DAGA TARIHINMU
“Ina Kamar Kunkuru a Cikin Ƙwaryarta”
SA’AD DA ake wani kamfen mai ci kamar wutar daji a watan Agusta da Satumba na shekara ta 1929, masu shela fiye da 10,000 sun yi wa’azi a ƙasar Amirka. Sun rarraba littattafai da mujallu guda dubu ɗari biyu da hamsin. Akwai majagaba guda dubu ɗaya cikin waɗannan masu shelan. Waɗannan majagaban sun yi yawa sosai! Hidimarmu ta Mulki ta ce “abin mamaki ne sosai” cewa an samu ƙaruwar majagaba ninki uku a tsakanin shekara ta 1927 zuwa 1929.
A shekara ta 1929, tattalin arziki ya soma taɓarɓarewa. A ranar Talata, 29 ga Oktoba, 1929, gurguncewar kasuwanci a birnin New York ta sa a faɗa cikin tawayar tattalin arziki. Duban bankuna suka rufe kuma gonaki suka daina aiki. Manyan kamfanoni suka rufe kuma miliyoyin mutane suka rasa aikinsu. A shekara ta 1933, ana kwace aƙalla gidaje dubu ɗaya a rana da aka yi jingina da su.
Ta yaya majagaba za su iya tsira a irin wannan mawuyacin yanayin? Ɗaki mai taya ce ta taimaka musu. Tun da ba a biyan kuɗin haya da na haraji a wannan ɗaki mai taya, majagaba sun samu damar yin hidimarsu ba tare da kashe kuɗi sosai ba.a Kuma a lokacin taron gunduma, wannan ɗaki mai taya yana zama masaukinsu kuma ba sa biyan ko sisi. A shekara ta 1934, Hidimarmu ta Mulki ta ba da fasalin yadda za a iya gina wannan gidan tare da saka masa bayan gida mai amfani da ruwa da rasho da gadon da ake naɗewa da kuma abin kāre sanyi.
Masu shela da ke da basira sosai sun gidan gidaje masu taya. Wani ɗan’uwa mai suna Victor Blackwell ya ce: “Nuhu bai iya gina jirgin ruwa ba, kuma ni ma ban iya gina ɗaki mai taya ba.” Amma duk da haka, ya gina gidan.
Avery da Lovenia Bristow suna da ɗaki mai taya. Avery ya ce, “Ina kamar kunkuru a cikin ƙwaryarta.” Avery da Lovenia Bristow sun yi hidimar majagaba tare da Harvey da Anne Conrow waɗanda suke da ɗaki mai taya da aka rufe bangon da takardu masu karo. Takardun suna faɗa ƙasa duk sa’ad da suke ƙaura da ɗakin wani wuri. Avery ya ce: “Babu mutumin da ya taɓa ganin irin wannan gidan kafin lokacin da kuma bayan hakan.” Amma Avery ya ce Harvey da Anne Conrow tare da yaransa biyu ne iyali mafi farin ciki da suka taɓa gani. Harvey Conrow ya ce: “Ba mu taɓa yin rashin kome ba, kuma hidimar Jehobah ta sa mu samu kāriya sosai.” Kuma daga baya, Harvey da Anne Conrow da yaransu biyu sun halarci Makarantar Gilead kuma an tura su yin hidima a ƙasar Peru a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje.
Su Battainos ma sun yi hidimar majagaba a matsayin iyali. Sa’ad da aka sanar da shi cewa matarsa ta yi juna biyu, sai suka mai da motarsu ƙirar Ford da ake yayi a shekara ta 1929 zuwa ɗaki. Ɗakin ya fi tantin da suke zama kafin lokacin kyau. Sun ci gaba da yin hidimarsu da suke so sosai tare da jaririyarsu, kuma suna wa Italiyawa da ke Amirka wa’azi.
Mutane da yawa sun saurari bisharar, amma tun da su talakawa ne kuma ba su da aiki, ba sa yawan ba da gudummawar kuɗi sa’ad da aka ba su littattafai. Maimakon haka, suna yin musanyar littattafan da wasu kayayyaki. Wasu majagaba biyu sun ambata kayayyaki iri-iri har guda sittin da huɗu da mutanen da suka wa wa’azi suka ba su. Sun karanta fallen littafin da suka rubuta sunan kayayyakin “kamar littafin da aka rubuta jerin sunayen kayayyaki a manyan shaguna.”
Wani ɗan’uwa mai suna Fred Anderson ya haɗu da wani manomi da ke son littattafanmu, sai ya ba masu shelan tabaran da mahaifiyarsa take amfani da su a dā. Sa’ad da ya je gonar da ke gaba, sai manomin ya ce yana son littattafanmu sosai, amma ba ya gani sosai kuma ba shi da tabarau. Mai shelan ya ba shi tabaran da ya karɓa daga wajen maƙwabcinsa. Sa’ad da ya saka su sun yi mai daidai, sai ya ba da gudummawar littattafan da kuma tabaran.
Herbert Abbott yana ɗaukan akurkin kaji a cikin motarsa mai ɗaki. Bayan an ba shi kaji uku ko huɗu sa’ad da yake wa’azi, sai ya kai su kasuwa ya sayar kuma ya sha māi a motar da kuɗin. Abbott ya ce: “A wasu lokatai, muna kashe duk kuɗinmu, amma ba mu ƙyale hakan ya sa mu sanyin gwiwa ba. Idan muna da māi a motarmu, za mu ci gaba da dogara ga Jehobah.”
Yin dogara ga Jehobah da kuma yin ƙarfin zuciya ya taimaka wa ’yan’uwa su jimre a waɗannan shekaru masu wuya sosai. Akwai wani lokaci da ake ruwa kamar da bakin ƙwarya, sai Maxwell da Emmy Lewis suka fita a guje daga motarsu, bayan haka, sai suka ga bishiya ta faɗo ta raba motar biyu. Maxwell ya ce, “Waɗannan aukuwar ba cin baya ba ne a gare mu domin ba mu taɓa tunanin ja da baya ba. Akwai ayyuka da yawa da muke bukatar mu yi kuma mun ƙudura mu yi su.” Maxwell da Emmy ba su yi fargaba ba kuma abokansu masu ƙauna sun taimaka musu su sake gina gidansu mai taya.
Miliyoyin Shaidun Jehobah masu ƙwazo suna sadaukar da kansu da yardar rai duk da ƙalubale. Muna yin koyi da misalan waɗannan majagaban kuma mun duƙufa mu ci gaba da yin wa’azi har sai Jehobah ya ce ya isa.
a A wannan lokacin, majagaba da yawa ba sa aiki. Suna karɓar littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da ɗan araha kuma idan suka sayar da su, sai su biya bukatunsu da kuɗin.