DAGA TARIHINMU
“Tsugune Ba ta Ƙare Ba”
A SHEKARA ta 1923, mutane sun cika babban ɗakin taro na koyar da wasan kwaikwayo da waƙa a birnin São Paulo! Ka yi tunanin kana jin muryar George Young sa’ad da yake jawabi kuma ana ta fassara jawabin jimla bayan jimla zuwa yaren Portuguese. Dukan mahalarta 585 suna sauraron jawabin da kyau. Ana nuna Nassosin da yake karantawa a telibijin da yaren Portuguese. An rarraba kofi ɗari na ƙasidar nan Millions Now Living Will Never Die!, wato (Miliyoyin Mutane da Suke Rayuwa Yanzu Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba!) a yaren Portuguese kuma an raba kofi 30 a Turanci da Jamusanci da kuma Italiyanci. Jawabin ya yi daɗi kuma labarin ya bazu sosai. Bayan kwana biyu, sai wannan babban ɗakin taron ya sake cika da mutane da suka zo don su saurari wani jawabi. Amma waɗanne abubuwa suka faru kafin waɗannan taron?
Sarah Bellona Ferguson da iyalinta sun ƙaura daga ƙasar Amirka zuwa Brazil a shekara ta 1867. A shekara ta 1899 ne Sarah ta karanta wasu littattafan da ƙaninta ya kawo daga Amirka kuma ta fahimci cewa ta gano koyarwa ta gaskiya. Da yake tana jin daɗin karanta littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki, ta ce a riƙa aiko mata da Hasumiyar Tsaro na Turanci. Saƙon Littafi Mai Tsarki da ta karanta ya burge ta sosai shi ya sa ta rubuta wa Ɗan’uwa Charles Taze Russell wasiƙa. A cikin wasiƙar ta ce “misalinta tabacci ne cewa babu wanda ya yi nisa ainun har da bishara ba za ta iya isa wajensa ba.”
Sarah Ferguson ta yi ƙwazo sosai wajen yaɗa saƙon Littafi Mai Tsarki, amma takan yi tunanin wanda zai taimaka mata da iyalinta da kuma sauran mutane masu kirki da ke ƙasar Brazil. A shekara ta 1912 ne aka sanar da ita daga Bethel da ke Brooklyn cewa wani zai zo birnin São Paulo da dubban kofofin warƙar nan Where Are the Dead? wato, Ina Matattu Suke? a yaren Portuguese. A shekara ta 1915, ta ce tana yawan mamaki a kan dalilin da ya sa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa suke begen zuwa sama ba da daɗewa ba. Ta bayyana ra’ayinta cewa: “To, me zai faru da ƙasar Brazil da kuma Amirka ta Kudu? . . . Idan ka yi tunanin yawan mutanen da suke ƙasar Amirka ta Kudu, za ka yarda cewa da sauran girbi. Hakika, tsugune ba ta kare ba!”
A misalin shekara ta 1920, wasu matuƙan jirgin ruwa guda takwas daga ƙasar Brazil sun halarci taro a ƙasar Amirka sa’ad da ake gyara musu jirgin yaƙinsu da ya lalace. Da suka dawo birnin Rio de Janeiro da suke da zama, sai suka gaya wa mutane abubuwan da suka koya daga Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, sai ga mai kula mai ziyara mai suna George Young a birnin Rio de Janeiro a watan Maris na shekara ta 1923 kuma ya tarar da mutane da suke son saƙon Littafi Mai Tsarki. Ya sa aka fassara wasu littattafai zuwa yaren Portuguese. Jim kaɗan, sai Ɗan’uwa Young ya je birnin São Paulo da ke da mazauna 600,000 a lokacin. A wurin ne ya yi jawabi kuma ya rarraba ƙasidu kamar yadda aka ambata a farkon wannan talifin. Ɗan’uwan ya ce: “Da yake ni kaɗai ne, na dangana sosai ga jaridu don gayyatar mutane su saurari jawaban.” Ya ƙara da cewa, “waɗannan ne jawabai na farko da aka yi da sunan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a ƙasar Brazil, wato International Bible Students Association.”a
Rahoton ƙasar Brazil da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga watan Disamba na shekara ta 1923, ya ce: “Idan muka yi la’akari da cewa an soma wannan aikin ran 1 ga watan Yuni kuma a lokacin ba mu da ko wani littafi guda a yaren, babu shakka, za mu iya kammalawa cewa Ubangiji ya albarkaci aikinmu sosai.” Rahoton ya ci gaba da cewa jawabai guda 21 ne aka yi a São Paulo daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa 30 ga Satumba kuma mutane 3,600 ne suka halarta. Ƙari ga haka, Ɗan’uwa Young ne ya yi biyu daga cikin jawaban. An yaɗa saƙon Mulkin a birnin Rio de Janeiro a hankali. A cikin ’yan watanni kawai, an rarraba littattafai fiye da 7,000 a yaren Portuguese! Ban da haka ma, an soma wallafa Hasumiyar Tsaro a yaren Portuguese da fitowar Nuwamba-Disamba 1923.
Hasumiyar Tsaro ta ba da rahoton abin da ya faru a lokacin da George Young ya kirawo Sarah Ferguson. Ta ce: “Da ’yar’uwar ta shiga cikin falo kuma ta ga Ɗan’uwa Young, sai ta kasa yin magana. Sai ta riƙe hannunsa, tana zuba masa idanu, bayan haka sai ta ce: ‘Kai ne mai kula mai ziyara da muke jin labarinsa?’” Ba da daɗewa ba, ita da wasu cikin yaranta suka yi baftisma. Hakika, ta yi shekara 25 tana jira a yi mata baftisma! Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta 1924 ta ce mutane hamsin ne suka yi baftisma a ƙasar Brazil kuma yawancinsu daga birnin Rio de Janeiro ne.
Yanzu bayan shekara 90, ba ma bukata mu yi tambayar nan: “To, me zai faru da ƙasar Brazil da kuma Amirka ta Kudu?” Domin yanzu muna da Shaidu fiye da 760,000 a ƙasar Brazil da suke wa’azi. Kuma a Nahiyar Amirka ta Kudu ma, ana nan ana wa’azin Mulkin a harsunan Portuguese, Sifanisanci da kuma wasu harsuna da yawa da ake yi a ƙasar. Furucin da Sarah Ferguson ta yi a shekara ta 1915 daidai ne cewa, ‘Tsugune ba ta ƙare ba’ a lokacin.—Daga tarihinmu a ƙasar Brazil.
a “International Bible Students Association suna ne da ake kiran Shaidun Jehobah a dā.”