Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w18 Agusta pp. 31-32
  • Yadda Aka Soma Wa’azi a Kasar Portugal

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Aka Soma Wa’azi a Kasar Portugal
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
w18 Agusta pp. 31-32

DAGA TARIHINMU

Yadda Aka Soma Wa’azi a Ƙasar Portugal

YAYIN DA raƙuman ruwan tekun Atilantika ke bugun jirgin ruwa da ke zuwa Turai, ɗaya cikin fasinjojin mai suna George Young yana farin ciki sa’ad da ya tuna yadda ya yi wa’azi da ƙwazo a Brazil.a Amma sa’ad da yake cikin tafiya, sai ya soma tunanin Sifen da Portugal sababbin ƙasashen da zai je. Kuma waɗannan ƙasashen suna da babban yankunan da ba a taɓa yin wa’azi a ciki ba. Muddin ya isa wurin, maƙasudinsa shi ne ya yi shiri don Ɗan’uwa J. F. Rutherford ya zo ya yi jawabi kuma zai rarraba warƙoƙi 300,000.

George Young yana tafiya ta jirgin ruwa

George Young ya yi tafiye-tafiye da jirgin ruwa sosai zuwa ƙasashe da yawa yana wa’azi

Da ya isa birnin Lisbon a shekara ta 1925, Ɗan’uwa Young ya ga cewa ana tashin hankali. Juyin mulki da aka yi a shekara ta 1910 ya rage ikon da Limaman Cocin Katolika suke da shi. Amma an ci gaba da tashin hankali a ƙasar duk da cewa mutanen sun sami ’yanci.

Sa’ad da Ɗan’uwa Young yake yin shirye-shirye don Ɗan’uwa Rutherford ya zo ya yi jawabi, sai gwamnati ta kafa wata doka da ta hana mutane yin wasu ayyuka domin an so a yi juyin mulki. Sakataren ƙungiyar Bible Society na Britaniya ya gaya wa Ɗan’uwa Young cewa ’yan adawa za su tsananta masa sosai. Duk da haka, ɗan’uwan ya nemi izinin yin amfani da ɗakin motsa jiki da ke makarantar sakandare na Camões, kuma aka ba shi izinin yin amfani da wurin!

Ɗan’uwa Rutherford zai yi jawabin a ranar 13 ga Mayu, kuma mutane suna ɗokin jin jawabin. Ƙari ga haka, an manna katuna a gine-gine kuma jaridu sun sanar da jawabi mai jigo, “How to Live on the Earth Forever,” (“Yadda Za a Yi Rayuwa Har Abada a Duniya.”) Sai masu hamayya suka yi hanzari suka wallafa wani talifi a nasu jaridu domin su gaya wa mutane cewa sabon addinin da ya shigo gari na “annabawan ƙarya ne.” A ƙofar majami’ar da za a yi jawabin, ’yan adawa sun rarraba dubban ƙasidu don su ƙaryata koyarwar Ɗan’uwa Rutherford.

Duk da haka, mutane 2,000 sun cika ɗakin maƙil kuma aka hana mutane da dama shiga don babu wurin zama. Wasu da suke son su ji jawabin sun hau tsāni na igiya a gefen ɗakin. Wasu kuma suka hau kan kayan motsa jiki.

Duk da haka an sami wasu matsaloli. ’Yan hamayya suna ta ihu da kuma kakkarye kujeru. Amma Ɗan’uwa Rutherford ya natsu kuma ya hau kan teburi don mutane su ji muryarsa sosai. Bayan ya gama jawabin a tsakar dare, mutane fiye da 1,200 sun ba da sunayensu da adireshi don a aika musu littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Washegari, aka wallafa wani talifi game da jawabin da Ɗan’uwa Rutherford ya yi a jaridar O Século.

An soma wallafa Hasumiyar Tsaro ta yaren Portuguese a watan Satumba 1925 a ƙasar Portugal. (Kafin wannan lokacin an riga an wallafa ta a Brazil.) A wannan lokacin, wani mai suna Virgílio Ferguson ya soma shirin ƙaura zuwa Portugal don ya yi wa’azi. Ya yi aiki tare da Ɗan’uwa Young a ƙaramin ofishin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da ke Brazil. Virgílio da matarsa Lizzie sun shiga jirgin ruwa don su je su sami Ɗan’uwa Young. Zuwansu ya dace don ba da daɗewa ba, Ɗan’uwa Young zai je yin wa’azi a Ƙasar Rasha ta Dā.

Takardan yarda a zauna a kasa na Lizzie da Virgílio Ferguson, a shekara ta 1928

Takardar izini na ’Yar’uwa Lizzie Ferguson da maigidanta Virgílio, a 1928

Mutanen sun sha wahala sosai kuma an ƙara tsananta wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sa’ad da gwamnati ta kafa mulkin kama karya a Portugal. Ɗan’uwa Ferguson ya kasance da gaba gaɗi kuma ya ɗauki mataki don ya kāre ƙaramin rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke ƙasar kuma ya ƙarfafa su. Ƙari ga haka, ya nemi izinin yin amfani da gidansa don yin taro kuma aka ba shi izinin yin hakan a watan Oktoba 1927.

A shekara ta farko ta mulkin kama karya, wajen mutane 450 ne a Portugal suka ce a riƙa tura musu Hasumiyar Tsaro. Ƙari ga haka, mutanen da suke ƙasashen da ake yaren Portuguese sun koyi gaskiya ta wurin karanta warƙoƙi da ƙasidu. Wuraren da ake yaren Portuguese su ne Angola da Azores da Cape Verde da East Timor da Goa da Madeira da kuma Mozambique.

Wani ɗan Portugal da ke aikin lambu mai suna Manuel da Silva Jordão ya zo Lisbon a shekara ta 1929. Sa’ad da yake zama a Brazil ya ji jawabin Ɗan’uwa Young. Ya fahimci cewa abin da ya ji gaskiya ne kuma ya yi ɗokin ya je ya yi wa’azi tare da Ɗan’uwa Ferguson. Sai Manuel ya soma hidimar majagaba. ’Yan’uwa da ke sabuwar ikilisiyar da ke Lisbon sun sami ci gaba sosai da yake an tsara yadda ake wallafa da kuma rarraba littattafanmu.

Ɗan’uwa da ’yar’uwa Ferguson sun koma Brazil a shekara ta 1934, amma sun riga sun yi wa’azi sosai. Kuma ƙaramin rukunin da ke Portugal sun kasance da aminci ga Jehobah sa’ad da ake yaƙin basasa a ƙasar Sifen da kuma Yaƙin Duniya na Biyu. Sun ɗan yi sanyi a ibadarsu, amma sun sake kasancewa da ƙwazo a 1947 sa’ad da Ɗan’uwa John Cooke wanda shi ne mai wa’azi a ƙasar waje na farko da ya je ƙasar ya ƙaura zuwa wurin. Tun daga lokacin, masu shelar Mulki suna ƙaruwa sosai. Kuma sun ci gaba da ƙaruwa a lokacin da gwamnati ta saka wa aikin Shaidun Jehobah takunkumi a shekara ta 1962. Ban da haka, da akwai masu shela 13,000 a ƙasar sa’ad da aka ɗage takunkumin da aka saka wa aikin Shaidun Jehobah a watan Disamba 1974.

A yau da akwai masu shela fiye da 50,000 da suke wa’azin Mulkin Allah a Portugal da kuma tsibirai da yawa da ake yaren Portuguese, har da yankunan Azores da Madeira. Zuriyar wasu da suka saurari jawabin Ɗan’uwa Rutherford a 1925 suna cikin waɗannan masu shela.

Muna godiya ga Jehobah da kuma waɗannan ’yan’uwa masu gaba gaɗi da suka yi ja-goranci wajen yin wa’azi game da ‘almasihu Yesu ga’ mutanen al’ummai.​—Rom. 15:​15, 16.​—Daga tarihinmu a Portugal.

a Ka duba talifin nan “Tsugune Ba ta Ƙare Ba” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 2014, shafuffuka na 31-32.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba