Abin Da Ke Ciki
3 Sun ba da Kansu da Yardar Rai—A Ƙasar Gana
MAKON 29 GA AGUSTA, 2016–4 GA SATUMBA, 2016
7 Ka Biɗi Mulkin Allah, Ba Abin Duniya Ba
Yesu ya koya mana cewa mu ‘biɗi mulkin’ Allah ba abin duniya ba. Ta yaya za mu guje wa tarkon son abin duniya? Ta yaya za mu sauƙaƙa rayuwarmu don mu mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci? Za mu duba abin da Yesu ya ce sa’ad da yake yin huɗuba a kan dutse da ke littafin Matta 6:25-34.
MAKON 5-11 GA SATUMBA, 2016
13 Me Ya Sa Ya Wajaba Mu Ci Gaba da ‘Yin Tsaro’?
A matsayinmu na Kiristoci, wajibi ne mu bi shawarar da Yesu ya ba mu na yin “tsaro” a wannan kwanaki na ƙarshe. (Mat. 24:42) Don kada hankalinmu ya rabu, muna bukatar mu guje wa abubuwa marar kyau da za su iya raba hankalinmu kamar yadda Yesu ya ce. Wannan talifin ya bayyana yadda za mu iya guje wa abubuwan da za su raba hankalinmu kuma su hana mu kasancewa a faɗake.
18 ‘Kada Ka Ji Tsoro, Zan Taimake Ka’
MAKON 12-18 GA SATUMBA, 2016
21 Ka Nuna Godiya don Alherin Allah
MAKON 19-25 GA SATUMBA, 2016
26 Ka Yi Wa’azi Game da Alherin Allah
Waɗannan talifofi biyun su bayyana yadda muke amfana daga alherin Allah. Ƙari ga haka, sun bayyana dalilin da ya sa alherin da Allah yake mana zai motsa mu mu gaya wa mutane game da yadda su ma za su iya amfana daga alherinsa.