TARIHI
Muhimman Abubuwan da Na Shaida a Bautar Jehobah
A shekara ta 1947, limaman Katolika da ke birnin Santa Ana, a ƙasar El Salvador, sun zuga mutane su yi wa Shaidun Jehobah fitina. Sa’ad da ake yin Nazarin Hasumiyar Tsaro, sai yara maza suka soma jifar kofar gidan Shaidun da suka zo wa’azi a ƙasar. Sai ga wasu sun yi jerin gwano tare da limamai. Wasu suna ɗauke da tocilan; wasu kuma da siffofi. Sun yi awa biyu suna jifar gidan da duwatsu, suna waƙa cewa: “Ranki ya Ɗaɗe Maryamu!” kuma, “Bari Jehobah ya mutu!” Sun yi hakan don su tsoratar da masu wa’azi da suka zo ƙasar kuma su bar garin. Na san da hakan don ina cikin waɗanda suka halarci taron nan da aka yi shekaru 67 da suka wuce.a
SHEKARU biyu kafin wannan abin ya faru, ni da Evelyn Trabert, abokiyar aikina mun sauke karatu daga Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. A lokacin, makarantar tana kusa da garin Ithaca da ke jihar New York. An tura mu hidima a birnin Santa Ana. Kafin in ci gaba da gajeren labarina game da hidimata na kusan shekaru 29 a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje, bari in bayyana muku dalilin da ya sa na soma wannan hidimar.
GĀDONA
Iyayena, John da Eva Olson suna zama a birnin Spokane, Washington, U.S.A., inda aka haife ni, a shekara ta 1923. Su ’yan Lutheran Church ne amma ba su amince da koyarwar jahannama ba, don ba su yarda cewa Allah mai ƙauna zai azabtar da mutane a wuta ba. (1 Yoh. 4:8) Mahaifina yana aiki a wani gidan burodi, sai wata rana da dare wani abokin aikinsa ya tabbatar masa cewa Littafi Mai Tsarki bai koyar da cewa Hades wajen azabtar da mutane ba. Nan ba da daɗewa ba, sai iyayena suka amince Shaidun Jehobah su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma suka koyi ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar a kan abin da yake faruwa bayan mutuwa.
Ni ’yar shekara tara ce a lokacin, amma ban manta da yadda nake sauraron iyayena yayin da suke bayyana ra’ayinsu game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da suka koya ba. Iyayena sun ƙara farin ciki da suka koyi cewa sunan Allah Jehobah ne, kuma hakan ya ’yantar da su daga koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya. Waɗannan koyarwar sun soma shiga zuciyata kuma na soma sanin “gaskiyar” da ke “’yantar” da mutane. (Yoh. 8:32) Saboda haka, ba na jinkirin nazarin Littafi Mai Tsarki, amma ina marmarin bincikawa a kowane lokaci. Ko da yake, ni mai jin kunya ce, duk da haka, ina zuwa wa’azi tare da iyayena. Sun yi baftisma a shekara ta 1934. Ni kuma na yi baftisma a shekara ta 1939 sa’ad da nake ’yar shekara 16.
Iyayena sun sayar da gidansu a watan Yuli na 1940, sai mu uku muka soma hidimar majagaba a birnin Coeur d’Alene, Idaho. Mun zauna a wani bene da ake gyaran mota a ƙasarsa. Ƙari ga haka, ana yin taro a gidanmu. A lokacin, babu Majami’un Mulki da yawa, saboda haka, ana yin taro a gidajen ’yan’uwa da kuma gidajen haya.
A shekara ta 1941 ne ni da iyayena muka halarci wani babban taro a birnin St. Louis, Missouri. An keɓe ranar Lahadi domin yara kuma ’yan shekara 5 zuwa 18 sun zauna a kujerun gaba a taron. Sa’ad da Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford yake ba da jawabinsa, ya ce mana: “Dukanku . . . yara . . . da kuka yarda ku bi Allah da Sarkinsa, don Allah ku tashi!” Sai dukanmu muka tashi. “Ku duba, mun sami Shaidu sababbi fiye da 15,000 da ke wa’azi game da Mulkin!” Wannan abin da ya faru ya sa na ƙudura niyyar ɗaukan hidimar majagaba a matsayin aikina.
WURIN DA IYALINMU SUKA YI HIDIMA
’Yan watanni bayan wannan taron da aka yi a birnin St. Louis, sai iyalinmu suka ƙaura zuwa kudancin California. An ba mu wani sabon aiki na kafa ikilisiya a birnin Oxnard. Muka soma zama a wani gidan tirela da ke da gado ɗaya kawai. Ana gyara “gadona” kowane dare a kan teburin cin abinci, wannan ba ƙaramin canji ba ne don a dā, ina da ɗakina ni kaɗai!
Jim kaɗan kafin mu isa California, rundunar Japan ta kai hari a Pearl Harbor da ke birnin Hawaii, a ranar 7 ga Disamba, shekara ta 1941. Washegari sai Amirka ta saka hannu a Yaƙin Duniya na Biyu. Hukuma suka ba da umurni cewa kada a kunna wutar lantarki kuma hakan ya sa ba ma kunna wuta da dare. Jiragen tafiya a ƙarƙashin teku na Japan suna ta yawo a bakin tekun California kuma saboda haka, jiragen ba su iya kawo hari a birnin ba.
Wasu watanni bayan haka, wato a Satumba na shekara ta 1942, mun halarci babban taron New World Theocratic Assembly a birnin Cleveland, a jihar Ohio. A wajen ne na saurari Ɗan’uwa Nathan H. Knorr sa’ad da ya ba da jawabin nan: “Peace—Can It Last?” (Salama, Za Ta Dawwama Kuwa?) Ya tattauna Ru’ya ta Yohanna sura 17, da ta kwatanta wata “Dabba” da ta “kasance a dā, ba shi yanzu” kuma, tana “bakin fitowa daga cikin rami marar-matuƙa.” (R. Yoh. 17:8, 11) Ɗan’uwa Knorr ya bayyana cewa ‘dabbar’ ita ce Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya, wadda ta daina ayyukanta a shekara ta 1939. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a maye gurbinta kuma hakan zai sa a yi salama na ɗan lokaci. Hakan ya faru don a shekara ta 1945 aka daina Yaƙin Duniya na Biyu. Bayan haka, ‘dabbar’ ta sake bayyana a matsayin Majalisar Ɗinkin Duniya. Sai Shaidun Jehobah suka faɗaɗa wa’azin da suke yi, kuma tun lokacin sai ƙaruwa suke yi!
Wannan annabcin ya taimaka mini na san abin da zai faru a nan gaba. Sa’ad da aka sanar cewa za a soma Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead a baɗi, sai na soma sha’awar zama mai wa’azi a wata ƙasa. A shekara ta 1943, aka tura ni hidima a birnin Portland da ke Oregon. A lokacin, mun yi amfani da garmaho don mu yi wa mutane wa’azi a bakin ƙofarsu, bayan haka sai mu ba su littattafanmu da suka yi magana a kan Mulkin Allah. A wannan shekarar, sai tunanin yin hidima a wata ƙasa nake ta yi.
A shekara ta 1944, na yi farin ciki sosai da aka gayyace ni zuwa makarantar tare da ƙawata Evelyn Trabert. A cikin watanni biyar, malamanmu sun nuna mana yadda za mu ji daɗin nazarin Littafi Mai Tsarki. Su masu tawali’u ne, kuma hakan ya burge mu. A wani lokaci, sukan ɗauki matsayin masu ba da abinci sa’ad da muke cin abinci. Mun sauke karatu a ranar 22 ga Janairu, 1945.
HIDIMAR DA NA YI A ƘASAR WAJE
Da ni da Evelyn, tare da Leo da Esther Mahan muka isa wurin da aka tura mu hidima a ƙasar El Salvador a watan Yuni 1946. Mun ga cewa wurin ya “isa girbi.” (Yoh. 4:35) Abin da ya faru a wurin da na ambata a farkon wannan labarin ya nuna cewa limaman sun yi fushi sosai. Mako ɗaya kafin lokacin, mun yi taron da’ira a birnin Santa Ana. Mun sanar da jawabi ga jama’a da za a ba da a taron a ko ta ina kuma mun yi farin ciki sa’ad da kusan mutane 500 suka halarci taron. Maimakon mu ji tsoro mu bar birnin, mun ƙuduri niyya mu zauna kuma mu taimaka wa mutane masu zuciyar kirki. Limaman sun gargaɗi mutanen kada su karanta Littafi Mai Tsarki duk da haka, mutane da yawa suna son su san gaskiyar, amma waɗanda suke da Littafi Mai Tsarki ba su da yawa. Sun yi farin ciki sosai don ƙoƙarin da muke yi na koyan Sfanisanci saboda mu koya musu game da Allah na gaskiya, Jehobah, da kuma alkawarin da ya yi na mai da duniya Aljanna.
Rosa Ascencio tana cikin waɗanda na soma nazari da su a El Salvador. Ta rabu da mutumin da suke zama tare bayan ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Sai mutumin ma ya amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Sun yi aure kuma suka yi baftisma suka zama Shaidun Jehobah masu ƙwazo sosai. Rosa ce ’yar gari da ta soma hidimar majagaba a birnin Santa Ana.b
Rosa tana da wani ƙaramin shago. Takan rufe shagon kuma ta fita wa’azi don ta dogara ga Jehobah cewa zai biya bukatunta. Sa’ad da ta dawo kuma ta buɗe shagon sai mutane su cika shagon suna sayan abubuwa. Hakan ya sa ta amince cewa abin da aka a faɗa a Matta 6:33 gaskiya ne. Rosa ta kasance da aminci har mutuwarta.
Akwai lokacin da wani limami ya je ya gaya wa mutumin da ya ba mu shida da muka zo wa’azi a ƙasar haya, cewa idan ya ci gaba da barin mu a gidan, za a yi masa da matarsa yankan zumunci daga cocin. Maigidan wani babban attajiri ne kuma a lokacin ya riga ya gaji da halin limaman coci. Saboda haka, bai saurare shi ba. A maimakon haka, ya gaya wa firist ɗin cewa ko an kore shi daga cocin bai damu ba. Ya gaya mana kada mu damu, kuma mu ci gaba da zamanmu.
WANI BABBAN MUTUM YA ZAMA MASHAIDI
Wani mai wa’azi a ƙasar waje yana yin nazari da matar wani injiniya mai suna Baltasar Perla a San Salvador, babban birnin ƙasar. Wannan injiniya mutumin kirki ne amma ya daina ba da gaskiya ga Allah don munafuncin limaman addini. Sa’ad da lokaci ya yi da za a gina reshen ofishi, Baltasar ya ce zai zana kuma ya gina ofishin kyauta, ko da yake shi ba mashaidi ba a lokacin.
Sa’ad da Baltasar ya yi cuɗanya da Shaidun Jehobah a lokacin da suke gina reshen ofishi, sai ya tabbata cewa su ne suke bin addini na gaskiya. Ya yi baftisma a ranar 22 ga Yuli, 1955, jim kaɗan bayan haka, matarsa ma ta yi baftisma. Suna da ’ya’ya biyu kuma duka suna bauta wa Jehobah har wa yau. Ɗansu, mai suna Baltasar, Jr., ya yi shekara 49 yana hidima a Bethel da ke Brooklyn, inda yake tallafa wa aikin wa’azi da ke bunƙasa a faɗin duniya. Yanzu yana cikin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe na Amirka.c
Sa’ad da muka soma yin babban taro a birnin San Salvador, Ɗan’uwa Baltasar Perla ya samo mana wani babban gidan motsa jiki don taron. Da farko, muna amfani da wasu jerin kujeru kaɗan ne kawai; amma da taimakon Jehobah da shigewar shekaru, muka ci gaba da ƙaruwa kuma muka cika gidan har ma gidan ya yi mana kaɗan! Na haɗu da waɗanda na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su a waɗannan taron. Na yi farin ciki sosai sa’ad da ɗalibaina na dā suka nuna mini waɗanda suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su da suka yi baftisma!
Sa’ad da muka halarci wani babban taro sai wani ɗan’uwa ya zo ya same ni ya ce yana so ya roƙi gafara. Ban gane shi ba kuma hakan ya sa ina so in san ko mene ne. Ya ce, “Ina cikin yaran da suka jejjefe ku da duwatsu a birnin Santa Ana.” Yanzu yana bauta wa Jehobah tare da mu! Hakan ya sa ni farin ciki sosai. Wannan abin da ya faru ya tabbatar mini cewa hidima ta cikakken lokaci ita ce aiki mafi gamsarwa a rayuwa.
ZAƁI MAI GAMSARWA
Na yi kusan shekaru 29 a matsayin mai wa’azi a ƙasar waje a El Salvador, da farko, a birnin Santa Ana, bayan haka, na yi a birnin Sonsonate da Santa Tecla da kuma a San Salvador. Iyayena masu aminci sun tsufa kuma suna bukatar taimako, saboda haka, bayan na nazarci batun sosai cikin addu’a, a shekara ta 1975, sai na bar hidimar mai wa’azi a ƙasar waje don in je in taimaka musu.
Bayan mutuwar mahaifina a shekara ta 1979, sai na ci gaba da kula da mahaifiyata yayin da take ƙara tsufa. Ta ƙara yin shekara 8 bayan haka kuma ta mutu sa’ad da take da shekaru 94. A wannan mawuyacin lokacin, na zo na gaji kuma na kasala. Hakan ya jawo mini wani ciwo da ake kira shingles. Addu’a da kuma tabbaci cewa Jehobah yana kula da ni ya ƙarfafa ni kuma na iya na jure a wannan lokacin. Jehobah ya ce: “Har lokacin da kuka tsufa . . . , Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”—Isha. 46:4, Littafi Mai Tsarki.
Na ƙaura zuwa birnin Omak, a jihar Washington a shekara ta 1990. A can na soma taimakawa a yanki da ake yaren Sfanisanci kuma ɗalibai da dama da na yi nazari da su sun yi baftisma. A shekara ta 2007, ba na iya kula da gidana da ke Omak, saboda haka, na ƙaura zuwa ƙaramin gida a garin Chelan da ke Washington. Ikilisiyar Sfanisanci da ke wurin suna kula da ni kuma ina godiya saboda haka. Da yake ni ce kaɗai ’yar’uwa tsohuwa a nan, ’yan’uwa maza da mata suna ɗauka na a matsayin “kakarsu.”
Da yake na ƙi yin aure don ba na so in kasance da iyali, ba wani abin da ke ‘raba hankalina’ a hidima, kuma ina da ’yan’uwa da yawa da suke kamar ’ya’yana. (1 Kor. 7:34, 35) Na san cewa a wannan zamanin, ba zan iya samun dukan abin da nake so ba. Saboda haka, na saka abin da ya fi muhimmanci kan gaba a rayuwata, wato bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Na san cewa a sabuwar duniya, zan sami lokacin jin daɗin abubuwa da yawa. Ayar da na fi so ita ce Zabura 145:16, da ta bayyana mana cewa Jehobah zai ‘buɗe hannunsa, yana biya wa kowane mai-rai muradinsa.’
Yanzu ina da shekara 91, ina da ɗan ƙarfi saboda haka, ina hidimar majagaba har ila. Hidimar majagaba tana sa ni farin ciki kuma tana sa rayuwata ta kasance da ma’ana. A lokacin da na je ƙasar El Salvador, ba a daɗe da soma wa’azi a wurin ba. Yanzu akwai masu shela fiye da 39,000 a ƙasar duk da hamayyar da Shaiɗan yake jawowa. Hakan ya ƙarfafa bangaskiyata. Babu shakka, Jehobah yana goyon bayan mutanensa da ruhu mai tsarki!
a Ka duba littafin nan 1981 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 45-46.
b Littafin nan 1981 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 41-42.
c Littafin nan 1981 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 66-67 da 74-75.