Kana Samun ‘Abinci a Lotonsa’ Kuwa?
MUNA rayuwa ne a kwanaki mafi wuya a tarihin ’yan Adam. (2 Tim. 3:1-5) Kowace rana muna fuskantar gwaji domin muna ƙaunar Allah kuma muna bin ƙa’idodinsa. Yesu ya san cewa zamaninmu zai kasance da wuya, saboda haka, ya yi wa mabiyansa alkawari cewa zai tanadar musu da abubuwan da za su ƙarfafa su don su jimre har ƙarshe. (Mat. 24:3, 13; 28:20) Ya cika alkawarinsa ta wajen naɗa bawan nan mai aminci mai hikima don ya tanadar da ‘abinci a lotonsa,’ wato koyarwar da za ta ƙarfafa dangantakarsu da Allah.—Mat. 24:45, 46.
An naɗa bawan nan mai aminci a shekara ta 1919 kuma tun daga lokacin, bawan yana tanadar wa ‘iyalin gidan,’ wato bayin Allah koyarwa a harsuna da yawa. (Mat. 24:14; R. Yoh. 22:17) Amma, littattafan da ake wallafawa a wasu harsuna sun fi na wasu, ƙari ga haka, ba dukan mutane ba ne suke samun littattafanmu da ake sakawa a Intane. Alal misali, mutane da yawa ba sa samun bidiyo da talifofin da ake sakawa a dandalin jw.org. Shin hakan yana nufin cewa wasu Kiristoci ba sa samun isashen koyarwa da suke bukata ne? Bari mu tattauna wasu muhimman tambayoyi huɗu don mu sami amsar wannan tambayar.
1. Mene ne ainihi Jehobah yake amfani da shi don ya koyar da bayinsa?
Sa’ad da Shaiɗan ya jarabci Yesu ya mai da duwatsu su zama gurasa, Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (Mat. 4:3, 4) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da maganar Allah. (2 Bit. 1:20, 21) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ne ainihin abin da Jehobah yake amfani da shi don koyar da bayinsa.—2 Tim. 3:16, 17.
Ƙungiyar Jehobah ta tanadar da juyin Littafi Mai Tsarki na New World Translation of the Holy Scriptures, rabi ko cikakke a cikin harsuna sama da 120, kuma ana ci gaba da wallafa shi a ƙarin harsuna kowace shekara. Ban da wannan juyin, akwai biliyoyin juyin Littafi Mai Tsarki rabi ko cikakke a cikin harsuna dubbai. Wannan abin da aka cim ma ya nuna cewa nufin Allah ne “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:3, 4) Da yake ‘ba wata halittar da za ta iya ɓuya’ wa Jehobah, muna da tabbaci cewa zai jawo “masu ladabi a ruhu,” wato masu marmarin bauta masa zuwa ƙungiyarsa kuma zai tanadar da koyarwar da za ta ƙarfafa dangatakarsu da shi.—Ibran. 4:13, Littafi Mai Tsarki; Mat. 5:3, 6; Yoh. 6:44; 10:14.
2. Mene ne matsayin littattafanmu a tanadar da koyarwar gaskiya?
Wajibi ne mutum ya karanta Littafi Mai Tsarki, ya fahimta kuma ya yi amfani da abin da ya koya don ya kasance da bangaskiya sosai. (Yaƙ. 1:22-25) Abin da wani Bahabashe a ƙarni na farko ya ga cewa yana bukata ya yi ke nan. Sa’ad da Filibus ya ga wannan mutum yana karanta Kalmar Allah, sai ya tambaye shi: “Ka fahimci abin da kake karantawa?” Mutumin ya ce: “Yaya zan iya, sai ko wani ya bishe ni?” (A. M. 8:26-31) Filibus ya taimake shi don ya fahimci abin da yake karantawa. Abin da wannan mutumin ya koya ya motsa shi ya yi baftisma. (A. M. 8:32-38) Hakazalika, littattafanmu sun taimaka mana mu fahimci koyarwar gaskiya. Abin da muka koya ya taɓa zuciyarmu kuma ya sa muna rayuwar da ta jitu da nufin Allah.—Kol. 1:9, 10.
Bayin Jehobah suna samun abinci da yawa, wato koyarwar da ke ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah ta wajen littattafanmu. (Isha. 65:13) Alal misali, Hasumiyar Tsaro da ake wallafawa a cikin harsuna sama da 210 tana bayyana annabcin Littafi Mai Tsarki, tana sa mu ƙara fahimtar gaskiya kuma tana ƙarfafa mu mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Mujallar Awake! da ake wallafawa cikin harsuna wajen 100 tana ƙara mana ilimi game da halittun Jehobah masu ban sha’awa kuma tana sa mu yi amfani da shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki. (Mis. 3:21-23; Rom. 1:20) Bawa nan mai aminci yana tanadar da littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a harsuna sama da 680! Kana keɓe lokaci kowace rana don ka karanta Littafi Mai Tsarki kuwa? Kana karanta kowace sabuwar mujalla da ke fitowa da kuma sababbin littattafan da suke fita kowace shekara a yarenku kuwa?
Bugu da ƙari, ƙungiyar Jehobah tana wallafa awutlayi dabam-dabam da ake amfani da su wajen ba da jawabai a taron ikilisiya da kuma a manyan taro. Shin, kana jin daɗin jawabai da wasannin kwaikwaiyo da gwaji da kuma ganawa da ake yi a waɗannan taron? Babu shakka, Jehobah yana tanadar mana da abubuwa masu yawa da za su ƙarfafa dangantakarmu da shi!—Isha. 25:6.
3. Idan a yarenku ba ka samun dukan littattafanmu da ake wallafawa, shin hakan yana nufin cewa ba ka samun isashen abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarka da Allah ne?
Amsar ita ce a’a. Ƙari ga haka, ba abin mamaki ba ne cewa a wasu lokuta, wasu bayin Jehobah za su iya samun koyarwar Allah fiye da wasu. Me ya sa? Ka yi la’akari da manzannin Yesu, sun sami umurni daga wajen Yesu fiye da wasu almajirai a ƙarni na farko. (Mar. 4:10; 9:35-37) Duk da haka, sauran almajiran sun sami isashen koyarwa da suke bukata.—Afis. 4:20-24; 1 Bit. 1:8.
Ya kamata mu tuna cewa ba a rubuta yawancin abubuwan da Yesu ya koyar da kuma yi sa’ad da yake duniya a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Manzo Yohanna ya ce: ‘Akwai kuma waɗansu abu da yawa da Yesu ya yi; ina tsammani da a ce za a rubuta su kowane ɗaya, da duniya da kanta ba za ta ɗauki littattafai waɗanda za a rubuta ba.’ (Yoh. 21:25) Kiristoci a ƙarni na farko sun fi mu sanin abubuwan da Yesu ya koyar da kuma yi, duk da haka, muna samun dukan abubuwan da muke bukata. Jehobah ya tabbatar cewa ya tanadar mana da isashen bayani da muke bukata don mu bi gurbin Yesu.—1 Bit. 2:21.
Wani abu kuma da za mu tuna shi ne wasiƙun da manzannin Yesu suka aika wa ikilisiyoyi a ƙarni na farko. Akwai aƙalla wasiƙa ɗaya da Bulus ya rubuta da ba a saka cikin Littafi Mai Tsarki ba. (Kol. 4:16) Shin hakan yana nufin cewa ba mu da isashen koyarwar gaskiya da yake ba mu da wannan wasiƙa? A’a. Jehobah ya san abubuwan da muke bukata kuma yana tanadar mana da isashen abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da shi.—Mat. 6:8.
Jehobah ya san abubuwan da muke bukata kuma yana tanadar mana da isashen abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da shi
A yau, wasu bayin Jehobah suna samun koyarwa da kuma littattafai sosai fiye da wasu. Wataƙila ba a wallafa littattafanmu da yawa a yarenku. Idan haka ne, ka tuna cewa Jehobah yana ƙaunarka. Ka yi nazarin littattafan da ake wallafawa a yarenku kuma idan zai yiwu, ka riƙa halartan taro a yaren da ka iya. Ta hakan, za ka kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah.—Zab. 1:2; Ibran. 10:24, 25.
4. Idan ba ka iya samun abubuwan da ake sakawa a dandalinmu na jw.org ba, shin hakan yana nufin cewa dangantakarka da Jehobah za ta yi sanyi ne?
Akwai mujallunmu da kuma wasu littattafan yin nazarin Littafi Mai Tsarki a dandalinmu. Ban da haka, ana samun bayanai da suke taimaka wa ma’aurata da matasa da iyaye masu ƙananan yara. Iyalai suna amfana idan suka yi amfani da waɗannan abubuwan sa’ad da suke Ibada ta Iyali. Ƙari ga haka, dandalinmu yana ɗauke da rahotanni game da wasu batutuwa na musamman, kamar rahoton sauke karatu a makarantar Gilead da taron shekara-shekara, kuma ana sanar da ’yan’uwa a faɗin duniya game da bala’i da kuma shari’o’in kotu da suka shafi Shaidun Jehobah. (1 Bit. 5:8, 9) Har ila, dandalin yana da amfani sosai wajen yaɗa bishara a ƙasashe dabam-dabam, har ma a ƙasashen da aka saka takunkumi a aikinmu ko kuma an hana aikin gaba ɗaya.
Duk da haka, za ka iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah ko da ba ka shiga dandalinmu. Bawan nan mai aminci ya yi aiki tuƙuru wajen tanadar da littattafai da aka buga don dukan Kiristoci su sami isashen abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Saboda haka, kada ka ɗauka cewa wajibi ne ka sayi na’ura don shiga dandalin jw.org. Wasu ’yan’uwa za su iya gurza bayanai da ake sakawa a dandalinmu kuma su ba wa waɗanda ba sa shiga dandalin, amma ba wajibi ba ne ikilisiyoyi su yi hakan ba.
Muna godiya cewa Yesu ya cika alkawarin da ya yi na tanadar mana da abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da tanadar mana da irin wannan ‘abinci a lotonsa,’ har ƙarshen wannan mugun zamani.