Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 3 p. 16
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Shin za a daina yin rashin adalci a duniya kuwa?
  • Shin Allah yana da mutanen da ya fi ƙauna fiye da wasu ne?
  • “Dukan Hanyoyinsa Gaskiya Ne”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Za A Taba Samun Adalci a Dukan Duniya Kuwa?
    Karin Batutuwa
  • Yesu “Ya Kafa Yin Gaskiya a Duniya”
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Ka Yi Adalci” Wajen Tafiya da Allah
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 3 p. 16
Mutanen kabilu dabam-dabam

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Shin za a daina yin rashin adalci a duniya kuwa?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa, da hakkin matalauta.” (Zabura 140:​12, Littafi Mai Tsarki) Mulkin Allah zai sa a daina rashin adalci a duniya.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Allah yana ganin abin da yake faruwa a yau, kuma zai gyara su.​—Mai-Wa’azi 5:8.

  • Adalcin da Allah zai yi zai kawo mana salama da kwanciyar hankali a duniya.​—Ishaya 32:​16-18.

Shin Allah yana da mutanen da ya fi ƙauna fiye da wasu ne?

Wasu sun yi imani cewa Allah yana wa wasu albarka kuma yana tsine wa wasu. Wasu kuma sun gaskata cewa Allah ba ya fifita kowa. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.” (Ayyukan Manzanni 10:​34, 35) A wajen Allah, dukanmu ɗaya ne.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da “bishara” ga “kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma.”​—Ru’ya ta Yohanna 14:6.

Don ƙarin bayani game da lokacin da za a riƙa yin adalci a duniya, ka duba babi na 3 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi

Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba