Abin da Ke Ciki
MAKON 30 GA AFRILU, 2018–6 GA MAYU, 2018
3 Baftisma Tana da Muhimmanci ga Kiristoci
MAKON 7-13 GA MAYU, 2018
8 Iyaye, Kuna Taimaka wa Yaranku Su Yi Baftisma?
Me ya kamata ya zama maƙasudinmu sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da wani? Me ya sa bai kamata mu jinkirta yin baftisma ba? Me ya sa wasu iyaye suke ƙarfafa yaransu su jinkirta yin baftisma? Za mu amsa waɗannan tambayoyin a waɗannan talifofi biyu.
13 Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
MAKON 14-20 GA MAYU, 2018
14 Farin Cikin da Karɓan Baƙi Ke Kawowa!
Manzo Bitrus ya ƙarfafa Kiristoci a ƙarni na farko cewa: “Ku dinga karɓar juna a cikin gidajenku.” (1 Bit. 4:9, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Me ya sa furucin nan yake da muhimmanci sosai a zamaninmu? A waɗanne hanyoyi ne za mu iya bin shawarar? Kuma ta yaya za mu zama baƙi na ƙwarai? Za a amsa tambayoyin nan a wannan talifin.
19 Tarihi—Jehobah Bai Taɓa Yasar da Ni Ba!
MAKON 21-27 GA MAYU, 2018
23 Horo, Alama Ce Ta Ƙaunar Allah
MAKON 28 GA MAYU, 2018–3 GA YUNI, 2018
28 ‘Ku Ji Horarwa Don Ku Zama Masu Hikima’
Waɗannan talifofi biyu za su taimaka mana mu ga cewa Jehobah yana ƙaunar mu sosai sa’ad da ya yi mana horo. Amma ta yaya Jehobah yake mana horo? Yaya ya kamata mu ɗauki horarwarsa? Kuma ta yaya za mu horar da kanmu? Za a amsa tambayoyin a talifin nan.