Kalmar Allah Rayayyiya Ce Ka Yi Amfani da Ita!
“Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.”—IBRAN. 4:12.
1, 2. Wane aiki ne Allah ya ba Musa, kuma wane tabbaci ne ya ba shi?
YAYA za ka ji idan aka ce ka yi magana da wani babban masarauci a nan duniya a madadin bayin Jehobah? Wataƙila hankalinka zai tashi kuma za ka ji tsoro da rashin cancanta. Yaya za ka shirya maganar da za ka yi? Mene ne za ka yi a matsayin wakilin Allah Maɗaukakin Sarki don furucinka ya yi tasiri?
2 Yanayin da Musa ya sami kansa a ciki ke nan. Jehobah ya gaya wa Musa, wanda shi “mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya,” cewa zai tura shi wurin Fir’auna don ya ceci bayinsa daga zalunci da kuma bauta a ƙasar Masar. (Lit. Lis. 12:3) Amma Fir’auna ya nuna cewa shi mai rashin kunya ne da kuma fahariya. (Fit. 5:1, 2) Duk da haka, Jehobah yana so Musa ya umurci Fir’auna ya saki miliyoyin bayinsa don su bar ƙasar. Wannan dalilin ne ya sa Musa ya tambayi Jehobah: “Wāne ni har da zan tafi wurin Fir’auna, in fito da ’ya’yan Isra’ila daga cikin Masar kuma?” Babu shakka, Musa ya ga kamar bai cancanta kuma ba zai iya yin wannan aikin ba. Amma Allah ya tabbatar masa cewa zai goyi bayansa. Jehobah ya gaya masa: “Hakika zan kasance tare da kai.”—Fit. 3:9-12.
3, 4. (a) Me ya sa Musa ya ji tsoro? (b) Ta yaya yanayinka zai iya zama ɗaya da na Musa?
3 Me ya sa Musa ya ji tsoro? Wataƙila ya ji tsoro cewa Fir’auna ba zai marabce shi ko kuma ya saurari wakilin Jehobah ba. Musa ya kuma ji tsoro cewa mutanensa ba za su gaskata cewa Jehobah ne ya naɗa shi ya yi musu ja-gora don su fita daga ƙasar Masar ba. Saboda haka, Musa ya gaya wa Jehobah: “Amma, ga shi, ba za su gaskanta ni ba, ba kuwa za su saurara ga maganata ba: gama za su ce, Ubangiji ba ya bayyana gare ka ba.”—Fit. 3:15-18; 4:1.
4 Dukanmu za mu iya koyan darasi daga amsar da Jehobah ya ba Musa da kuma abubuwan da suka faru bayan hakan. Wataƙila ba za ka taɓa zuwa gaban wani babban ma’aikacin gwamnati ba. Amma, shin ya taɓa maka wuya ka yi wa mutanen da kake gani kullum wa’azi game da Allah da kuma Mulkinsa? Idan hakan ne, ka yi la’akari da darussan da za mu iya koya daga Musa.
‘MENE NE WANNAN A HANNUNKA?’
5. Mene ne Jehobah ya ba Musa, kuma ta yaya wannan ya sa ya daina fargaba? (Ka duba hoton da ke shafi na 11.)
5 Sa’ad da Musa ya bayyana cewa yana tsoro don ba za a ɗauki maganarsa da muhimmanci ba, Allah ya shirya shi a hanyar da zai yi nasara. Littafin Fitowa ya ce: ‘Ubangiji ya ce wa [Musa], Mene ne wannan a hannunka? Ya ce, Sanda ce. Ya ce, Jefa ta ƙasa. Ya jefa ta ƙasa, ta kuwa zama maciji; Musa kuwa ya guje masa. Amma Ubangiji ya ce wa Musa, Miƙa hannunka, ka kama shi a wutsiya: (ya fa miƙa hannunsa, ya kama shi, ya komo sanda cikin hannunsa:) Domin su gaskata Ubangiji, . . . ya bayyana gare ka.’ (Fit. 4:2-5) Hakika, Allah ya ba Musa wata alama a hannunsa da za ta sa mutane su gaskata cewa saƙonsa daga wurin Jehobah ne. Sanda da yawancin mutane za su gani ba ta da muhimmanci ne Allah ya sa ta zama maciji. Wannan mu’ujizar ce ta sa mutane suka gaskata cewa Jehobah ne ya naɗa Musa. Jehobah ya gaya wa Musa: “Cikin hannunka kuma za ka ɗauki wannan sanda, wadda za ka yi alamu da ita.” (Fit. 4:17) Musa ya tafi wurin mutanensa da kuma Fir’auna babu fargaba, da yake yana riƙe da wannan shaidar da ta nuna cewa Jehobah ne ya aiko shi.—Fit. 4:29-31; 7:8-13.
6. (a) Me ya kamata ya kasance a hannunmu sa’ad da muke yin wa’azi, kuma me ya sa? (b) Ka bayyana yadda “maganar Allah mai-rai ce” da kuma yadda take ‘aikatawa.’
6 Za a iya maka wannan tambayar sa’ad da kake wa’azin bishara: “Mene ne wannan a hannunka?” A yawancin lokaci, muna riƙe da Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke wa’azi. Ko da yake wasu suna gani cewa Littafi Mai Tsarki littafi ne kawai, amma Jehobah yana mana magana ta wurin Kalmarsa da ya hure. (2 Bit. 1:21) Yana ɗauke da alkawarin da ya yi game da abubuwan da za su faru sa’ad da Mulkinsa ya soma sarauta. Shi ya sa manzo Bulus ya ce: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” (Karanta Ibraniyawa 4:12.) Dukan alkawuran Jehobah suna kan cika, kuma za su cika tabbas. (Isha. 46:10; 55:11) Da zarar mutum ya fahimci hakan game da Kalmar Jehobah, abin da ya karanta a ciki zai iya yin tasiri sosai a rayuwarsa.
7. Ta yaya za mu iya ‘fassara Maganar gaskiya daidai’?
7 Hakika, Jehobah ya ba mu rubutacciyar Kalmarsa don mu yi amfani da ita wajen tabbatar wa mutane cewa saƙon da muke bayarwa daga wurinsa ne. Babu shakka, bayan da Bulus ya rubuta wasiƙa ga Ibraniyawa, ya ƙarfafa Timotawus ya yi iya ƙoƙarinsa wajen ‘fassara Maganar gaskiya daidai.’ (2 Tim. 2:15, Littafi Mai Tsarki) Ta yaya za mu iya bin shawarar Bulus? Ta wajen karanta nassosi da suka dace da za su iya ratsa zuciyar waɗanda muke musu wa’azi. An wallafa warƙoƙin da aka fitar da su a shekara ta 2013 don su taimaka mana mu yi hakan.
KA KARANTA NASSIN DA YA DACE DA KA ZAƁA!
8. Mene ne wani mai kula da hidima ya faɗa game da warƙoƙinmu?
8 Dukan sababbin warƙoƙin suna da manufa ɗaya. Idan mun iya yin amfani da guda, za mu iya yin amfani da dukansu. Shin yana da sauƙi a yi amfani da waɗannan warƙoƙin? Wani mai kula da hidima a tsibirin Hawaii a ƙasar Amirka ya ce: “Ban taɓa sanin cewa waɗannan warƙoƙin suna da amfani sosai a wajen yin wa’azi gida-gida da kuma a kan titi ba.” Ya fahimta cewa yadda aka tsara warƙoƙin yana sa mutane su bayyana ra’ayinsu kuma su yarda a tattauna da su. Ƙari ga haka, ya ji cewa da yake kowace warƙa tana ɗauke da tambaya da kuma amsoshi dabam-dabam a farkon shafin, mutane ba sa jin tsoron ba da amsa.
9, 10. (a) Ta yaya warƙoƙinmu suke sa mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki? (b) Waɗanne cikin warƙoƙinmu ne ka fi jin daɗin yin amfani da su, kuma me ya sa?
9 Kowace warƙa tana ɗauke da nassin da ya dace da za mu iya karanta wa maigida. Bari mu yi la’akari da warƙar nan, Wahala Za Ta Ƙare Kuwa? Ko da mutumin ya amsa “e” ko “a’a,” ko kuma “wataƙila” don ya ba da amsar tambayar, ka buɗe shafi na ciki ba tare da wani ƙarin bayani ba kuma ka ce, “Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.” Bayan haka, sai ka karanta littafin Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
10 Hakazalika, sa’ad da kake yin amfani da warƙar nan Mene ne Ra’ayinka Game da Littafi Mai Tsarki? ko da wace amsa ce mutumin ya zaɓa cikin amsoshi uku da ke farkon warƙar ba damuwa ba ce. Ka buɗe shafi na ciki kuma ka ce, “Littafi Mai Tsarki ya ce ‘Kowane nassi hurarre ne daga wurin Allah.’” Za ka iya daɗa cewa, “Hakika, wannan nassin yana ɗauke da ƙarin bayani.” Sai ka buɗe Littafi Mai Tsarki kuma ka karanta 2 Timotawus 3:16, 17.
11, 12. (a) Ta yaya warƙoƙi suke sa ka ji daɗin yin wa’azi? (b) Ta yaya warƙoƙi za su iya taimaka maka ka shirya don ka koma ziyara?
11 Yawan abin da za ka karanta da kuma tattauna a warƙar ya dangana ne ga yadda mutumin ya karɓi saƙon. Ko da mutane sun so saƙonmu ko a’a, mun yi nasara domin mun ba su warƙa kuma mun karanta musu wani nassi. Ko da nassi ɗaya ko biyu ka karanta wa mutumin, za ka iya sake dawowa don ku ci gaba da tattaunawa.
12 Bayan kowace warƙar tana ɗauke da wannan tambayar, “Ka Yi Tunani a Kan Wannan Tambayar” kuma akwai nassosin da za a iya tattaunawa da maigida sa’ad da kuka dawo ziyara. Alal misali, idan ka ba da warƙar nan Mene ne Ra’ayinka Game da Nan Gaba? za ka iya koma ziyara don ka tattauna tambayar nan: “Ta yaya Allah zai mai da duniya ta zama wuri mai kyau?” An saka Matta 6:9, 10 da kuma Daniyel 2:44 a ciki. Warƙar nan Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa? tana da wannan tambayar: “Me ya sa muke tsufa da kuma mutuwa?” An saka Farawa 3:17-19 da kuma Romawa 5:12 a ciki.
13. Ka bayyana yadda za ka iya yin amfani da warƙoƙi wajen soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane.
13 Ka yi amfani da warƙoƙi wajen soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Akwai wani ƙaramin akwati da ke bayan warƙar, da ake kira QR, wato (quick response code), idan an yi amfani da shi, za a iya shiga wani shafi a dandalinmu da za a ga bidiyon nan “Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?” kuma wannan bidiyon yana ƙarfafa mutane su soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Warƙoƙin sun yi nuni ga wani darasi da ke ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Alal misali, warƙar nan Wane ne Ainihi Yake Iko da Duniya? ya yi nuni ga darasi na biyar na wannan ƙasidar. Warƙar nan Mene ne Ke Kawo Farin Ciki a Iyali? ya yi nuni ga darasi na tara. Yin amfani da warƙoƙinmu yadda ake so zai sa a bi tsari mai kyau na yin amfani da Littafi Mai Tsarki sa’ad da ake wa’azi gida-gida da kuma koma ziyara. A sakamakon haka, za ka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Mene ne kuma za ka iya yi don ka ƙware a yin amfani da Kalmar Allah a hidimarka?
KA TATTAUNA BATUN DA KE DAMUN MUTANE
14, 15. Ta yaya za ka yi koyi da Bulus a wa’azi?
14 Bulus ya kasance da burin sanin tunanin mutane “masu-yawa” a hidimarsa. (Karanta 1 Korintiyawa 9:19-23.) Ka lura cewa Bulus ya so ya “ribato Yahudawa . . . , waɗanda ke ƙarƙashin shari’a . . . , waɗanda ba su da shari’a” da kuma “raunana.” Hakika, ya so ya ribato ‘dukan mutane, domin ko da ƙaƙa [ya] ceci waɗansu.’ (A. M. 20:21) Ta yaya za mu yi koyi da Bulus sa’ad da muke yin shirin yi wa “dukan mutane” wa’azi a yankinmu?—1 Tim. 2:3, 4.
15 A kowane wata, muna samun shawarwari a Hidimarmu ta Mulki da za su taimaka mana sa’ad da muke yin wa’azi. Ka gwada yin amfani da waɗannan shawarwari. Amma idan ka san wasu abubuwa da ke damun mutane a yankinku, ka shirya gabatarwa da za ta jawo hankalinsu don su so saƙonmu. Ka yi la’akari da yankinku da irin mutanen da ke zama a wurin da kuma abin da suka fi damuwa da shi. Bayan haka, sai ka yi tunani a kan nassin da za ka karanta da ya yi magana a kan abin da ke damunsu. Wani mai kula mai ziyara ya faɗi yadda shi da matarsa suke mai da hankali ga yin amfani da Littafi Mai Tsarki, ya ce: “Yawancin mutane suna ba mu damar karanta nassi ɗaya idan muka taƙaita saƙonmu. Bayan mun gai da mutane yadda aka saba yi a yankin muna riƙe da Littafi Mai Tsarki a buɗe, sai mu karanta nassi ba tare da ɓata lokaci ba.” Ga wasu misalan batutuwa da tambayoyi da kuma nassosin da za ka iya yin amfani da su a yankinku.
16. Ka bayyana yadda za a iya yin amfani da littafin Ishaya 14:7 a wa’azi.
16 Idan kana zama a wurin da ake yawan zalunci da kuma nuna ƙarfi, za ka iya yin wannan tambayar: “Ka taɓa yin tunani cewa wannan zai zama kan maganar labarai wata rana: ‘Duniya ta huta yanzu daga tashin hankali. Mutane suna murna’? Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ke nan a Ishaya 14:7. Babu shakka, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da alkawura da yawa da Allah ya yi game da kwanciyar hankali da za a samu a nan gaba.” Sai ka karanta ɗaya daga cikin waɗannan alkawuran daga Littafi Mai Tsarki.
17. Ta yaya za ka yi amfani da Matta 5:3 sa’ad da kake yin wa’azi?
17 Shin yana wa mazaje da yawa a yankinku wuya su kula da iyalinsu? Idan haka ne, za ka iya yi musu wannan tambayar: “Nawa ne mutum yake bukata don shi da iyalinsa su yi farin ciki?” Idan ya ba da amsa, sai ka ce: “Mutane da yawa suna samun fiye da haka, amma, iyalinsu ba sa gamsuwa. Saboda haka, mene ne ake bukata?” Sai ka karanta Matta 5:3 kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku yi nazarin Littafi Mai Tsarki.
18. Ta yaya za mu yi amfani da Irmiya 29:11 wajen ƙarfafa mutane?
18 Shin mutane a yankinku suna wahala ne saboda wani bala’in da ya addabe su a kwanan nan? Za ka iya soma gabatarwarka da cewa: “Na zo gidanka don in ƙarfafa ka. (Karanta Irmiya 29:11.) Ka lura da wasu abubuwa biyu da Allah ya shirya mana kuwa? ‘Lafiya’ da kuma ‘bege mai kyau.’ Shin ba abin farin ciki ba ne sanin cewa Allah yana so mu ji daɗin rayuwa? Amma ta yaya hakan zai yiwu?” Sai ka nuna wa mutumin darasin da ya dace a ƙasidar nan Albishiri Daga Allah!
19. Ka bayyana yadda za a iya yin amfani da littafin Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7 wajen tattauna da mutanen da suke son addini.
19 Kana zama ne a yanki da mutane suke son addini? Idan haka ne, za ka iya soma tattaunawa da wannan tambayar: “A ce mala’ika ya yi maka magana, za ka yi abin da ya gaya maka kuwa? (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.) Da yake mala’ikan nan ya ce ka ‘ji tsoron Allah,’ kana ganin bai da muhimmanci mu san Allahn da yake so mu ji tsoronsa? Mala’ikan ya ɗan bayyana wannan Allahn sa’ad da ya ce, shi ne ‘wanda ya yi sama da duniya.’ Waye ke nan?” Sai ka karanta Zabura 124:8, da ta ce: “Taimakonmu yana wajen sunan Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasa.” Ka gaya masa cewa za ka dawo don ka bayyana masa ko wane ne wannan Ubangijin.
20. (a) Ta yaya za a iya yin amfani da Misalai 30:4 don a koya wa mutane sunan Allah? (b) Wane nassi ne ka taɓa amfani da shi kuma ka sami sakamako mai kyau?
20 Idan za ka tattauna da matashi, za ka iya cewa: “Zan so in karanta maka wani nassi da ya yi wata tambaya mai muhimmanci. (Karanta Misalai 30:4.) Babu wani ɗan Adam da zai iya yin waɗannan abubuwan, don haka, wannan wurin yana magana ne game da Mahaliccinmu. Ta yaya za mu san sunansa? Zan so in nuna maka sunan a cikin Littafi Mai Tsarki.”
KA BARI KALMAR ALLAH TA YI TASIRI A HIDIMARKA
21, 22. (a) Ta yaya yin amfani da nassi da ya dace da muka zaɓa zai iya canja halin mutum? (b) Mene ne ka ƙudura ka yi a hidimarka?
21 Ba za ka iya sanin yadda mutane za su ji ba idan ka karanta musu wani nassin da ka zaɓa da ya dace. Alal misali, wasu Shaidun Jehobah biyu a ƙasar Ostareliya sun ƙwanƙwasa ƙofar wata mata. Ɗaya daga cikinsu ya tambaye ta, “Kin san sunan Allah kuwa?” bayan haka, sai ya karanta Zabura 83:18. Matan ta ce, “Na yi mamaki sosai! Bayan da suka tafi, sai na yi tafiyar mil 35 (kilomita 56) zuwa wani shagon sayar da littattafai don in bincika wasu fassarar Littafi Mai Tsarki kuma na duba sunan a kamus. Sa’ad da na tabbata cewa sunan Allah shi ne Jehobah, sai na fahimci cewa akwai abubuwa da yawa da nake bukata in sani.” Bayan haka, sai ita da mutumin da ya zama mijinta suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma daga baya suka yi baftisma.
22 Kalmar Allah tana gyara halin mutanen da suke karanta ta kuma tana sa mu kasance da bangaskiya ga alkawuran Jehobah. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:13.) Maganar Allah tana da tasiri fiye da duk wani abin da za mu iya faɗa don mu ratsa zuciyar mutum. Shi ya sa ya kamata mu riƙa yin amfani da Kalmar Allah a kowane lokaci. Babu shakka, Kalmar Allah Rayayyiya ce!