Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 1/15 pp. 27-31
  • Yaushe Ne ‘Mulkin Allah Zai Zo?’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaushe Ne ‘Mulkin Allah Zai Zo?’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MAHAYAN DAWAKIN SU BAYYANA
  • MUGUNTA TANA DAƊA ƘARUWA
  • WANNAN TSARAR BA ZA TA SHUƊE BA
  • YESU ZAI YI NASARA NAN BA DA DAƊEWA BA
  • ‘Bari Mulkinka Ya Zo’
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ka Yi Sauraron Ranar Jehovah
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 1/15 pp. 27-31

Yaushe Ne ‘Mulkin Allah Zai Zo?’

“Lokacin da kun ga waɗannan al’amura duka, ku sani ya yi kusa, har bakin ƙofa.”—MAT. 24:33.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya abubuwan da ke faruwa a duniya tun shekara ta 1914 suke cika annabcin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne yanayin duniya da ke daɗa muni yake nuna mana?

  • Mene ne ra’ayinka da yake ƙarshe ya kusa?

1, 2. (a) Mene ne zai iya jawo wata irin makanta? (b) Mene ne muka sani game da Mulkin Allah?

WATAƘILA ka lura cewa idan wani abu ya faru, waɗanda ke wurin ba sa iya bayyana abin da ya faru daidai iri ɗaya. Hakazalika, zai kasance da wuya mutum ya tuna abin da likita ya gaya masa dalla-dalla bayan ya yi masa gwaje-gwaje kuma ya gano ciwon da ke damunsa. Ko kuma mutum zai iya riƙe makullinsa ko kuma tabaraunsa a hannu, amma ya ta nemansa. Me ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa? Masu bincike sun ce irin wannan makantar takan auku ne sa’ad da muke ƙoƙarin yi abubuwa da yawa a lokaci ɗaya. Babu shakka, ƙwaƙwalwarmu za ta iya mai da hankali a yin abu ɗaya ne kawai a lokaci guda.

2 Mutane da yawa a yau suna fuskantar irin wannan “makantar” a abubuwan da ke faruwa a duniya. Wataƙila su amince cewa duniya ta canja sosai tun shekara ta 1914, amma ba su san abin da hakan yake nufi ba. A matsayin ɗaliban Littafi Mai Tsarki, mun san cewa an kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914, sa’ad da aka naɗa Yesu Sarki a sama. Amma har ila, ba a gama amsa wannan addu’ar cewa, ‘Mulkinka ya zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama’ ba. (Mat. 6:10) Za a amsa wannan addu’ar gabaki ɗaya sa’ad da aka cire wannan muguwar duniyar. Sai idan hakan ya faru ne za a ce an yi nufin Allah a duniya kamar yadda ake yi a sama.

3. Mene ne muka gano ta wajen yin nazarin Kalmar Allah?

3 Da yake muna nazarin Kalmar Allah a kai a kai, muna ganin yadda wannan annabcin yake cika a yau. Babu shakka, hakan ya bambanta mu da yawancin mutane! Sun shaƙu da cin rayuwa har sun kasa ganin tabbaci cewa Kristi ya soma sarauta tun daga shekara ta 1914 kuma zai halaka wannan muguwar duniyar. Amma, ka yi wa kanka waɗannan tambayoyin: Shin har ila na gaskata cewa ƙarshen wannan duniyar ya kusa kuma abubuwan da suke faruwa a duniya a yau sun tabbatar da hakan? Ko da ba ka jima da zama Mashaidi ba, a kan me ka fi maida wa hankali? Ko da mene ne amsarmu, bari mu tattauna dalilai uku masu muhimmanci da za su sa mu kasance da tabbaci cewa, nan ba da daɗewa ba, za a yi nufin Allah a duniya.

MAHAYAN DAWAKIN SU BAYYANA

4, 5. (a) Mene ne Yesu yake yi tun daga shekara ta 1914? (Ka duba hoto na farko a talifin nan.) (b) Mene ne sukuwar mahayan dawaki uku take wakilta, kuma yaya wannan annabcin ya cika?

4 A shekara ta 1914 ne aka saka wa Yesu Kristi rawani a sama, wato ya zama Sarkin Mulkin Allah. Annabcin da aka rubuta a littafin Ru’ya ta Yohanna sura 6 ya ce Yesu yana sukuwa a kan farar doki. Nan da nan bayan ya zama Sarki, sai ya je don ya kammala cin nasara a kan muguwar duniyar Shaiɗan. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 6:1, 2.) Annabcin ya ce bayan an kafa Mulkin Allah, matsalolin duniya za su daɗa tsanani. Yaƙi da rashin abinci da cuta da kuma wasu abubuwan da ke jawo mutuwa za su daɗa tsanani. Mahayan dawaki guda uku da ke sukuwa a bayan Yesu Kristi da aka ambata a cikin annabcin suna wakiltar waɗannan matsalolin.—R. Yoh. 6:3-8.

5 An ambata a cikin annabcin cewa an “amshi salama daga duniya.” Hakan ya faru duk da cewa al’ummai da yawa sun yi alkawarin kasancewa da haɗin kai da kuma salama. Yaƙin Duniya ta Ɗaya ce yaƙi ta farkon cikin yaƙe-yaƙe masu tsanani da suka taɓa auku kuma suka ɗauke salama daga duniya. Tun daga shekara ta 1914, an sami ci gaba sosai a tattalin arziki da kuma kimiyya, amma har ila ƙarancin abinci ya ci gaba haifar da tashin hankali da kuma yaƙe-yaƙe a wurare dabam-dabam a duniya. A bayyane yake cewa cuta da bala’i da kuma wasu matsaloli suna ɗaukan rayukan miliyoyin mutane a kowace shekara. Waɗannan abubuwan suna da haɗari sosai, suna daɗa faruwa kusan kullum kuma suna kashe mutane sosai fiye da dā. Shin ka san abin da hakan yake nufi?

6. Su wane ne suka mai da hankali ga annabcin Littafi Mai Tsarki, kuma me suka yi sa’ad da annabcin ya cika?

6 Hankalin mutane da yawa ya rabu sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na Ɗaya kuma cutar da ake kiran Spanish Flu ta ɓarke. Amma, Kiristoci shafaffu suna ɗokin ganin cewa Lokuttan Al’ummai ko kuma “zamanan Al’ummai” sun cika a shekara ta 1914. (Luk 21:24) Shafaffu ba su san ainihin abin da zai faru ba, amma sun san cewa a shekara ta 1914, wani abu mai muhimmanci da ya shafi Mulkin Allah zai faru. Nan da nan bayan sun fahimci cewa annabcin Littafi Mai Tsarki ya cika, sai suka sanar cewa Mulkin Allah ya soma sarauta. Kuma an tsananta musu sosai sa’ad da suka soma wa’azin Mulki. Wannan tsanantawar ma ta cika annabcin Littafi Mai Tsarki. A cikin shekaru da yawa bayan hakan, maƙiyan Mulkin sun ƙoƙarta su sa a daina wa’azin ta wajen yin amfani da dokoki da zalunci da fursuna da kuma kisa ta ratayewa da harɓi ko kuma yanke kai.—Zab. 94:20; R. Yoh. 12:15.

7. Me ya sa yawancin mutane ba sa iya ganin abubuwan da suke faruwa a duniya a yau?

7 Idan akwai tabbaci sosai da ya nuna cewa Mulkin Allah yana sarauta yanzu a sama, shin me ya sa yawancin mutane ba sa ganin haka? Me ya sa ba sa ganin cewa abubuwan da ke faruwa a duniya suna cika annabcin Littafi Mai Tsarki daidai yadda mutanen Allah suke faɗa tun shekaru da yawa? Wataƙila yawancin mutane suna mai da hankali a kan abubuwan da za su iya gani da idanunsu ne kawai. (2 Kor. 5:7) Shin sun shagala ne da harkokinsu har suka kasa ganin abin da Allah yake yi? (Mat. 24:37-39) Shin ayyukan wannan duniyar sun janye hankalin wasu ne? (2 Kor. 4:4) Idan muna so mu fahimci abin da Mulkin Allah yake yi, muna bukatar bangaskiya don mu iya fahimtar hakan. Muna farin ciki sosai da yake muna ganin abubuwan da ke faruwa!

MUGUNTA TANA DAƊA ƘARUWA

8-10. (a) Ta yaya abin da ke littafin 2 Timotawus 3:1-5 yake cika? (b) Me ya sa muka ce mugunta tana daɗa ƙaruwa?

8 Dalili na biyu da ya sa muka sani cewa Mulkin Allah zai yi sarauta bisa duniya nan ba da daɗewa ba, shi ne: Muguntar da ake yi a duniya tana daɗa ƙaruwa. A kusan shekara ɗari, mun ga yadda annabcin da ke littafin 2 Timotawus 3:1-5 yake cika. Irin halayen da aka ambata a waɗannan ayoyin suna yaɗuwa a dukan ɓangaren duniya. Shin kana ganin hakan kuwa? Bari mu tattauna wasu misalai.—Karanta 2 Timotawus 3:1, 13.

9 Ka gwada abubuwan da mutane suke ƙyama a tsakanin shekara ta 1940 zuwa 1959 da waɗanda ke faruwa yau a wajajen aiki da nishaɗi da wasanni da kuma ado da tufa. Mugunta da kuma lalata sun zama gama gari. Mutane suna aikata mugunta da lalata da kuma halayen banza don kawai su burge wasu. Shirye-shiryen talabijin da mutane a shekara ta 1950 zuwa 1959 suke ganin bai da kyau, shi ya zama abin da iyalai da yawa suke so. Kuma ’yan luwaɗi suna shafan nishaɗi da ado kuma suna ƙarfafa salon rayuwarsu a fili. Muna farin ciki ƙwarai don sanin ra’ayin Allah game da waɗannan abun!—Karanta Yahuda 14, 15.

10 Ka kuma gwada taurin kan matasan zamanin dā da na yanzu. Alal misali, tsakanin shekara ta 1950 zuwa 1959, iyaye suna damuwa sosai idan suka san cewa yaransu suna shan sigari ko giya ko kuma suna rawan ’yan iska. Amma a yau, muna jin wasu labarai masu ban tsoro kamar irin wannan: Wani ɗan shekara sha biyar ya harɓe wasu ’yan ajinsa, a sakamako, ya kashe guda biyu kuma guda sha uku sun ji rauni. Wani rukunin ’yan shaye-shaye sun kashe wata ’yar shekara tara kuma suka yi wa babanta da kuma wani danginta dukan tsiya. An ce a Asiya, matasa ne suke aikata rabin laifuffukan da aka yi tsakanin shekaru goma da suka shige. Shin akwai mutumin da zai ce mugunta ba ta daɗa ƙaruwa?

11. Me ya sa mutane da yawa ba sa fahimta cewa abubuwa suna daɗa tsanani?

11 Manzo Bitrus ya ce: “Cikin kwanaki na ƙarshe masu-ba’a za su zo da ba’a, suna bin nasu sha’awoyi, suna cewa, Ina alkawarin tafowarsa? gama, tun daga randa ubanni suka kwanta barci, dukan al’amura suna nan kamar yadda suke tun farkon halitta.” (2 Bit. 3:3, 4) Me ya sa mutane suke yin hakan? Wataƙila domin idan muka saba ganin wani abu, ba ma cika mai da masa hankali. Za mu iya razana idan halin wani abokinmu ya canja farat ɗaya. Amma, idan halaye ko ɗabi’ar mutane da dama ya canja a hankali, zai kasance da wuya mu lura da hakan. Bugu da ƙari, irin wannan canjin yana da lahani sosai.

12, 13. (a) Me ya sa bai kamata mu yi sanyi gwiwa game abubuwan da ke faruwa a yau ba? (b) Me zai taimaka mana mu jure da kwanaki na ƙarshe da ke da “wuya ƙwarai”?

12 Manzo Bulus ya gargaɗar da mu cewa a kwanaki na ƙarshe “za a sha wuya ƙwarai.” (2 Tim. 3:1, Littafi Mai Tsarki) Duk da haka, za mu iya mu yi rayuwa a duniyar nan kuma kasance da aminci ga Jehobah. Za mu iya shawo kan kowane tsoron da muke ji. Da taimakon Jehobah da ruhunsa mai tsarki da kuma ikilisiyar Kirista, za mu iya kasancewa da aminci. Allah zai ba mu “mafificin girman iko.”—2 Kor. 4:7-10.

13 Manzo Bulus ya soma annabci game da kwanaki na ƙarshen da furucin nan “ka san wannan.” Waɗannan kalamin sun nuna tabbaci cewa wannan annabcin zai cika. Mun san cewa muguntar wannan duniyar za ta ci gaba da ƙaruwa har sai Jehobah ya kawo ƙarshenta. ’Yan tarihi sun lura cewa idan mutanen wani yanki ko al’umma ba su ɗauki mizanan nagarta da mugunta da muhimmanci ba, al’ummarsu za ta taɓarɓare. Ba a taɓa raina mizanan nagarta da kuma mugunta kamar yadda ake yi a duniya a yau ba. Wataƙila mutane da yawa su ƙi da wannan gaskiyar, amma ya kamata abubuwan da suke faruwa tun daga shekara ta 1914 su tabbatar mana cewa Mulkin Allah zai kawo ƙarshen mugunta nan ba da daɗewa ba.

WANNAN TSARAR BA ZA TA SHUƊE BA

14-16. Wane dalili na uku ne ya sa muka gaskata cewa Mulkin Allah zai “zo” nan ba da daɗewa ba?

14 Har ila akwai dalili na uku da ya sa za mu kasance da tabbaci cewa ƙarshe ya kusa. Alal misali, kafin Mulkin Allah ya soma sarauta a sama, akwai wani rukunin shafaffu masu aminci da ke bauta wa Allah. Sa’ad da annabci bai cika kamar yadda suka yi tsammani ba a shekara ta 1914, mene ne suka yi? Yawancinsu sun ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci kuma sun jure wa gwaje-gwaje da kuma tsanantawa. A shekarun da suka shige, yawancin waɗannan shafaffun sun kasance da aminci har mutuwa.

15 Sa’ad da Yesu yake yin annabci game da ƙarshen wannan zamanin, ya ce: “Wannan tsara ba za ta shuɗe ba, sai an cika waɗannan abubuwa duka.” (Karanta Matta 24:33-35.) Mun fahimci cewa sa’ad da Yesu ya ambata “wannan tsarar,” yana magana game da rukunin Kiristoci shafaffu guda biyu ne. Rukuni na farko ya wanzu a shekara ta 1914 kuma ya gane cewa Yesu ya soma sarauta a matsayin Sarki a wannan shekarar. Waɗanda suka ƙunshi wannan rukunin suna da rai a shekara ta 1914 kuma an shafe su da ruhu mai tsarki kafin wannan shekarar ko kuma bayanta.—Rom. 8:14-17.

16 Rukuni na biyu da suka ƙunshi “wannan tsarar,” su ma suna da rai kuma an shafe su da ruhu mai tsarki a lokacin da wasu cikin rukuni na farko suke duniya. Saboda haka, ba dukan shafaffu ba ne a yau suke cikin “wannan tsarar” da Yesu ya ambata ba. A yau, waɗanda suke rukuni na biyu sun soma tsufa. Duk da haka, kalamin Yesu da ke littafin Matta 24:34 ya tabbatar mana cewa aƙalla wasu cikin ‘wannan tsara ba za su shuɗe ba’ kafin su ga somawar ƙunci mai girma. Hakan ya daɗa sa mu kasance da tabbaci cewa, nan ba da daɗewa ba, Sarkin Mulkin Allah zai halaka miyagu kuma ya kawo sabuwar duniya mai adalci.—2 Bit. 3:13.

YESU ZAI YI NASARA NAN BA DA DAƊEWA BA

17. Mene ne muka gane daga dalilai uku da muka tattauna?

17 Shin kana ganin yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika a yanzu kuwa? Yesu ya gargaɗar da mu cewa ba mu san ranar ko sa’ar da ƙarshe zai zo ba. (Mat. 24:36; 25:13) Amma, manzo Bulus ya ambata cewa mun san “lokacin nan,” wato kwanaki na ƙarshe. (Karanta Romawa 13:11.) Muna cikin wannan zamanin yanzu. Idan muka mai da hankali ga annabcin Littafi Mai Tsarki da abin da Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi suke yi, za mu ga sarai cewa ƙarshen wannan muguwar duniyar ya kusa.

18. Mene ne zai faru da waɗanda suka ƙi Yesu Kristi a matsayin Sarkinsu?

18 Nan ba da daɗewa ba, waɗanda suka ƙi amince da ikon Yesu, wanda shi ne Mahayin farar dokin, za su yarda cewa sun yi kuskure. Ba za su iya guje wa shari’ar da ke tafe ba. A lokacin, za su yi kuka ƙwarai suna cewa: “Wa ke da iko ya tsaya kuma?” (R. Yoh. 6:15-17) Ru’ya ta Yohanna sura ta 7 ta ba da amsar tambayar. Shafaffu da kuma “taro mai-girma” za su “tsaya” domin Allah ya amince da su. Bayan hakan, “taro mai-girma” na waɗansu tumaki za su tsira daga ƙunci mai girma.—R. Yoh. 7:9, 13-15.

19. Me kake ɗokin yi da yake ka san cewa ƙarshe ya yi kusa?

19 Idan muka ci gaba da mai da hankali ga annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suke cika a zamaninmu, duniyar Shaiɗan ba za ta janye hankalinmu ba. Za mu ga dalla-dalla ma’anar abubuwan da ke faruwa a duniya. Nan ba da jimawa ba, Yesu zai yi nasara kuma ya halaka wannan muguwar duniyar a lokacin yaƙi na ƙarshe, wato Armageddon. (R. Yoh. 19:11, 19-21) Ka yi tunanin irin farin ciki da za mu yi bayan hakan.—R. Yoh. 20:1-3, 6; 21:3, 4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba