Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 11/1 p. 5
  • Me Ya Sa Allah Ya Ce Mu Rika Addu’a?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Allah Ya Ce Mu Rika Addu’a?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Allah yana so mu zama aminansa.
  • Allah yana so ya taimake ka.
  • ’Yan Adam suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.
  • Shin, Allah Yana Jin Addu’arka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Jawowa Kurkusa da Allah Cikin Addu’a
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 11/1 p. 5

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | SHIN YIN ADDU’A ƁATA LOKACI NE?

Me Ya Sa Allah Ya Ce Mu Riƙa Addu’a?

Allah yana so mu zama aminansa.

Aminai suna tattaunawa da juna don dangantakarsu ta yi danƙo. Hakazalika, Allah yana so mu riƙa tattauna da shi don dangantakarmu da shi ta yi ƙarfi. Ya ce: “Za ku kira gareni, ku tafi ku yi mani addu’a, ni ma in ji ku.” (Irmiya 29:12) Idan kana tattaunawa da Allah, za ka ‘kusace [shi], shi ma zai kusace ka.’ (Yaƙub 4:8, Littafi Mai Tsarki) Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi.’ (Zabura 145:18) Idan mun ci gaba da yin addu’a ga Allah, babu shakka, dangantakarmu da shi za ta yi ƙarfi.

“Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda suke kira bisa gareshi.”—Zabura 145:18

Allah yana so ya taimake ka.

Yesu ya ce: “To, wane ne a cikinku ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse? Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji? To, [idan kun] . . . san yadda za ku ba ’ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?” (Matta 7:9-11, LMT) Hakika, Allah yana so ka riƙa addu’a domin “yana kula da” kai kuma yana so ya taimake ka. (1 Bitrus 5:7) Ya ma ce ka gaya masa dukan matsalolinka. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kada ka yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ka bar roƙe-roƙenka su sanu ga Allah.’—Filibiyawa 4:6.

’Yan Adam suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.

Masana a kan yanayin ’yan Adam sun lura cewa miliyoyin mutane suna jin cewa ya dace su riƙa yin addu’a. Har wasu mutanen da ba su gaskata da wanzuwar Allah ba da kuma masu shakkar wanzuwarsa sun yarda da hakan.a Wannan ya nuna cewa an halicci ’yan Adam da sha’awar ƙulla dangantaka da Allah. Yesu ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.” (Matta 5:3, New World Translation) Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce ta wurin tattaunawa da Allah a kai a kai.

Ta yaya za mu amfana idan muka amince da gayyatar da Allah yake mana cewa mu riƙa yin addu’a?

a Wani bincike da aka yi a shekara ta 2012 ya ce kashi 11 cikin 100 na mutanen da ba su gaskata da wanzuwar Allah ba da kuma waɗanda suke shakkar wanzuwarsa a ƙasar Amirka suna addu’a aƙalla sau ɗaya a wata.

Mene ne Yin Addu’a Ya Ƙunsa?

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa addu’a ta ƙunshi dukan fannonin rayuwarmu. Addu’a ta ƙunshi abubuwan da ke gaba:

  • Yin Iƙirari da Laifi “Na furta zunubaina gare ka, ban ɓoye laifofina ba.”—Zabura 32:5, LMT.

  • Godiya “Yin godiya ga Ubangiji yana da kyau.”—Zabura 92:1.

  • Yabo “Zan albarkaci Ubangiji a kowane loto: yabonsa kuwa za ya zauna a bakina tuttur.”—Zabura 34:1.

  • Neman Ja-gora “Ka sa ni in yi tafiya cikin hanyar dokokinka; gama a cikinta ni ke jin daɗi.”—Zabura 119:35.

  • Neman Ƙarfafa “Ka juyo wajena, ka yi mani jinƙai: ka bada ƙarfinka ga bawanka.” —Zabura 86:16.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba