Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp19 Na 1 pp. 4-5
  • Mene ne Sunan Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Sunan Allah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA YA SA SUNAN ALLAH YAKE DA MUHIMMANCI
  • ME SUNAN YAKE NUFI?
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Amfani da Sunan Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Daraja Suna Mai Girma Na Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ma’anar Sunan Allah da Yadda Ake Amfani da Shi
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ka San Sunan Allah Kuma Kana Amfani da Shi Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
wp19 Na 1 pp. 4-5

Mene Ne Sunan Allah?

Idan kana son ka san game da wani, ba mamaki za ka soma da yi masa wannan tambayar, “Mene ne sunanka?” Idan ka yi wa Allah wannan tambayar, me kake ganin zai ce?

“Ni ne Yahweh [Jehobah], sunana ke nan.”​—Ishaya 42:8.

Mai yiwuwa wannan ne ƙaro na farko da ka soma jin sunan nan domin yawancin mafassaran Littafi Mai Tsarki ba sa cika amfani da ainihin sunan Allah. Wasu ma sun cire sunan gaba ɗaya daga nasu juyin. Sukan maye gurbinsa da laƙabin nan “UBANGIJI.” Amma sunan Allah ya bayyana aƙalla sau 7,000 a cikin ainihin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da shi. An rubuta sunan da baƙaƙen harufa guda huɗu, wato YHWH ko kuma JHVH, kuma an daɗe ana fassara shi zuwa “Jehovah” ko Jehobah a Hausa.

Sunan Allah na Ibrananci a Littattafan da Aka Samu a Tekun Gishiri

Ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu, IBRANANCI

Sunan Allah a Turanci a fassarar Tyndale

Fassarar Tyndale 1530, TURANCI

Sunan Allah a Sifanisanci a juyin Littafi Mai Tsarki na Reina-Valera

Juyin Reina-Valera 1602, Sifanisanci

Sunan Allah a Cinanci a juyin Littafi Mai Tsarki na Union Version

Juyin Union 1919, Cinanci

Sunan Allah ya bayyana sau da yawa a cikin littattafan Ibrananci da kuma wasu juyin Littafi Mai Tsarki da yawa

ABIN DA YA SA SUNAN ALLAH YAKE DA MUHIMMANCI

Sunan yana da muhimmanci ga Allah. Allah ne ya saka wa kansa sunan, ba wani ba. Jehobah ya ce: “Wannan shi ne sunana har abada, da wannan suna za a dinga kirana har dukan tsara masu zuwa.” (Fitowa 3:15) Sunan Allah ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki fiye da laƙabin nan da ake kiransa da shi, wato Maɗaukaki da Ubangiji, ko kuma Allah. Ya kuma bayyana fiye da sunayen bayinsa, kamar su Ibrahim da Musa da Dauda da kuma Yesu. Ƙari ga haka, Jehobah yana son kowa da kowa ya san sunansa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari su san cewa kai kaɗai ne Mai suna Yahweh, Mafi Ɗaukaka a dukan duniya.”​—Zabura 83:18.

Sunan yana da muhimmanci ga Yesu. A cikin addu’ar da Yesu ya koyar da aka fi sani da Addu’ar Ubangiji, ya gaya wa almajiransa su yi addu’a ga Allah cewa: ‘A kiyaye sunanka da tsarki.’ (Matiyu 6:9) Yesu ma da kansa ya yi addu’a ga Allah ya ce: ‘Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.’ (Yohanna 12:28) Ɗaukaka ko kuma tsarkake sunan Allah yana da muhimmanci ga Yesu, shi ya sa ya ce: “Na kuma sanar musu da sunanka, zan kuma sanar da shi.”​—Yohanna 17:​26, Littafi Mai Tsarki.

Sunan yana da muhimmanci ga waɗanda suka san Allah. Bayin Allah a zamanin dā sun gaskata cewa sunan Allah yana kāre su da kuma sa su sami ceto. “Sunan Yahweh katanga mai ƙarfi ne, mai adalci yakan gudu ya shiga ya zauna lafiya.” (Karin Magana 18:10) “Duk wanda ya kira ga Sunan Yahweh domin neman taimako za a cece shi.” (Yowel 2:32) Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa sunan Allah ne zai sa a san waɗanda suke bauta masa. Ya ce: “Gama dukan ƙabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”​—Mika 4:​5, LMT; Ayyukan Manzanni 15:14.

ME SUNAN YAKE NUFI?

Sunan yana wakiltar Allah shi kaɗai. Masanan Littafi Mai Tsarki da yawa sun ce sunan yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Jehobah ya sa mun fahimci ma’anar sunansa ta abin da ya gaya wa Musa: “Zan Zama Abin da Nake So In Zama.” (Fitowa 3:​14, New World Translation) Saboda haka, sunan bai nuna mana cewa shi ne mahaliccin kome da kome kawai ba. Amma ya nuna cewa yana da ikon sa kansa ko kuma halittunsa su yi duk wani abin da yake so. Laƙabi da ake kiran Allah da shi yana nuna matsayinsa ko ikonsa ko kuma ƙarfinsa, amma sunansa ne kaɗai yake wakiltar kome game da shi da kuma abubuwan da zai iya yi.

Sunan ya nuna cewa Allah yana ƙaunar mu. Ma’anar sunan Allah ta nuna cewa yana ƙaunar halittunsa har da mu ’yan Adam. Ƙari ga haka, tun da Allah ya sanar da sunansa, hakan yana nufin cewa yana son mu san shi. Domin shi ya gaya mana sunansa tun kafin mu tambaye shi. Hakika, Allah yana so mu san cewa za mu iya kusantar sa kuma mu zama aminansa.​—Zabura 73:28.

Idan muna amfani da sunan Allah, hakan zai nuna cewa muna ƙaunarsa. Alal misali, a ce ka gaya ma wani ainihin sunanka don kana so ya zama abokinka. Yaya za ka ji idan mutumin ya ƙi ya kira ka da ainihin sunanka? Da shigewar lokaci, za ka ji cewa mutumin ba ya son ya zama abokinka. Haka yake da Allah. Jehobah ya gaya ma ’yan Adam sunansa kuma ya ce mu riƙa kiransa da shi. Idan mun yi amfani da sunan, muna nuna ma Jehobah cewa muna so mu zama aminansa. Domin yana sane da waɗanda suke “yin tunanin sunansa.”​—Malakai 3:16.

Abu na farko da ya kamata mu yi idan muna son mu san Allah shi ne mu san sunansa. Amma bai ƙare a nan ba. Muna bukatar mu san halayensa.

MENE NE SUNAN ALLAH? Sunan Allah shi ne Jehobah ko kuma Yahweh. Sunan yana wakiltar Allah shi kaɗai kuma ya nuna cewa Allah zai iya yin duk wani abin da yake so

WA YA HALICCI ALLAH?

Mutane da yawa suna marmarin sanin amsar wannan tambayar. Ba mamaki kai ma kana marmarin sanin amsar wannan tambayar. Ko kuma mu yi tambayar kamar haka: Tun da yake Allah ne ya halicci sama da ƙasa, to shi da kansa wa ya halicce shi?

’Yan kimiyya sun gaskata cewa akwai wanda ya yi sama da ƙasa. Hakan ya yi daidai da abin da aya ta farko ta Littafi Mai Tsarki ta faɗa cewa: “Da farko Allah ya halicci sammai da kuma duniya.”​—Farawa 1:​1, NW.

Ba za mu ce taurari da kuma duniyoyi su suka halicci kansu ba. Idan har wani abu ya soma wanzuwa, akwai wanda ya halicci abin. In har babu mahalicci, mu kanmu da dukan abubuwan da muke gani kewaye da mu ba za su wanzu ba. Saboda haka, akwai mahalicci mai iko sosai kuma sunansa shi ne Jehobah.​—Yohanna 4:24.

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da Allah cewa: ‘Kafin haihuwar manyan tuddai, tun kafin fitowar ƙasa da duniya, kai Allah ne har abada, marar farko marar ƙarshe.’ (Zabura 90:2) Allah ba shi da farko balle ƙarshe. Saboda haka, “da farko” Allah ne ya halicci sama da ƙasa.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba