Abin Da Ke Ciki
15 ga Yuli, 2015
© 2015 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
NA NAZARI
31 GA AGUSTA, 2015–6 GA SATUMBA, 2015
Ka Yi Aiki don Kyautata Yanayin Salama da Muke Mora
SHAFI NA 7
7-13 GA SATUMBA, 2015
SHAFI NA 14
14-20 GA SATUMBA, 2015
Ka Ci gaba da Kasancewa da Aminci ga Mulkin Allah
SHAFI NA 22
21-27 GA SATUMBA, 2015
SHAFI NA 27
TALIFOFIN NAZARI
▪ Ka Yi Aiki don Kyautata Yanayin Salama da Muke Mora
Bayin Jehobah suna jin daɗin yanayi na salama ta musamman a sashen kungiyarsa da ke duniya. Ta yaya za mu nuna godiyarmu don wannan tanadin da Jehobah ya yi mana? Mene ne kowannenmu zai iya yi don ya kyautata wannan yanayin? Za mu sami amsoshin a wannan talifin.
▪ “Fansarku Ta Kusa”!
A wannan talifin, za a tattauna wasu abubuwa masu ban mamaki da za su faru nan ba da daɗewa ba. Kari ga haka, talifin zai taimaka mana mu san dalilin da ya sa za mu dogara ga Jehobah a lokacin kunci mai girma.
▪ Ka Ci gaba da Kasancewa da Aminci ga Mulkin Allah
A wannan duniyar da Shaiɗan yake mulki, mutane sukan ɗauki kasarsu ko al’adarsu ko kuma launin fatarsu da muhimmanci fiye da kome. Amma Kiristoci sun yi alkawari cewa za su kasance da aminci ga Jehobah. Za mu bincika dalilin da ya sa bai kamata mu saka hannu a tashen-tashen hankula da ake yi a duniya ba. Kari ga haka, ya nuna mana yadda za mu horar da kanmu don mu kasance da ra’ayin Jehobah da kuma Yesu a wannan batun.
▪ Wannan Wurin Ne Muke Bauta
Bayin Jehobah suna yin ibada a Majami’un Mulki. Za mu tattauna ka’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu san yadda za mu ɗaukaka Jehobah ta halinmu a Majami’ar Mulki, ta kula da kuma ba da gudummawa don gina Majami’un Mulki.
A FITOWAR NAN
3 Sun Ba da Kansu da Yardar Rai—A Kasar Rasha
12 Ka Ci gaba da Bauta wa Jehobah a “Miyagun Kwanaki”
20 Yana da Muhimmanci a San da Aikinka Ne?
32 Ka Sani?
BANGO: Wani rukunin masu wa’azi suna ɗan shakatawa da rana yayin da suke wa’azi a wasu sassan yankin Saiberiya
RASHA
YAWAN JAMA’A
143,930,000
MASU SHELA