Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/15 pp. 12-16
  • Ka Bauta wa Allah da Aminci Duk da ‘Wahala da Yawa’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bauta wa Allah da Aminci Duk da ‘Wahala da Yawa’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TSANANTAWA A LISTRA
  • FARMAKI NA KAI TSAYE
  • FARMAKIN DA BA A SAURIN GANEWA
  • KA YI SHIRI YANZU DON GWAJI
  • Kada Ka Yi Kasala A Aikin Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Jehobah Yana Karfafa Mu Sa’ad da Muke Cikin Matsala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • “Ku Yi Ta Gina Juna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Yadda Za Ka Yi Shiri don Kunci Mai Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/15 pp. 12-16

Ka Bauta wa Allah da Aminci Duk da “Wahala da Yawa”

“Sai ta wurin wahala da yawa za mu shiga mulkin Allah.”—A. M. 14:22.

MECE CE AMSARKA?

  • Wane ne yake haddasa wahalar da muke fuskanta?

  • Ta yaya za mu yi shiri don fuskantar tsanantawa da kuma sanyin gwiwa?

  • Wace lada ce za a ba waɗanda suka jimre wahala?

1. Me ya sa bayin Jehobah ba sa mamaki cewa za su fuskanci wahala?

SHIN kana mamaki cewa za ka fuskanci “wahala da yawa” kafin ka sami rai na har abada? Wataƙila ba ka fargaba. Ko da ba ka daɗe da soma bauta wa Jehobah ba ko ka daɗe da yin haka, babu shakka, ka san cewa dole a sha wahala a wannan duniyar Shaiɗan.—R. Yoh. 12:12.

2. (a) Ban da wahalar da ke shafan dukan ’yan Adam, wace irin wahala ce Kiristoci suke fuskanta? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Wane ne ke haddasa tsanantawar da muke fuskanta, kuma yaya muka san da haka?

2 Dukan ’yan Adam ajizai suna fuskantar matsaloli a rayuwa. Amma Kiristoci suna fuskantar ƙarin wahala. (1 Kor. 10:13) Wace wahala ke nan? Suna fuskantar tsanantawa sosai domin suna bin dokokin Allah. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Bawa bai fi ubangijinsa girma ba. Idan suka tsananta mini, za su tsananta muku kuma.” (Yoh. 15:20) Wane ne yake haddasa wannan tsanantawar? Babu shakka, Shaiɗan ne kuma Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi kamar “zaki mai-ruri,” wanda ke “neman wanda za ya cinye.” (1 Bit. 5:8) Shaiɗan zai yi amfani da kowane irin dabara domin ya hana mu bauta wa Jehobah. Bari mu tattauna abin da ya faru da manzo Bulus.

TSANANTAWA A LISTRA

3-5. (a) Wace tsanantawa ce Bulus ya fuskanta a Listra? (b) A wace hanya ce furucin Bulus game da tsanantawa yake da ban ƙarfafa?

3 An tsananta wa Bulus sau da yawa saboda imaninsa. (2 Kor. 11:23-27) Akwai lokacin da aka taɓa tsananta masa a Listra. Bayan da Bulus da abokin aikinsa Barnaba suka warkar da wani mutum da aka haife shi gurgu, jama’a sun yaba musu kuma sun kira su alloli. Bayan haka, sai suka soma roƙon mutanen cewa kada su bauta musu! Ba da daɗewa ba, sai limaman Yahudawa suka zo kuma suka zuga jama’ar. Nan da nan, jama’ar suka ji zugin kuma suka jefe su da duwatsu har ma aka zata Bulus ya mutu.—A. M. 14:8-19.

4 Bayan Bulus da Barnaba sun ziyarci birnin Darba, sun “koma Listra, da Ikoniya da Antakiya, suna ƙarfafa rayukan masu-bi, suna yi masu gargaɗi su lizima a cikin imani.” Kuma suka daɗa cewa: “Sai ta wurin wahala da yawa za mu shiga mulkin Allah.” (A. M. 14:21, 22) Da farko, wataƙila ba za mu fahimci wannan batun ba. Ballantana ma, sanin cewa za mu fuskanci “wahala da yawa” ba abin ƙarfafa ba ne. Ta yaya Bulus da Barnaba suka ‘ƙarfafa’ masu-bi da yake sun ce za su fuskanci wahala da yawa?

5 Idan muka bincika furucin Bulus sosai, za mu sami amsar wannan tambayar. Bai ce: “Wajibi ne mu jimre wahala da yawa” ba. Amma ya ce: ‘Sai ta wurin wahala da yawa za mu shiga mulkin Allah.’ Bulus ya ƙarfafa masu-bi ta wajen nanata ladar da za su samu idan suka kasance da aminci. Ladar ba bula ba ce. Hakika, Yesu ya ce: ‘Wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.’—Mat. 10:22.

6. Wace lada ce mutanen da suka jimre za su samu?

6 Za mu sami lada idan muka jimre. Kiristoci shafaffu za su yi sarauta tare da Yesu a sama kuma ba za su sake mutuwa ba. “Waɗansu tumaki” kuma za su yi rayuwa har abada a cikin duniya “inda adalci” zai kasance. (Yoh. 10:16; 2 Bit. 3:13) Amma Bulus ya ce kafin mu sami wannan ladar, za mu sha wahala da yawa. Ka yi la’akari da wahala guda biyu da za mu iya fuskanta.

FARMAKI NA KAI TSAYE

7. Wane irin farmaki ne na kai tsaye?

7 Yesu ya annabta cewa: Mutane “za su ba da ku ga Sanhedrin [majalisa]; a cikin majami’u kuwa za a duke ku; za ku tsaya a gaban mahukumta da sarakuna.” (Mar. 13:9) Wannan furucin ya nuna cewa wasu Kiristoci za su fuskanci tsanantawa kuma wataƙila limamai ko shugabanni ne za su yi hakan. (A. M. 5:27, 28) Bari mu sake yin la’akari da misalin Bulus. Shin ya ji tsoro domin za a tsananta masa? A’a.—Karanta Ayyukan Manzanni 20:22, 23.

8, 9. Ta yaya Bulus ya nuna cewa ya ƙuduri niyyar ya jimre, kuma ta yaya wasu a yau suka kasance da irin wannan aniyar?

8 Bulus ya tsayayya wa farmaki na kai tsaye da Shaiɗan ya kai masa, kuma ya ce: “Ban mai da raina wani abu ba, kamar abin tamani a gareni, bisa ga in cika tafiyata, da hidima kuma wadda na karɓa daga wurin Ubangiji Yesu, in shaida bishara ta alherin Allah ke nan.” (A. M. 20:24) Hakika, tsanantawa bai sa Bulus tsoro ba. Akasin haka, ya ƙudura ya jimre ko da me zai faru. Abin da ya fi damunsa shi ne ya “shaida bishara” duk da wahala.

9 Abin da ’yan’uwanmu da yawa a yau suka ƙuduri niyyar yi ke nan. Alal misali, Shaidun Jehobah a wata ƙasa sun jimre a kurkuku kusan shekara ashirin domin sun ƙi shiga soja. Ba a taɓa yin shari’a da su a kotu ba, domin ƙasar ba ta yi wani tanadi don mutanen da suka ƙi saka hannu a yaƙi saboda imaninsu ba. Sa’ad da suke cikin kurkuku, an hana mutane ziyartarsu har da iyalansu. An yi wa wasu duka kuma an azabtar da su.

10. Me ya sa bai kamata mu ji tsoro don wahalar da za ta iya faruwa farat ɗaya ba?

10 Wasu ’yan’uwa kuma sun jimre da wahalar da ta taso farat ɗaya. Idan hakan ya faru da kai, kada ka ji tsoro. Ka yi la’akari da Yusufu. An sayar da shi don ya zama bawa, amma Jehobah ya “tsamar da shi daga cikin ƙuncinsa duka.” (A. M. 7:9, 10) Jehobah zai iya ’yantar da kai ma daga ƙunci. Ka tuna cewa Jehobah “ya san yadda zai ceci masu-ibada daga cikin jaraba.” (2 Bit. 2:9) Shin za ka ci gaba da dogara ga Jehobah domin ka san cewa zai iya ceton ka daga wannan muguwar duniyar Shaiɗan kuma ya sa ka ji daɗin rayuwa har abada a ƙarƙashin Mulkinsa? Hakan dalili ne mai kyau na kasancewa da gaba gaɗi sa’ad da kake fuskantar tsanantawa.—1 Bit. 5:8, 9.

FARMAKIN DA BA A SAURIN GANEWA

11. Ta yaya farmaki na kai tsaye ya bambanta da farmakin da ba a saurin ganewa?

11 Wata irin wahalar kuma da muke fuskanta ita ce farmaki da ba a saurin ganewa. Ta yaya wannan ya bambanta da farmaki na kai tsaye, wato tsanantawa? Farmaki na kai tsaye yana kamar guguwa da ke shiga cikin gari kuma ya halaka gidanka farat ɗaya. Amma, farmakin da ba a saurin ganewa yana kamar gara da ke cin katakon gidanka a hankali. Kafin ka san abin da yake faruwa, gidan ya kusan rushewa.

12. (a) Wane farmakin da ba a saurin ganewa ne Shaiɗan yake amfani da shi, kuma me ya sa yake yin nasara sosai? (b) Ta yaya Bulus ya yi fama da sanyin gwiwa?

12 Shaiɗan zai so ya gurɓata dangantakarka da Jehobah. Zai iya yin hakan ta wajen yin amfani da farmaki na kai tsaye, wato tsanantawa, ko kuma farmakin da ba a saurin ganewa da zai gurɓata imaninka a hankali. Wani farmakin da ba a saurin ganewa da Shaiɗan yake amfani da shi sosai shi ne sanyin gwiwa. Manzo Bulus ma ya ce ya yi sanyin gwiwa a wasu lokuta. (Karanta Romawa 7:21-24.) Me ya sa Bulus wanda dangantakarsa da Jehobah take da danƙo sosai kuma wataƙila shi memban hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko ya ce shi “mutum, abin tausayi” ne? Bulus ya ce ya ji hakan domin shi ajizi ne. Yana son yin abin da ya dace, amma muradin yin abu marar kyau ne ke yawan shiga zuciyarsa. Idan kana fama da irin wannan yanayin a wasu lokuta, sanin cewa manzo Bulus ma ya yi fama da irin wannan matsalar abin ƙarfafa ne, ko ba haka ba?

13, 14. (a) Me yake sa wasu bayin Jehobah sanyin gwiwa? (b) Wane ne yake so mu daina bauta wa Jehobah, kuma me ya sa?

13 A wasu lokuta, ’yan’uwa da yawa suna yin sanyin gwiwa da alhini ko kuma su ji kamar ba su da mutunci. Alal misali, wata majagaba mai ƙwazo da za mu kira Deborah a wannan talifin ta ce: “Ina yawan yin tunani a kan wani kuskuren da na taɓa yi, kuma hakan yana sa ni sanyin gwiwa. Sa’ad da na yi tunani a kan dukan kurakuran da na yi, sai na ga kamar babu mutumin da zai taɓa ƙaunata, har ma da Jehobah.”

14 Me zai iya sa wasu bayin Jehobah masu ƙwazo kamar Deborah su yi sanyin gwiwa? Akwai dalilai da dama da za su iya jawo hakan. Wasu suna yawan so yin tunani marar kyau game da kansu da kuma yanayinsu. (Mis. 15:15) Wasu kuma suna irin tunanin nan don rashin lafiyar da ke shafan motsin ransu. Ko da mene ne ya jawo matsalar, wajibi ne mu tuna ainihin wanda ke so ya yi amfani da wannan damar. Shin wane ne yake so mu yi sanyin gwiwa har mu karaya? Babu shakka Shaiɗan ne. An yanke masa hukuncin mutuwa kuma yana so ka ji cewa kai ma ba ka da mafita. (R. Yoh. 20:10) Babu shakka, Shaiɗan ne. Gaskiyar ita ce, ko da Shaiɗan ya yi amfani da farmaki na kai tsaye ko kuma farmakin da ba a saurin ganewa, muradinsa shi ne ya sa mu sanyin gwiwa kuma mu daina bauta wa Jehobah. Ka tuna cewa bayin Allah suna baƙin dāga, wato suna ƙoƙari su kāre dangantakarsu da Jehobah!

15. Ta yaya za mu iya nuna cewa mun ƙuduri niyyar ci gaba da bauta wa Jehobah?

15 Ka ƙuduri niyya cewa ba za ka daina bauta wa Jehobah ba. Ka tuna cewa za a ba ka lada. Bulus ya rubuta wasiƙa ga Kiristocin da ke Korinti cewa: “Ba mu yi yaushi ba; amma ko da mutumin namu na waje yana lalacewa, mutumin namu na ciki yana sabuntuwa yau da gobe. Gama ƙuncinmu mai-sauƙi, wanda ke na lokaci kaɗan, yana aika dominmu nauyin daraja madawwami gaba gaba ƙwarai.”—2 Kor. 4:16, 17.

KA YI SHIRI YANZU DON GWAJI

16. Me ya sa ya kamata mu yi shiri yanzu don wahala da za mu fuskanta?

16 Kamar yadda muka tattauna, Shaiɗan yana da ‘dabaru’ da yawa da yake amfani da su. (Afis. 6:11) Dukanmu muna bukatar mu bi shawarar da Bitrus ya bayar cewa: “Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa kan bangaskiyarku.” (1 Bit. 5:9, Littafi Mai Tsarki) Idan muna so mu yi hakan, muna bukatar mu yi shiri yanzu don yin abin da ya dace. Alal misali: Akan horar da sojoji sosai don su yi shiri kafin lokacin yaƙi. Hakazalika, ya kamata mu kasance a shirye tun yanzu. Ba mu san irin famar da za mu yi a nan gaba ba. Saboda haka, zai dace mu horar da kanmu sosai yanzu da ba ma fuskantar farmaki. Bulus ya ce wa Korintiyawa: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani; ku yi wa kanku ƙwanƙwanto.”—2 Kor. 13:5.

17-19. (a) A waɗanne hanyoyi ne za mu iya gwada kanmu? (b) Ta yaya matasa za su iya yin shiri don su bayyana imaninsu a makaranta?

17 Hanya ɗaya da za mu iya bin shawarar Bulus ita ce ta wajen bincika kanmu sosai. Ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Shin ina nacewa wajen yin addu’a? Sa’ad da nake fuskantar matsi daga tsarana, ina yin biyayya ga Allah maimakon ’yan Adam? Ina halartar taron ikilisiya a kai a kai? Ina yin wa’azi da gaba gaɗi kuwa? Ina ƙoƙarin gafarta wa ’yan’uwana kamar yadda su ma suke gafarta mini? Shin ina biyayya ga waɗanda suke ja-gora a cikin ikilisiya da kuma ƙungiyar Jehobah ko da yin hakan bai da sauƙi ne?’

18 Ka lura cewa biyu cikin waɗannan tambayoyin game da yin wa’azi da gaba gaɗi ne da kuma yin tsayin daka sa’ad da muke fuskantar matsi daga tsara. Matasanmu da yawa sun yi hakan sa’ad da suke makaranta. Sun koyi yin magana game da imaninsu da gaba gaɗi. An wallafa shawarwari masu kyau game da wannan batun a cikin mujallunmu. Alal misali, Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 2013, shafi na 6, ya bayyana yadda za mu daɗa yin gaba gaɗi sa’ad da muke tattauna da ’yan ajinmu game da imaninmu ta wajen yi musu tambayoyi da za su sa su yi tunani. Iyaye, ku tabbata cewa kun yi ganawa da yaranku domin su kasance a shirye su ba da amsa sa’ad da suka fuskanci matsi daga tsaransu a makaranta.

19 A gaskiya, bayyana imaninmu ko kuma bin dokokin Jehobah bai da sauƙi a koyaushe. A wasu lokatai, muna halartar taro da kyar bayan mun dawo daga aiki kuma mun gaji. Tashi daga barci da sassafe don zuwa wa’azi bai da sauƙi. Amma, ya kamata mu tuna cewa idan mun saba yin waɗannan abubuwan yanzu, za mu sami gaba gaɗin jimrewa sa’ad da muka fuskanci gwaji masu tsanani sosai a nan gaba.

20, 21. (a) Ta yaya yin bimbini a kan hadayar fansar Yesu zai taimaka mana mu daina sanyin gwiwa? (b) Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi duk da wahalar da za mu fuskanta?

20 Farmakin da ba a saurin ganewa kuma fa? Alal misali, me zai taimaka mana mu daina sanyin gwiwa? Yin bimbini a kan hadayar fansar Yesu zai taimaka mana sosai. Abin da manzo Bulus ya yi ke nan. A wasu lokuta, baƙin ciki yakan sa ya ɗauka cewa shi abin tausayi ne. Amma, ya san cewa Yesu ya mutu don masu zunubi ne, ba domin kamiltattu ba, kuma Bulus ma mai zunubi ne. Shi ya sa ya ce: ‘Ina rayuwa cikin bangaskiya, bangaskiya wanda take cikin ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, ya ba da kansa kuma domina.’ (Gal. 2:20) Hakika, Bulus ya amince da fansar Yesu kuma ya san cewa Yesu ya mutu domin shi.

21 Hakazalika, sanin cewa Jehobah ya aiko Yesu ya mutu dominka, zai taimaka maka sosai. Hakan ba ya nufin cewa za mu daina yin sanyin gwiwa farat ɗaya. Wasu cikinmu za su yi fama da wannan matsalar har matuƙar wannan mugun zamani. Amma ya kamata mu tuna cewa: Mai haƙuri zai iya dafa dutse kuma ya sha romonsa. Mun yi kusa da ranar da Mulkin Allah zai kawo salama kuma zai mayar da dukan ’yan Adam kamiltattu. Ka ƙuduri niyyar cewa za ka shiga Mulkin, duk da wahala da yawa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba