Abin Da Ke Ciki
15 ga Nuwamba, 2013
© 2013 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania.
NA NAZARI
30 GA DISAMBA, 2013–5 GA JANAIRU, 2014
Ka Kasance a Faɗake Domin Yin Addu’a
SHAFI NA 3 • WAƘOƘI: 67, 81
6-12 GA JANAIRU, 2014
Ta Yaya Za Mu Kasance da Haƙuri Yayin da Muke “Jira”?
SHAFI NA 10 • WAƘOƘI: 119, 32
13-19 GA JANAIRU, 2014
Su Waye Ne Makiyaya Bakwai da Shugabanni Takwas a Yau?
SHAFI NA 16 • WAƘOƘI: 43, 123
20-26 GA JANAIRU, 2014
Ka Yi Biyayya ga Makiyayan da Jehobah Ya Naɗa
SHAFI NA 21 • WAƘOƘI: 125, 122
27 GA JANAIRU, 2014–2 GA FABRAIRU, 2014
Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
SHAFI NA 26 • WAƘOƘI: 5, 84
TALIFOFIN NAZARI
▪ Ka Kasance a Faɗake Domin Yin Addu’a
Yayin da ƙarshen wannan mugun zamanin da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan yake kusatowa, ya wajaba mu yi hankali don kada dangantakarmu da Jehobah ta yi tsami. Wannan talifin ya tattauna yadda yin lura tare da yin addu’a zai taimaka mana mu kasance a faɗake.
▪ Ta Yaya Za Mu Kasance da Haƙuri Yayin da Muke “Jira”?
Ka koyi yadda za mu iya amfana daga haƙurin da Mikah ya yi. Ka bincika abin da zai faru yayin da muke jira Jehobah ya kawo ƙarshen wannan mugun zamanin. Ka kuma koyi yadda za mu iya nuna godiya don jimirin Allah.
▪ Su Waye Ne Makiyaya Bakwai da Shugabanni Takwas a Yau?
Za mu iya koyon darussa masu muhimmanci game da harin da Sennakerib ya kai wa Urushalima a zamanin Hezekiya. Wannan talifin zai taimaka wa dattawa musamman, domin su aka danƙa wa hakkin kula a cikin ikilisiya.
▪ Ka Yi Biyayya ga Makiyayan da Jehobah Ya Naɗa
▪ Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
Sashe na farko na wannan talifin ya tattauna yadda Jehobah da kuma Yesu suke kula da garkensu da ke duniya a yau. Ya kuma tattauna ra’ayin da garken ya kamata ya kasance da shi yayin da makiyayan suke kula da shi. Sashe na biyu kuma ya bayyana halayen da ya kamata dattawa su kasance da su yayin da suke aikinsu na masu kula da garken Allah.
BANGO: Yin wa’azi a kan titi a tashar jirgin ƙasa a birnin Tokyo. Fiye da mutane miliyan biyu da dubu dari takwas suna zuwa birnin Tokyo kowace rana. Ana ƙoƙartawa don a yi wa’azi ga mutanen da ba a tarar da su a gidajensu ba
JAPAN
YAWAN JAMA’A:
126,536,000
ABIREJIN MASU SHELA:
216,692
MAJAGABA NA KULLUM:
65,245