‘Ku Ƙallafa Ranku ga Abubuwan da Ke Bisa’
‘Ku ƙallafa ranku ga abubuwan da ke bisa, ba wajen na ƙasa ba.’—KOL. 3:2.
1, 2. (a) Me ya nuna cewa ikilisiya na ƙarni na farko da ke Kolosi na cikin hadari? (b) Wace shawara ce aka ba wa ’yan’uwa da ke Kolosi don su kasance da dangantaka mai kyau da Allah?
IKILISIYAR Kirista na ƙarni na farko da ke Kolosi tana cikin hadari! Wasu cikin ikilisiyar sun ce lallai sai kowa ya bi Dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa. Wasu kuma sun ce laifi ne a yi annashuwa. Bulus ya rubuta wasiƙa mai ban ƙarfafa ga Kolosiyawa don ya gargaɗe su game da waɗannan koyarwar ƙarya, ya ce: “Ku lura kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al’adar mutane kawai, wato bisa ga al’adun duniyan nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.”—Kol. 2:8, Littafi Mai Tsarki.
2 Idan Kiristoci shafaffu suka ƙallafa ransu ga “al’adun duniyan nan,” hakan zai sa su yi watsi da tanadin da Jehobah ya yi don ceto. (Kol. 2:20-23) Don ya taimaka musu su ci gaba da kasancewa da bangaskiya ga Allah, Bulus ya gaya musu: “Ku ƙalafa ranku ga abubuwan da ke bisa, ba wajen na ƙasa ba.” (Kol. 3:2) Hakika, ya kamata waɗannan almajiran Yesu su sa rai a kan gādo marar lalacewa da aka ajiye musu a “cikin sama.”—Kol. 1:4, 5.
3. (a) Wane bege ne shafaffu Kiristoci suke sa rai a kai? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a wannan talifin?
3 A yau, shafaffun Kiristoci sun ƙallafa ransu ga Mulkin Allah da kuma gatan zama “masu-tarayyan gādo da Kristi.” (Rom. 8:14-17) Waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya kuma fa? Ta yaya za su amfana daga furucin da Bulus ya yi? A wace hanya ce “waɗansu tumaki” za su ƙallafa ransu ga “abubuwan da ke bisa”? (Yoh. 10:16) Kuma ta yaya dukanmu za mu amfana daga bincika labaran mutanen dā masu aminci kamar su Ibrahim da Musa da suka ƙallafa ransu ga abubuwan da ke sama duk da tsananin da suka fuskanta?
ABIN DA ƘALLAFA RANMU GA ABIN DA KE BISA YAKE NUFI
4. Ta yaya waɗansu tumaki za su ƙallafa ransu ga abubuwan da ke sama?
4 Waɗansu tumaki za su iya ƙallafa ransu ga abubuwan da ke sama ko da yake ba su da begen zuwa sama. Ta yaya? Ta wajen saka Jehobah Allah da kuma Mulkinsa kan gaba a rayuwarsu. (Luk 10:25-27) Don mu cim ma wannan burin, muna bukata mu bi gurbin Kristi. (1 Bit. 2:21) Kamar ’yan’uwa a ƙarni na farko, duniyar Shaiɗan tana matsa mana da ra’ayoyin ƙarya da falsafa na ruɗu da kuma son abin duniya. (Karanta 2 Korintiyawa 10:5.) Da yake mu masu bin gurbin Yesu ne, ya kamata mu kasance a faɗake don kada waɗannan abubuwa su ɓata dangantakarmu da Jehobah.
5. Ta yaya za mu bincika tunaninmu game da biɗan abubuwan duniya?
5 Shin ra’ayin mutane game da abin duniya ya soma shafar mu ne? Tunaninmu da kuma ayyukanmu za su iya nuna abubuwan da muka fi so. Yesu ya ce: “Wurin da dukiyarka ta ke, can zuciyarka za ta kasance kuma.” (Mat. 6:21) Don mu san irin tunanin da muke yi, zai yi kyau mu riƙa bincika kanmu a kai a kai. Za ka iya tambayar kanka: ‘Ina yawan tunanin kuɗi ne? Ina yawan damuwa game da sana’a da aiki da kuma rayuwar jin daɗi ne? Ko kuma ina mai da hankali ga abubuwan da za su ƙarfafa dangantakata da Allah?’ (Mat. 6:22) Yesu ya ce waɗanda suka fi damuwa da ‘tara wa kansu dukiya a duniya’ suna sa kansu cikin hadari.—Mat. 6:19, 20, 24.
6. Ta yaya za mu yi nasara a kan ajizancinmu?
6 Da yake mu ajizai ne, a wani lokaci za mu riƙa yin wasu abubuwa don gamsar da kanmu. (Karanta Romawa 7:21-25.) Idan ba tare da taimakon ruhu mai tsarki ba, za mu riƙa yin “ayyukan duhu.” Hakan zai haɗa da “shashanci da buguwa ko fasikanci da fajirci.” (Rom. 13:12, 13, LMT) Amma, idan muka mai da hankali ga abubuwan da ke sama, za mu iya yin nasara a kan abubuwan da ke “ƙasa,” wato abubuwa masu ƙayatar da ranmu. Yin hakan yana bukatar ƙwazo sosai. Shi ya sa manzo Bulus ya ce: “Ina dandaƙin jikina, ina kai shi cikin bauta.” (1 Kor. 9:27) Babu shakka, wajibi ne mu yi aiki tuƙuru don mu ci gaba da bauta wa Allah da aminci! Bari mu bincika abin da wasu amintattun bayin Allah guda biyu suka yi don su ‘gamsar’ da Allah.—Ibran. 11:6.
IBRAHIM YA “BA DA GASKIYA GA UBANGIJI”
7, 8. (a) Waɗanne matsaloli ne Ibrahim da Saratu suka fuskanta? (b) Ga mene ne Ibrahim ya mai da hankali?
7 A lokacin da Jehobah ya umurci Ibrahim ya ɗauki iyalinsa kuma ya je ƙasar Kan’ana, Ibrahim ya yi biyayya. Da yake Ibrahim ya ba da gaskiya kuma ya yi biyayya, Jehobah ya yi masa alkawari cewa: “Daga wurinka zan yi al’umma mai-girma, zan albarkace ka kuma.” (Far. 12:2) Amma an yi shekaru da dama bayan haka Ibrahim da matarsa Saratu ba su haihu ba. Shin Jehobah ya manta da alkawarin da ya yi wa Ibrahim ne? Ƙari ga haka, rayuwa a ƙasar Kan’ana ba ta da sauƙi. Ibrahim da iyalinsa sun bar gidansu da kuma danginsu a Ur, wani birni mai ni’ima da ke ƙasar Mesopotamiya. Sun yi tafiyar kilomita 1,600 zuwa ƙasar Kan’ana inda suka yi rayuwa a tantuna. Ƙari ga haka, sun yi fama da karancin abinci da kuma ɓarayi. (Far. 12:5, 10; 13:18; 14:10-16) Duk da haka, ba su so koma birnin Ur inda ake rayuwar jin daɗi ba!—Karanta Ibraniyawa 11:8-12, 15.
8 Ibrahim bai mai da hankali ga abubuwan da ke “ƙasa” ba, maimakon haka, ya “ba da gaskiya ga Ubangiji.” (Far. 15:6) Hakika, ya mai da hankali ga abubuwan da ke sama, wato ya sa rai ga alkawuran Allah. A sakamakon haka, Allah Maɗaukakin Sarki ya albarkaci Ibrahim sa’ad da ya bayyana a gare shi kuma ya ce: “Ka duba yanzu zuwa sama, ka yi lissafin taurari, ko ka iya lissafinsu: kuma ya ce masa, Hakanan zuriyarka za ta yi.” (Far. 15:5) Hakan ya ƙarfafa Ibrahim sosai! A duk lokacin da ya kalli sama, sai ya tuna da alkawarin da Allah ya yi masa cewa zai sa zuriyarsa ta yi yawa kamar taurarin sama. Kuma a lokacin da ya dace, Ibrahim ya haifi ɗa kamar yadda aka yi masa alkawari.—Far. 21:1, 2.
9. Ta yaya bin misalin Ibrahim zai iya ƙarfafa mu mu yi ƙwazo a hidimar Allah?
9 Kamar Ibrahim, mu ma muna jiran cikar alkawuran Allah. (2 Bit. 3:13) Idan ba mu mai da hankali ga abubuwan da ke sama ba, za mu ga kamar zai daɗe kafin alkawuran Allah su cika kuma hakan zai sa mu yi sanyin gwiwa a ibadarmu. Alal misali, shin ka yi sadaukarwa ne a dā don ka soma hidimar majagaba ko kuma ka faɗaɗa hidimarka a wasu hanyoyi? Idan haka ne, kana ƙoƙari. Yanzu kuma fa? Ka tuna cewa Ibrahim ya mai da hankali ga “birnin da ke da tussa.” (Ibran. 11:10) Ya “ba da gaskiya ga Allah, aka lissafta wannan gare shi adalci.”—Rom. 4:3.
MUSA YA GA “WANDA BA SHI GANUWA”
10. Wace irin rayuwa ce Musa ya yi sa’ad da yake matashi?
10 Wani kuma da ya mai da hankali ga abubuwan da ke sama shi ne Musa. A lokacin da yake matashi, an koya masa “dukan hikimar Masarawa,” kuma ba ƙaramin ilimi ba ne ya samu. Ya girma a gidan Fir’auna kuma a lokacin, Masar ita ce ƙasa mafi iko. Babu shakka, don wannan ilimin ne Musa ya kasance “mai-iko cikin zantattukansa da ayyukansa.” (A. M. 7:22) Da a ce Musa ya ci gaba da kasancewa a gidan Fir’auna, da ya zama wani babban mutum a ƙasar Masar! Duk da haka, Musa ya mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci, wato yin nufin Allah.
11, 12. Wace irin koyarwa ce Musa ya ɗauka da muhimmanci kuma ta yaya muka san hakan?
11 A lokacin da Musa yake yaro, mahaifiyarsa Jochebed, ta koyar da shi game da Allah na Ibraniyawa. Kuma ya ɗauki wannan koyon da muhimmanci fiye da wadata. Hakika, Musa ya yi watsi da gata da kuma wasu abubuwan da zai samu a gidan Fir’auna. (Karanta Ibraniyawa 11:24-27.) Koyo game da Allah da kuma bangaskiya ne suka taimaka wa Musa ya mai da hankali ga abubuwan da ke sama.
12 Da yake Musa ya je babbar makarantar boko a zamaninsa, shin ya yi amfani da wannan ilimin don ya cim ma wani babban abu a ƙasar Masar ko ya yi suna ko kuma ya sami wadata ne? A’a. Da a ce ya yi hakan, da bai “ƙi yarda a ce da shi ɗan ɗiyar Fir’auna” ba, kuma da bai “gwammace a wulakance shi tare da mutanen Allah, da ya ji daɗin nishatsin zunubi domin ’yan kwanaki” ba. Hakika, Musa ya yi amfani da koyarwar Allah don ya yi nufin Jehobah.
13, 14. (a) Me ya taimaka wa Musa ya cancanci aikin da Jehobah ya ba shi? (b) Kamar Musa, me ya kamata mu yi?
13 Musa yana ƙaunar Jehobah da kuma mutanensa. A lokacin da yake shekara 40, Musa ya ɗauka cewa zai iya ceton mutanensa da suke bauta a ƙasar Masar. (A. M. 7:23-25) Amma kafin Jehobah ya ba shi wannan aikin, yana bukata ya kasance da tawali’u da haƙuri da farar zuciya da kuma kamewa. (Mis. 15:33) Musa yana bukatar horo da zai taimaka masa ya jimre wa gwaji da matsalolin da zai fuskanta daga baya. Shekarun da zai yi yana kiwo za su taimaka masa ya kasance da waɗannan halayen da ake bukata.
14 Shin Musa ya koyi waɗannan halayen a lokacin da yake kiwo ne? Hakika! Kalmar Allah ta ce Musa “mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya.” (Lit. Lis. 12:3) Tawali’un da ya koya ne ya taimaka masa ya bi da mutane dabam-dabam da kuma matsalolinsu masu wuya. (Fit. 18:26) Hakazalika, muna bukatar kasancewa da halaye masu kyau da za su taimaka mana mu tsira wa ‘babban tsanani’ kuma mu shiga sabuwar duniya. (R. Yoh. 7:14) Shin muna iya bi da mutane dabam-dabam ne, har da waɗanda suke saurin fushi? Ya kamata mu mai da hankali ga furucin Bitrus sa’ad da yake magana ga ’yan’uwansa cewa: “Ku girmama kowa, ku ƙaunaci ’yan’uwa” duka.—1 Bit. 2:17, LMT.
ƘALLAFA RANMU GA ABUBUWAN DA KE BISA
15, 16. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da ƙallafa ranmu ga abubuwan da suka dace? (b) Me ya sa ya dace Kiristoci su riƙa nuna halin kirki?
15 Muna rayuwa a “miyagun zamanu.” (2 Tim. 3:1) Saboda haka, don mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah, yana da muhimmanci mu ƙallafa ranmu ga abubuwan da suka dace. (1 Tas. 5:6-9) Ka yi la’akari da hanyoyi uku da za mu iya yin hakan.
16 Halinmu: Bitrus ya fahimci muhimmancin kasancewa da halin kirki. Ya ce: “Kuna al’amura na dacewa wurin al’ummai; domin . . . ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah.” (1 Bit. 2:12) Ya kamata mu riƙa ƙoƙari muna girmama Allah ta halinmu, ko a gida ko a wurin aiki ko a makaranta ko a wurin nishaɗi ko kuma a wa’azi. A gaskiya, da yake dukanmu masu zunubi ne, muna yin kuskure. (Rom. 3:23) Idan muka ci gaba da yin “yaƙin kirki na imani,” Jehobah zai sa mu yi nasara.—1 Tim. 6:12.
17. Ta yaya za mu kasance da irin ra’ayin Kristi? (Ka duba hoton da ke shafi na 28.)
17 Ra’ayinmu: Ra’ayi mai kyau yana da alaƙa da halin kirki. Manzo Bulus ya ce: “Ku kasance da wannan hali a cikinku wanda ke cikin Kristi Yesu kuma.” (Filib. 2:5) Wane irin hali ne Yesu ya nuna? Shi mai tawali’u ne. Tawali’u ya sa ya ba da kansa a yin wa’azi. Ya saka yin wa’azi game da Mulkin Allah kan gaba a rayuwarsa. (Mar. 1:38; 13:10) Yesu ya ɗauki Kalmar Allah a matsayin tushen abin da yake koyarwa. (Yoh. 7:16; 8:28) Ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai don ya yi ƙaulinsa, ya ɗaukaka da kuma bayyana nassosi. Idan muka kasance da tawali’u kuma muka yi ƙwazo a wa’azi da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki, ra’ayinmu zai kasance irin na Kristi.
18. A wace hanya mai muhimmanci ce za mu yi ƙwazo a aikin Jehobah?
18 Ƙoƙarinmu: Nufin Jehobah shi ne, “cikin sunan Yesu kowace gwiwa ta rusuna, ta cikin sama da ta kan duniya.” (Filib. 2:9-11) Duk da matsayin da Yesu yake da shi a sama, zai ci gaba da sarayar da kansa ga yin nufin Ubansa, mu ma ya kamata mu yi hakan. (1 Kor. 15:28) Ta yaya? Ta wurin yin iya ƙoƙarinmu a aikin da aka umurce mu, wato “almajirtar da dukan al’ummai.” (Mat. 28:19) Ƙari ga haka, muna son mu riƙa “aika nagarta zuwa ga dukan mutane,” wato Shaidu da waɗanda ba Shaidu ba.—Gal. 6:10.
19. Mene ne ya kamata mu kuɗiri niyyar yi?
19 Muna godiya cewa Jehobah yana ƙarfafa mu mu riƙa ƙallafa ranmu ga abubuwan da ke sama! Muna bukata “mu yi tseren da an sa gabanmu.” (Ibran. 12:1) Bari dukanmu mu yi aiki da ƙwazo wajen “aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji,” kuma Ubanmu na sama zai albarkace mu don ƙoƙarin da muka yi.—Kol. 3:23, 24.