Abin da Ke Ciki
MAKON 29 GA OKTOBA, 2018–4 GA NUWAMBA, 2018
3 In “Kun San Waɗannan Abubuwa, Za Ku Zama Masu Albarka Idan Kun Yi Su”
Ilimi zai kasance da amfani a gare mu idan muna yin amfani da shi. Amma za mu yi abin da muka koya idan mu masu tawali’u ne. A wannan talifin, za a koya mana yadda za mu yi koyi da waɗanda aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki da suka yi wa mutane dabam-dabam wa’azi kuma sun yi addu’a a madadin wasu. Ƙari ga haka, sun jira Jehobah ya ɗau mataki.
8 Tsofaffi—Jehobah Yana Daraja Ku Don Amincinku
MAKON 5-11 GA NUWAMBA, 2018
12 Ku Riƙa Nuna Ƙauna Domin Tana Ƙarfafa Mutane
A wannan mawuyacin zamani, mukan yi sanyin gwiwa don matsalolin rayuwa. Amma Jehobah da Yesu za su taimaka mana mu jimre. Duk da haka, dukanmu za mu iya ƙarfafa da kuma yi wa juna ta’aziyya. A wannan talifin, za mu koyi yadda za mu riƙa ƙarfafa juna.
MAKON 12-18 GA NUWAMBA, 2018
17 Waɗanda Ke Bauta wa Allah Suna Farin Ciki
Jehobah Allah ne mai farin ciki kuma yana son bayinsa su riƙa farin ciki. Amma ta yaya za mu riƙa farin ciki duk da cewa muna fuskantar matsaloli a wannan duniyar? A Huɗubar da Yesu ya yi a kan Dutse ya ba da shawara mai kyau da za ta taimaka mana mu riƙa farin ciki.
22 Ta Yaya Ake Sanin Lokaci a Zamanin Dā?
MAKON 19-25 GA NUWAMBA, 2018
23 Shi Maɗaukaki Ne Amma Yana Yin La’akari da Mu
MAKON 26 GA NUWAMBA, 2018–2 GA DISAMBA, 2018
28 Ka Riƙa Yin La’akari da Mutane Kamar Jehobah
A yau, mutane suna daɗa zama masu son kai. Amma, bayin Jehobah ba sa hakan domin suna ƙaunar mutane sosai. Hanyar da suke yin hakan ita ce ta wajen yin la’akari da mutane. A waɗannan talifofi biyu za mu tattauna yadda Jehobah yake yin la’akari da dukanmu. Ƙari ga haka, za mu yi bitar yadda za mu iya yin koyi da shi.