Abin Da Ke Ciki
15 ga Yuni, 2015
© 2015 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
NA NAZARI
27 GA YULI, 2015–2 GA AGUSTA, 2015
SHAFI NA 3 • WAƘOƘI: 14, 109
3-9 GA AGUSTA, 2015
SHAFI NA 8 • WAƘOƘI: 84, 99
10-16 GA AGUSTA, 2015
Za Mu Iya Kasancewa da Ɗabi’a Mai Kyau
SHAFI NA 13 • WAƘOƘI: 83, 57
17-23 GA AGUSTA, 2015
Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?—Sashe na I
SHAFI NA 20 • WAƘOƘI: 138 Jehovah Is Your Name (Jehobah Ne Sunanka, sabuwar waƙa), 89
24-30 GA AGUSTA, 2015
Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?—Sashe na II
SHAFI NA 25 • WAƘOƘI: 22, 68
TALIFOFIN NAZARI
▪ Kristi Shi Ne Ikon Allah
▪ Ya So Mutane
Waɗannan talifofin sun yi magana game da mu’ujizan Yesu, kuma za mu koya mana darussa masu kyau game da karimci da kuma taimaka wa mutane. Ƙari ga haka, an tattauna wasu abubuwa masu ban sha’awa game da halin Yesu. Talifofin za su sa mu kasance da bege game da nan gaba, a lokacin da za mu shaida mu’ujizan da za a yi a faɗin duniya.
▪ Za Mu Iya Kasancewa da Ɗabi’a Mai Kyau
Muna rayuwa a duniya da zina da fasikanci sun zama ruwan dare. Saboda haka, bai da sauƙi mu kasance da ɗabi’a mai kyau. A wannan talifin, za mu koyi yadda dangantakarmu da Jehobah, da shawarar da ke cikin Kalmarsa da kuma taimakon ’yan’uwa Kiristoci da suka manyanta za su taimaka mana mu guji tunanin banza kuma mu manne wa ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a.
▪ Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?—Sashe na I
▪ Kana Rayuwa Bisa Addu’ar Misali Kuwa?—Sashe na II
Kiristoci ba sa maimaita addu’ar misali na Yesu kowace rana, amma batutuwan da aka tattauna a cikin addu’ar suna da ma’ana a gare mu duka. A waɗannan talifofin, za mu koyi yadda za mu yi rayuwar da ta jitu da roƙon da aka yi a cikin addu’ar.
BANGO: Shaidun Jehobah suna zuwa tsibiran Bocas del Toro da suke arewa maso yammar gaɓar teku a Panama don su yi wa’azi wa wasu mutane da ke zama a wuraren. Hakan ya haɗa da yin wa’azi da harshen Ngabere
PANAMA
YAWAN JAMA’A
3,931,000
MASU SHELA
16,217
MAJAGABA NA KULLUM
2,534
Akwai ikilisiyoyi 309 a ƙasar Panama da kuma majagaba na musamman fiye da 180. Masu shela wajen 1,100 suna hidima a ikilisiyoyi 35. Ƙari ga haka, rukuni guda 15 suna amfani da harshen Ngabere. Kusan masu shela guda 600 ne suke hidima a ikilisiyoyin yaren kurame kuma rukuni 6 suna amfani da yaren kurame na Panama