TARIHI
Albarkar Yi wa Allah Hidima
Na soma fama da wariyar launin fata da rashin gaba gaɗi da kuma kunya tun ina ƙarami. Hakan ya sa na soma zuwa Cocin Katolika na yankinmu don su taimaka mini in fahimci Littafi Mai Tsarki. Na sa rai cewa hakan zai ƙarfafa ni. Amma da yake ba su taimaka mini ba, sai na mai da hankali ga yin wasanni.
Ba da daɗewa ba na shagala da wasannin motsa jiki da kuma ɗaukan nauyi. A kwana a tashi, na buɗe gidan wasannin motsa jiki a garin San Leandro da ke Kalifoniya a Amirka. Ƙari ga haka, na yi aiki da masu ɗaukan nauyi dabam-dabam, har da wani da ya taɓa cin lambar yabo ta Mr. America. Amma, samun siffa mai kyau bai sa ni farin ciki ba.
BUKATATA TA BIYA
Wani abokina a gidan motsa jiki ya fahimci cewa ina so in koyi Littafi Mai Tsarki kuma ya ce zai so in sadu da wani abokinsa. Washegari, wani Mashaidin Jehobah ya zo gidana kuma muka yi awa huɗu muna tattaunawa, yana amsa tambayoyina daga Littafi Mai Tsarki. Na gaya masa ya sake dawowa da yamma kuma da ya dawo, sai muka tattauna Littafi Mai Tsarki tare har tsakar dare. Na ji daɗin abubuwan da na koya sosai kuma na tambaye shi ko zan iya binsa washegari don in ga yadda yake yin wa’azi. Yadda yake nuna wa mutane amsoshin tambayoyinsu a cikin Littafi Mai Tsarki ya burge ni ƙwarai. Hakan ya sa na tsai da shawara cewa abin da zan yi a rayuwata ke nan!
Sai na sayar da gidan motsa jikin kuma na ci gaba da yin wa’azi da wannan majagaban.a Na yi baftisma a watan Mayu na shekara ta 1948, a wani babban taron da aka yi a filin wasan Cow Palace da ke birnin San Francisco a Kalifoniya. Bayan haka, ni ma na zama majagaba a wannan shekarar.
Kafin wannan lokacin, na gaya ma wasu Shaidun Jehobah su je su yi wa mahaifiyata wa’azi. Ta saurare su kuma ba da daɗewa ba, ta zama Mashaidiyar Jehobah. Duk da hamayyar da iyalinta suka yi da ita, ta ci gaba da bauta wa Allah shekaru da yawa kafin mutuwarta. Mu biyu ne kawai muka zama Shaidun Jehobah a iyalinmu.
YADDA NA HAƊU DA MATAR DA NA AURA
A shekara ta 1950, na ƙaura zuwa birnin Grand Junction, a jihar Colorado, kuma a nan ne na haɗu da Billie. An haife ta ne a shekara ta 1928 kuma ta girma a lokacin da ake matsanancin talauci. Mahaifiyarta Minnie takan karanta mata Littafi Mai Tsarki kowane dare da fitila. A sakamakon haka, Billie ta iya karatu tun tana ’yar shekara huɗu, kuma ta haddace labaran Littafi Mai Tsarki da yawa. Kafin shekara ta 1949, Shaidun Jehobah sun koya mata cewa Littafi Mai Tsarki bai ce Allah zai ƙona mutane a wutar jahannama ba. (Mai-Wa’azi 9:5, 10) Minnie da maigidanta sun zama Shaidun Jehobah.
A shekara ta 1949, Billie ta sauke karatu daga wani kwaleji a birnin Boston kuma ta mai da hankali ga yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Maimakon ta zama malama, ta keɓe kanta ga Allah kuma ta yi baftisma a shekara ta 1950 a wani taron ƙasashe da Shaidun Jehobah suka yi a filin wasan Yankee, a Amirka. Jim kaɗan bayan wannan taron ne na haɗu da ita sai muka yi aure kuma muka soma yin hidimar majagaba.
Mun soma hidimarmu a birnin Eugene a jihar Oregon kuma mun yi abokai da yawa. A 1953, mun koma birnin Grants Pass a Oregon don mu taimaka wa ƙaramar ikilisiyar da ke wurin. Daga baya a wannan shekarar, an gayyace mu zuwa aji na 23 na makarantar Gilead, wato makarantar Shaidun Jehobah don horar da masu wa’azi a ƙasashen waje. Wannan makarantar tana kusa da birnin South Lansing, wajen mil 250 daga birnin New York a Amirka.
YIN HIDIMA A BRAZIL
A watan Disamba na 1954, watanni biyar da sauke karatu a makarantar Gilead, ni da Billie muka shiga jirgin sama zuwa ƙasar Brazil. Awa ɗaya bayan da muka tashi, jirgin ya sami matsala kuma muka sauka a tsibirin Bermuda. Daga wurin muka kama tafiya amma muka sake sauka a ƙasar Cuba saboda wata matsala. Bayan tafiya mai gajiyarwa na awa 36, muka iso ofishin Shaidun Jehobah da ke birnin Rio de Janeiro, a Brazil.
Majami’ar Mulki ta farko a Bauru, wadda gidan haya ne, ɗauke da allon da na zana a 1955
Bayan mun zauna a wurin na ɗan lokaci, sai mu da wasu ’yan’uwa mata biyu masu wa’azi a ƙasashen waje muka je birnin Bauru a jihar São Paulo don mu soma wa’azi a wurin. A lokacin birnin yana da mazauna sama da 50,000 kuma mu ne Shaidun Jehobah na farko a wurin.
Mun soma wa’azi gida-gida, amma firist ɗin Cocin Katolika na yankin ya soma hamayya da mu nan da nan. Ya bi mu gida-gida yana yi wa mutane gargaɗi cewa kada su saurare mu. Amma bayan ’yan makonni kawai, wani iyalin da muka yi nazari da su sun amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma suka yi baftisma. Ba da daɗewa ba, mun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu.
Wannan iyalin da suka yi baftisma suna da wani dangi da shugaban wani babban gidan fati ne. Na shirya da shi don mu yi wani babban taro a gidan fatin. Sa’ad da firist ɗin ya sami labarin taron, ya yi ƙoƙari ya sa a hana mu wurin. Amma, shugaban gidan fatin ya ce wa sauran ma’aikatan: “Idan kun hana su gidan fatin, to na bar aiki ke nan!” A sakamakon haka, an yarda mana mu yi taron.
A shekara ta 1956, an gayyace mu wani taron gunduma a birnin Santos, a São Paulo. Shaidun Jehobah kusan 40 daga ikilisiyarmu sun je taron a jirgin ƙasa. Da muka dawo Bauru, an rubuto mini wasiƙa in soma hidimar mai kula mai ziyara, wato in riƙa ziyartar ikilisiyoyin Shaidun Jehobah. Na yi kusan shekaru 25 ina wannan hidimar a ƙasar Brazil kuma na kusan zagaya ƙasar.
A cikin shekara guda kawai, mun sami masu wa’azi da himma a Bauru
ABIN DA HIDIMARMU TA ƘUNSA
Yin tafiya bai kasance da sauƙi a lokacin ba. Mun kusan zagaya ƙasar, muna tafiya a bas da jirgin ƙasa da karusa da keke da kuma ƙafa. Ɗaya daga cikin biranen da muka fara ziyarta shi ne birnin Jaú, a São Paulo. A wurin ne wani firist ya ja da mu.
Ya ce: “Kada ku yi wa ‘tumakina’ wa’azi.”
Sai muka ce masa: ‘Su na Allah ne, ba naka ba.’
Mun shirya mu nuna wa mutane wani fim game da wa’azinmu a faɗin duniya, mai suna The New World Society in Action, amma firist ɗin ya shirya da wasu ’yan cocinsa su kawo mana hari. Da jin hakan, muka sanar da ’yan sanda. Sa’ad da firist ɗin da ’yan cocinsa suka iso wurin taron, sun tarar da ’yan sanda riƙe da bindigogi a bakin ƙofa. Jama’ar sun ji daɗin fim ɗin sosai.
A kusan dukan wuraren da muka yi hidima a lokacin, mun tarar da irin wannan hamayyar. Alal misali, a birnin Brusque, kusa da birnin Blumenau, a jihar Santa Catarina, mun haɗu da wasu majagaba biyu mata da suke fuskantar hamayya sosai. Duk da haka, sun ci gaba da yin hidima kuma Allah ya albarkace su. A yanzu haka bayan sama da shekaru 50, akwai ikilisiyoyi sama da 60 a wannan yankin da kuma wata kyakkyawar Majami’ar Babban Taro a birnin Itajaí!
Abin da ya fi burge ni a hidimarmu shi ne lokatan da muke aiki tare da ’yan’uwa Shaidu wajen shirya manyan taro. Daga shekara ta 1975 zuwa 1977, na yi hidimar mai kula da babban taro a filin wasan da ke yankin Morumbi. An aika wasiƙu zuwa ikilisiyoyi wajen ɗari da ke kusa don su turo ’yan’uwa goma-goma su zo su taimaka da sharan filin wasan da daren da ya gabaci taron.
Yayin da ’yan ƙwallo suke barin filin wasan da daren, an ji wasu daga cikinsu suna cewa, “Ku ga waɗannan matan da tsintsiyoyinsu, suna ganin za su iya share wannan filin wasan.” Amma kafin tsakar dare, sun share filin gaba ɗaya! Manajan filin wasan ya ce, “Wannan aikin da ma’aikatana za su yi cikin mako guda, shi ne ku Shaidun Jehobah kuka yi a cikin ’yan awoyi kawai?”
MUN KOMA AMIRKA
A shekara ta 1980, mahaifina ya rasu, kuma jim kaɗan bayan haka muka koma Amirka don mu kula da mahaifiyata a birnin Fremont da ke jihar Kalifoniya. Mun soma aikin sharan gidaje da dare kuma mun ci gaba da hidimar majagaba muna taimaka wa mutanen yaren Portuguese da ke wannan yankin. Daga baya muka ƙaura zuwa San Joaquin Valley, kuma muka soma neman mutanen da suke yaren Portuguese daga yankin Sacramento zuwa Bakersfield. A yanzu haka, akwai ikilisiyoyin yaren Portuguese kusan goma a Kalifoniya.
Bayan rasuwar mahaifiyata a shekara ta 1995, mun ƙaura zuwa jihar Florida don mu kula da mahaifin matata har lokacin da ya rasu. Mahaifiyarta ta riga ta rasu tun shekara ta 1975. A shekara ta 2000, mun ƙaura zuwa wani hamada da ke kudu maso yammacin jihar Colorado kuma muka yi hidima ta cikakken lokaci a wurin muna yin wa’azi ga asalin ’yan Amirka da ke yankin Navajo da Ute. Abin baƙin ciki fa, matata Billie ta rasu a watan Fabrairu na 2014.
Har yanzu ina farin ciki matuƙa cewa sama da shekaru 65 da suka gabata, na haɗu da Mashaidin Jehobah da ya amsa tambayoyina daga Littafi Mai Tsarki! Ina murna cewa na yi bincike a kan abin da ya koya mini don in tabbatar cewa hakan ya yi daidai da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Hakan ya sa na yi wa Allah hidima kuma na sami albarka mai yawa.
[Hasiya]
a Majagaba shi ne Mashaidin Jehobah da ke yin wa’azi na ayanannen sa’o’i.