Abin Da Ke Ciki
MAKON 29 GA MAYU, 2017–4 GA YUNI, 2017
3 ‘Ka Biya Abin da Ka Yi Wa’adi’ ko Alkawarinsa
Alkawari guda nawa ne ka yi wa Jehobah? Ɗaya ko biyu ko kuma uku? Shin kana iya ƙoƙarinka don ka cika su? Alkawarin da ka yi cewa za ka bauta wa Jehobah kuma fa? Ban da haka ma, ka yi alkawari sa’ad da ka yi aure, ko ba haka ba? A wannan talifin, za mu koyi darussa masu muhimmanci daga labaran Jephthah da kuma Hannatu da za su taimaka mana mu cika alkawuran da muka yi wa Allah.
MAKON 5-11 GA YUNI, 2017
9 Mene ne Mulkin Allah Zai Kawar?
Sau da yawa mukan yi tunani a kan abin da Jehobah zai yi mana a Aljanna, amma a wannan talifin, za mu bincika abubuwan da Jehobah zai kawar. Waɗanne abubuwa ne Jehobah zai kawar domin mu yi farin ciki kuma mu zauna lafiya a wannan duniyar? Sanin amsar wannan tambayar zai ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ya sa mu ƙuduri niyyar jimre matsalolin da muke fuskanta.
14 TARIHI—Na Ƙuduri Aniyar Zama Sojan Kristi
MAKON 12-18 GA YUNI, 2017
18 “Mai-Shari’an Dukan Duniya” Yana Yin Abin da Ya Dace a Kowane Lokaci
MAKON 19-25 GA YUNI, 2017
23 Kana da Ra’ayin Jehobah Game da Yin Adalci?
Idan muna ganin an yi mana rashin adalci ko kuma mun ga wani da aka yi masa hakan, bangaskiyarmu za ta iya raunana kuma hakan yana iya shafan halinmu da kuma amincinmu. A waɗannan talifofin, za mu bincika labaran Littafi Mai Tsarki guda uku da za su taimaka mana mu kasance da ra’ayin Jehobah game da yin adalci.
MAKON 26 GA YUNI, 2017–2 GA YULI, 2017
28 Ta Yaya Ba da Kai Yake Sa a Yabi Jehobah?
Jehobah ba ya bukatar wani abu daga wurinmu, amma yana farin ciki idan muna iya ƙoƙarinmu don mu goyi bayan sarautarsa. A littafin Alƙalawa sura ta 4 da 5, za mu bincika yadda Jehobah yake farin ciki idan muna bauta masa da dukan zuciyarmu kuma muna bin ja-gorarsa.