wa kurwar miyagun mutane? Sa’ad da waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne suka amince da ƙagen kurwa marar mutuwa, hakan ya sa su amince da wata ƙage, wato, koyarwar wutar jahannama.

Ka gwada waɗannan ayoyi na Littafi Mai Tsarki: Mai-Wa’azi 3:19; Matta 10:28; Ayyukan Manzanni 3:23

GASKIYA:

Sa’ad da mutum ya mutu ba ya ci gaba da rayuwa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba