Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w16 Mayu p. 2
  • Abin Da Ke Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin Da Ke Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
w16 Mayu p. 2

Abin Da Ke Ciki

MAKON 27 GA YUNI, 2016–3 GA YULI, 2016

3 Ku Sasanta Matsalolinku Cikin Ƙauna

Domin mu ajizai, mun tabbata cewa za mu fuskanci yanayi da za su iya sa mu samu saɓani da ’yan’uwanmu. Wannan talifin ya nuna yadda za mu iya yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don mu sasanta saɓani da ’yan’uwanmu.

MAKON 4-10 GA YULI, 2016

8 ‘Ku Tafi . . . , Ku Almajirtar da Dukan Al’ummai’

A wannan talifin an tattauna wasu abubuwan da suka nuna cewa Shaidun Jehobah ne kaɗai a duniya suke cika annabcin Yesu da ke Matta 24:14. An kuma bayyana abin da zama “masuntan mutane” ya ƙunsa.—Mat. 4:19.

MAKON 11-17 GA YULI, 2016

13 Yaya Kake Tsai da Shawarwari?

A lokacin da kake tsai da shawarwari, shin kana yin abin da kake ganin ya dace ne? Ko kuma kana tambayar mutane don ka san ra’ayinsu? Wannan talifin ya bayyana yadda za mu tsai da shawarwari masu kyau idan muka yi la’akari da ra’ayin Jehobah Allah.

MAKON 18-24 GA YULI, 2016

18 Kana Barin Littafi Mai Tsarki Ya Kyautata Halayenka Har Ila?

Wataƙila ka yi canje-canje da dama kafin ka yi baftisma, amma shin kana ganin yana maka wuya yanzu ka yi wasu canje-canje domin ka yi koyi da Jehobah da Yesu sosai? A wannan talifin za a bayyana dalilin da ya sa yake da wuya sosai a yi waɗannan canje-canjen da kuma yadda za mu ci gaba da koyon halaye masu kyau da taimakon Kalmar Allah.

MAKON 25-31 GA YULI, 2016

23 Kana Amfana Daga Dukan Abubuwan da Jehobah Yake Tanadinsu Kuwa?

A wannan talifin, an bayyana mana wani tarko da zai hana mu jin daɗin abubuwa masu amfani da Jehobah yake tanadar mana a yau. Za mu tattauna yadda za mu guji faɗawa cikin wannan tarko, kuma za mu koya yadda za mu amfana daga dukan abubuwan da Jehobah yake tanadar mana.

28 Daga Tarihinmu

30 Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba