Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 1/1 p. 16
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta yaya za a koyar da yara su ƙaunaci Allah?
  • A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
    A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
  • Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
    Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
  • Mene Ne ra’ayinka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 1/1 p. 16

AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI

Ta yaya za a koyar da yara su ƙaunaci Allah?

Wani mahaifi yana yin amfani da halittu wajen koyar da dansa

Ka yi amfani da halittu wajen taimaka wa ɗanka ya san Allah kuma ya ƙaunace shi

Sai yaranku sun ga tabbaci cewa Allah ya wanzu da gaske kuma yana ƙaunarsu kafin su koyi yadda za su ƙaunace shi. Suna bukatar su san Allah kafin su ƙaunace shi. (1 Yohanna 4:8) Alal misali, suna bukatar su san: Dalilin da ya sa Allah ya halicci mutum, abin da ya sa Allah yake barin mutane su sha wahala, da kuma abin da Allah zai yi wa ’yan Adam a nan gaba.—Karanta Filibiyawa 1:9.

Idan kana so ka taimaki yaranka su ƙaunaci Allah, wajibi ne ka nuna musu cewa kana ƙaunar Allah. Idan sun ga hakan, za su bi misalinka.—Karanta Kubawar Shari’a 6:5-7; Misalai 22:6.

Ta yaya za ka ratsa zuciyar yaranka?

Kalmar Allah tana da iko sosai. (Ibraniyawa 4:12) Saboda haka, ka taimaka wa yaranka su san muhimman koyarwar da ke cikinta. Sa’ad da Yesu yake neman ya ratsa zuciyar mutane, ya yi tambaya, ya saurara, kuma ya bayyana Nassosi. Hakazalika, idan kana so ka ratsa zuciyar yaranka, wajibi ne ka yi koyi da yadda Yesu ya yi koyarwa.—Karanta Luka 24:15-19, 27, 32.

Ƙari ga haka, labaran Littafi Mai Tsarki a kan yadda Allah ya bi da mutane a dā zai iya taimaka wa yara su san Allah kuma su ƙaunace shi. Akwai littattafai da aka shirya don hakan a dandalin www.jw.org/ha.—Karanta 2 Timotawus 3:16.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 14 a wannan littafin, Shaidun Jehobah ne suka wallafa

Za ka iya samunsa a dandalin www.jw.org/ha, ko ka aika saƙo zuwa ɗaya daga cikin adiresoshin da ke shafi na 2 don a aika maka littafin kyauta

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba