DAGA TARIHINMU
Ya Yi Shekara 100 Yana Ƙarfafa Imaninmu
“Lallai, mutumin da aka nuna a wannan fim ɗin ya yi kama da Ɗan’uwa Russell sosai.”—In ji wani da ya kalli fim ɗin “Photo-Drama of Creation” a shekara ta 1914.
SHEKARA 100 ke nan tun da aka shirya fim ɗin nan “Photo-Drama of Creation.” An shirya wannan fim ɗin don ya ƙarfafa bangaskiyar mutane ga Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki. Bidiyon ya sa mutane su san cewa Jehobah ne Mahaliccinmu duk da yake koyarwar ra’ayin bayyanau da sūkar Kalmar Allah ya zama ruwan dare kuma ya gurɓata imanin mutane da yawa.
Ɗan’uwa Charles Taze Russell, wanda ke ja-gorar Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a lokacin, ya nemi hanya mafi kyau da kuma mafi sauri na yaɗa gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun riga sun yi fiye da shekara 30 suna yin amfani da littattafai da mujallu don yin wa’azi. Amma yanzu, sun kirkiro wani sabon abin da zai jawo hankalin mutane, wato fim.
YIN WA’AZI TA HANYAR FIM
An fara fitar da fim marar sauti a tsakanin shekara ta 1890 zuwa 1899. A shekara ta 1903, an nuna wani fim na addini a wani coci a birnin New York, a Amirka. Kamfanoni masu tsara fina-finai ba su ƙware ba tukun a shekara ta 1912 sa’ad da Ɗan’uwa Russell ya soma shirya fim ɗin “Photo-Drama of Creation.” Ya fahimci cewa wannan hanyar koyar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki za ta fi yin amfani da littattafai.
Fim ɗin “Photo-Drama of Creation” yana da sashe huɗu kuma baki ɗayansa sa’o’i takwas ne. Fim ɗin yana da jawabai na Littafi Mai Tsarki guda 96 wanda wani ɗan’uwa mai muryar mai daɗi ya ɗauka. An saka waƙoƙi masu daɗi a wasu sassan fim ɗin. Wani ƙwararre da ya iya na’ura sosai ne yake buga sautin da waƙar a garmaho tare da fim da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki.
“Yana ɗauke da hotunan daga halittar taurari har ƙarshen Sarautar Yesu ta Shekara Dubu.” —F. Stuart Barnes, ɗan shekara 14 a shekara ta 1914
An samo yawancin hotunan daga wurin masu yin fim. Ƙwararrun masu zane-zane a birnin Philadelphia da New York da Paris da kuma Landan ne suka zana hotunan ɗaya bayan ɗaya. ’Yan’uwa da ke aiki a Sashen Zane-zane a Bethel ma sun yi zane da yawa, a yawancin lokaci, suna gyara hotunan da suka lalace. Ƙari ga sayan fina-finai, an ɗauki hotunan ’yan’uwa a Bethel a birnin Yonkers a New York yayin da suka yi shiga kamar Ibrahim da Ishaƙu da kuma mala’ikan da ya hana Ibrahim yin hadaya da ɗansa.—Far. 22:9-12.
Wani abokin aikin Ɗan’uwa Russell ya gaya wa maneman labarai cewa wannan hanyar sadarwa “za ta sa mutane da yawa su so saƙon Nassosi fiye da kowane abu da aka taɓa yi don yaɗa koyarwar addini.” Shin limamai sun yi farin ciki don wannan sabon fim da zai taimaka wa mutane su daɗa sanin Allah? Ko kaɗan. Limaman Kiristendam sun yi tir da fim ɗin “Photo-Drama of Creation,” wasu ma cikinsu sun yi amfani da hanyoyi dabam-dabam don hana mutane kallonsa. A wata majami’a da ake kallon wannan fim ɗin, wani limami ya sa aka yanka wutar lantarkinsu.
Duk da haka, jama’a suna cika majami’a don su kalli fim mai suna “Photo-Drama of Creation” kyauta. Wajen birane 80 a ƙasar Amirka ne suke yin shiri don su kalli fim ɗin a kowace rana. Wannan lokaci ne na farko da masu kallo da yawa suka kalli fim da mutane suke motsi a ciki. Sun kalli inda aka nuna yadda ƙwai ya ƙyanƙyashe kuma ’yar tsaki ta fito. Bayanan kimiyya da suka kalli a ranar sun nuna hikimar Jehobah. Kamar yadda aka ambata ɗazun, sa’ad da wani mutum da ya kalli fim ɗin ya ga Ɗan’uwa Russell yana yin gabatarwa, sai ya ce “Lallai, mutumin da aka nuna a wannan fim ɗin ya yi kama da Ɗan’uwa Russell sosai!”
LOKACI NA MUSAMMAN A ILIMANTARWAR LITTAFI MAI TSARKI
Wani ɗan tarihin fim mai suna Tim Dirks ya ce “Photo-Drama of Creation” ne “fim na farko da aka nuna mutane suna motsi da magana kuma hotuna masu launi mai kyau.” An yi amfani da wannan fasalin don yin wasu fina-finai kafin “Photo-Drama of Creation,” amma ba a yi amfani da dukan fasalin ba musamman ma waɗanda suke da jigon Littafi Mai Tsarki. Mutane miliyan tara a Arewacin Amirka da Turai da Ostareliya da New Zealand sun kalli wannan fim ɗin kuma babu fim da aka taɓa kallo haka cikin shekara guda.
An fara fitar da “Photo-Drama of Creation” a ranar 11 ga Janairu, 1914, a birnin New York. Watanni bakwai bayan haka, sai aka soma Yaƙin Duniya na Ɗaya da ya ci rayukan mutane da yawa. Amma mutane daga ƙasashe dabam-dabam sun ci-gaba da taruwa don su kalli wannan fim ɗin kuma suna samun ƙarfafa daga albarkar da Mulkin Allah zai kawo. Daga shekara ta 1914, babu wani abin da za a iya gwadawa da wannan fim ɗin “Photo-Drama of Creation.”