Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 10/15 pp. 7-11
  • Halitta Tana Bayyana Allah Mai Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Halitta Tana Bayyana Allah Mai Rai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TABBACI DA DALILI NE KE SA MU KASANCE DA BANGASKIYA
  • HALITTA TANA NUNA IKON ALLAH
  • HALITTA TANA BAYYANA HIKIMAR ALLAH
  • KA TAIMAKI MUTANE SU GIRMAMA ALLAH MAƊAUKAKI
  • Matasa, Ku Karfafa Bangaskiyarku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Kana Nuna Godiya Don Alherin Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Karfafa Bangaskiyarka Cewa Akwai Mahalicci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ruhu Mai Tsarki Ya Yi Aiki Wajen Halitta!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 10/15 pp. 7-11

Halitta Tana Bayyana Allah Mai Rai

“Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka . . . gama kai ka halicci dukan abu.”—R. YOH. 4:11.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne ya wajaba mu yi don mu shawo kan koyarwar ƙarya?

  • Ta yaya halitta ta nuna iko da kuma hikimar Allah?

  • Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su yi imani da Jehobah?

1. Me ya wajaba mu yi don mu tabbata cewa mun yi imani ga Allah?

MUTANE da yawa sun ce sun fi gaskatawa da abin da suke gani da idanunsu ɓaro-ɓaro. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce babu ‘wanda ya taɓa ganin Allah daɗai.’ (Yoh. 1:18) Tun da ba za mu iya ganin Allah ba, ta yaya za mu iya taimaka wa mutane su yi imani da shi? Mene ne za mu iya yi don mu tabbata cewa mun ci gaba da yin imani ga “Allah marar-ganuwa”? (Kol. 1:15) Abu na farko shi ne mu san koyarwar da take hana mutane sanin gaskiya game da Jehobah. Bayan haka, wajibi ne mu koyi yadda za mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki a hanyar da ta dace don mu tabbatar wa mutane cewa waɗannan koyarwar suna “gāba da sanin Allah.”—2 Kor. 10:4, 5.

2, 3. Waɗanne koyarwar biyu ne suke hana mutane koyon gaskiya game da Allah?

2 Wata koyarwa da take hana mutane sanin gaskiya game da Allah ita ce ra’ayin bayyanau. Wannan koyarwar ba ta jitu da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba kuma tana sa mutane su yi rashin bege. Mutanen da suka yi imani da wannan koyarwar sun ce rai ya soma ne kawai farat ɗaya. Amma in da hakan gaskiya ce, to ba mu san abin da ya sa muke duniyar nan ba.

3 Wasu ’yan coci ba su fahimci Littafi Mai Tsarki sosai ba, a sakamako, sun ce bai daɗe da aka halicci sararin sama da duniya da kuma dukan halittun da ke cikinsu ba. Waɗanda suke wannan koyarwar suna iya daraja Littafi Mai Tsarki, amma sun ce Allah ya halicci kome cikin kwana shida na sa’o’i 24, wato kome da Allah ya halitta bai wuce aƙalla shekara dubu goma ba. Waɗannan mutanen sun ƙi da koyarwar kimiyya da ta saɓa wa ra’ayinsu. A sakamako, wannan koyarwar tana rage darajar Littafi Mai Tsarki kuma ta sa mutane su ga kamar akwai kurakurai a cikinsa. Waɗannan mutanen suna sa mu tuna da wasu a ƙarni na farko da suke da himmar bauta wa Allah, “amma ba da cikakken sani ba.” (Rom. 10:2) Ta yaya za mu iya yin amfani da Kalmar Allah don taimaka wa waɗannan mutanen su san cewa wannan koyarwa ‘mai ƙarfi’ na ra’ayin bayyanau ba gaskiya ba ce? Za mu iya taimaka musu idan mun yi ƙoƙari mu san ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

TABBACI DA DALILI NE KE SA MU KASANCE DA BANGASKIYA

4. Ya kamata imaninmu ya dangana ga me?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce mu daraja ilimi. (Mis. 10:14) Jehobah yana so imaninmu a gare shi ya dangana ga tabbaci da kuma dalili, ba ga tunani ko al’adun addinan ’yan Adam ba. (Karanta Ibraniyawa 11:1.) Idan muna so mu kasance da imani sosai ga Allah, wajibi ne mu gaskata cewa Jehobah ya wanzu. (Karanta Ibraniyawa 11:6.) Mun gaskata cewa Allah ya wanzu ba don ra’ayinmu ba, amma don muna da tabbaci da kuma dalilin yin hakan.

5. Wane dalili na farko ne ya kamata ya sa mu gaskata cewa Allah ya wanzu?

5 Manzo Bulus ya bayyana dalili na farko da ya sa ya kamata mu gaskata cewa Allah ya wanzu ko da ba za mu iya ganinsa ba. Ya ce: “Tun halittar duniya al’amura nasa da ba su ganuwa, watau ikonsa madawwami da allahntakarsa, a sarari ake ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su.” (Rom. 1:20) Ta yaya za ka iya taimaka wa wani da bai gaskata cewa Allah ya wanzu ba ya amince da abin da Bulus ya ce? Za ka iya yin amfani da wasu cikin waɗannan misalan don ka tabbatar musu cewa Mahalicci yana da iko da kuma hikima.

HALITTA TANA NUNA IKON ALLAH

6, 7. A waɗanne abubuwa biyu ne ake ganin ikon Jehobah a halitta?

6 Muna iya ganin alamar ikon Allah a abubuwa biyu da suke kāre mu. Wato, sarari da maganaɗisun duniya. Alal misali, sarari yana tanadar mana da iskar da muke shaƙa, kuma yana kāre mu. A wace hanya? Akwai wasu manya-manyan duwatsun da suke faɗowa daga sama, idan suka kai duniya, za su iya halaka abubuwa da dama. Hakan ba ya faruwa domin muddin sun isa sarari, suna narkewa. Bayan sun narke, suna zama wasu abubuwa masu haske kamar taurari da ke wucewa da gudu a sama daddare.

7 Maganaɗisun duniya kuma yana kāre mu. Akwai narkakken ƙarfe mai zafi a tsakiyar ƙasa. Wannan yana haifar da ƙarfin maganaɗisu da ke kewaye da mu kuma yake kai sarari. Wannan ƙarfi maganaɗisun yana kāre mu daga rana da kuma ƙunarta mai guba sosai. Kuma yana hana ƙunar ta halaka halittu masu rai a duniya. Maganaɗisun yana shanye gubar ko kuma ya komar da ita sarari. Babu shakka, Jehobah yana da iko sosai.—Karanta Ishaya 40:26.

HALITTA TANA BAYYANA HIKIMAR ALLAH

8, 9. Ta yaya aka ga hikimar Allah a tsarin iska da ke sa abubuwa masu rai su rayu?

8 Muna ganin hikimar Allah a wasu abubuwa da suke taimaka mana mu yi rayuwa a nan duniya. Ka yi tunanin wani birni mai ganuwa da miliyoyin mutane suke zama a ciki. Ba a iya shigar da ruwa mai tsabta birnin kuma ba a iya fitar da ruwa mai datti. Ba zai jima ba irin wannan birnin zai yi datti kuma mutane za su kasa zama a cikinsa. A wani bangare kuma, haka duniyarmu take. Da yake duniya wadda take kama da “birnin” ba ta da isashen ruwa a ciki, ba za mu iya wanke dukan dattin da ke ciki ba. Amma duk da haka, duniya tana iya tanadar wa dukan abubuwa masu rai abin da suke bukata don su rayu. Me ya sa? Domin duniya tana amfani da wata hanya mai ban al’ajabi na juya duk abin da ake bukata don abubuwa masu rai su iya rayuwa.

9 Bari mu yi la’akari da yadda duniya take tanadar da iska don abubuwa masu rai su shaƙa. Biliyoyin halittu suna shaƙar wannan iska mai kyau kuma su fitar da iskar ƙuna. Ko da yake ana yin hakan a ko da yaushe, ba a taɓa yin rashin iska mai kyau a duniya ba. Me ya sa? Domin shuke-shuke suna bukatar iskar ƙuna da ruwa da hasken rana da wasu sinadarai don su iya ba mu kuzari da kuma iskar shaƙa mai kyau. Sa’ad da muka shaƙa iska kuma muka fitar da iskar ƙuna, mun bi tsarin zagayar iska ke nan. Ana kiran wannan tsari na musamman photosynthesis. Hakika, Jehobah yana amfani da shuke-shuke da ya yi don ya ba “kowa rai, da numfashi.” (A. M. 17:25) An ga hikimar Allah sosai a nan, ko ba haka ba?

10, 11. Ta yaya muke ganin hikimar Allah a yadda Jehobah ya tsara malam buɗe littafi da kuma ɗan mazarin-iya?

10 Za mu iya ganin hikimar Allah ta yadda ya tsara wasu abubuwa masu rai da yawa a duniya. Wani bincike ya nuna cewa akwai abubuwa masu rai dabam-dabam aƙalla miliyan biyu zuwa ɗari a duniya. (Karanta Zabura 104:24.) Za mu koyi hikimar Allah a yadda ya tsara wasu cikin waɗannan abubuwa masu rai dabam-dabam.

11 Alal misali, akwai wani malam buɗe littafi da ke da ƙaramar ƙwaƙwalwar da girmanta bai wuce baƙin alƙalami ba. Duk da haka, wannan malam buɗe littafin yana iya gudun mil 1,800 (kusan kilomita 3,000) kuma rana ce take taimakon sa ya san inda zai je. Ta yaya zai iya yin hakan yayin da rana take tafiya? Jehobah ya halicci ƙaramar ƙwaƙwalwarsa a hanyar da zai iya sanin inda zai je ko da rana tana tafiya. Ka yi tunanin idon ɗan mazarin-iya. Ƙaramar ƙwaƙwalwar wannan halittar tana taimakonta ta fahimci abubuwa da dama da idanunta suka gani ko da ɗan motsi ne.

12, 13. Mene ne ya burge ka a yadda Jehobah ya halicci ƙwayoyin halitta na jikinmu?

12 Yadda Jehobah ya tsara ƙwayoyin halittar abubuwa masu rai abin ban al’ajabi ne. Alal misali, jikinmu yana ɗauke da ƙwayoyin halitta wajen tiriliyan ɗari. Akwai wani abu a cikin kowanne ƙwayoyin halitta da ake kira matattarin sanin asalin halitta, wato DNA. Wannan matattarin sanin asalin halitta yana ɗauke da yawancin abubuwan da suke taimakawa wajen gina jikinmu.

13 Yaya yawan bayanin da ke DNA? Bari mu kwatanta yawan bayanan da ƙaramin cokali cike da busashen DNA zai iya ɗauka da faifan CD. Za a iya saka dukan bayanan da ke ƙamus a cikin faifan CD guda, kuma wannan abin mamaki ne domin faifan CD bai da girma. Amma, ƙaramin cokali ɗaya da aka cika da DNA zai iya ɗaukan bayanan da ya cika faifan CD guda tiriliyan biyar!

14. Mene ne abin da masana suka gano yake tabbatar maka game da Jehobah?

14 Sarki Dauda ya ce kamar Jehobah ya rubuta bayanin da ake bukata don gina jikin ’yan Adam a cikin littafi. Da yake magana game da Jehobah, Dauda ya ce: “Idanunka sun ga gaɓaɓuwan jikina tun ba su cika ba, a cikin littafinka an rubuta dukansu, waɗanda a ke sifantarsu yau da gobe, tun ba ko ɗaya a cikinsu ba.” (Zab. 139:16) Hakika, sa’ad da Dauda ya yi tunani a kan yadda aka halicci jikinsa, sai hakan ya motsa shi ya yabi Jehobah. Masanan kimiyya sun gano wasu abubuwa da yawa masu ban al’ajabi game da jikinmu. Wannan abin da suka gano ya sa mun amince da abin da marubucin zabura ya ce game da Jehobah: “Zan yi godiya gareka; gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa: ayyukanka suna da ban al’ajabi; wannan ma raina ya sani sarai.” (Zab. 139:14) Hakika, abubuwan da Allah ya halitta da muke gani suna tabbatar mana cewa akwai Allah, ko ba haka ba?

KA TAIMAKI MUTANE SU GIRMAMA ALLAH MAƊAUKAKI

15, 16. (a) Ta yaya littattafanmu suke taimaka mana mu nuna godiya ga ikon halittar da Jehobah yake da shi? (b) Wane talifi ne ya fi burge ka?

15 A cikin shekaru da yawa yanzu, littattafan da Shaidun Jehobah suka wallafa suna taimaka wa mutane su koyi game da Allah daga halittunsa. Alal misali, an wallafa wasu littattafan musamman don taimaka wa mutanen da suka yi imani da koyarwa bayyanau da wasu koyarwar ƙarya. Wata ’yar’uwa ta rubuta wasiƙa zuwa ofishin reshe da ke ƙasar Amirka game da wasu cikin waɗannan littattafan. Ta ce: “Mun yi nasara a kamfen ɗin wannan mujallar. Har wata mata mai koyar da ilimin halittu ta karɓi kofi 20 don ta rarrabawa ɗalibanta.” Wani ɗan’uwa ya rubuta: “Na soma yin wa’azi a tsakanin shekara ta 1946 zuwa 1949 kuma yanzu na kusan shekara 75, amma ban taɓa jin daɗin yin wa’azi kamar yadda na ji sa’ad da nake kamfen da wannan mujallar a watan nan ba.”

16 A kwanan nan, muna da littattafai da yawa da suke ɗauke da wasu talifofi da suka tattauna game da halitta. Waɗannan talifofin sun mai da hankali ga yadda halittun Allah suke da ban mamaki da kuma yadda ’yan Adam suke ƙoƙari su yi koyi da Mahalicci ta abubuwan da suke ƙerawa. An wallafa waɗannan talifofin ne don su taimaka mana mu nuna godiya ga ikon halittar da Jehobah yake da shi. Tambayoyin da suke cikin waɗannan talifofin suna taimaka wa mai karatu ya yi bimbini a kan abubuwan da ya karanta. Shin kana yin amfani da wasu cikin abubuwan da ka karanta a waɗannan talifofin don ka yi wa’azi gida-gida da a fili da kuma sa’ad da ka sami zarafin yin haka?

17, 18. (a) Wace nawaya ce iyaye suke da ita? (b) Yaya kuka yi amfani da wasu talifofin da suka tattauna batun halitta a bautarku ta iyali?

17 Iyaye, shin kuna tattauna waɗannan talifofin da yaranku sa’ad da kuke bauta ta iyali kuwa? Idan kuna yin hakan, za ku taimaka wa yaranku su ba da gaskiya ga Allah. Wataƙila kuna da matasa da suke makarantar gaba da sakandare. Akwai malamai da yawa da suke ƙoƙari su rinjaye su da ƙarya cewa babu Mahalicci. Masanan kimiyya da malaman makaranta da shirye-shiryen talabijin suna koyar da ra’ayin bayyanau. Za ku iya taimaka wa yaranku su yi amfani da wasu talifofin da suka tattauna hakan a littattafanmu don su iya tabbatar wa mutane cewa akwai Mahalicci. Waɗannan littattafan suna ƙarfafa matasa su kasance da fahimi. (Mis. 2:10, 11) Hakan yana taimaka musu su san ko abin da aka koya musu a makaranta gaskiya ne.

18 A wasu lokatai, matasa sukan sami labari cewa wasu masanan kimiyya sun gano wasu ƙasusuwa da suka tabbatar da koyarwar ra’ayin bayyanau. Ko kuma su ji labari cewa masana sun halicci rai a ɗakin gwaji. An rubuta talifofi a littattafanmu da suka tattauna wannan batun don su taimaka wa ɗalibai su yanke shawara ko hakan gaskiya ne. Iyaye, ku yi amfani da waɗannan talifofin don taimaka wa yaranku su kasance da gaba gaɗi sa’ad da suke tattauna da mutane dalilin da ya sa suka yi imani da Mahalicci.—Karanta 1 Bitrus 3:15.

19. Wane gata ne dukanmu muke da shi?

19 Za mu koyi abubuwa da yawa game da halayen Allah masu kyau idan muka karanta talifofin da suka tattauna batun halitta a littattafan da ƙungiyarmu ta wallafa. Dukan waɗannan tabbaci da muka samu suna sa mu yabi Jehobah daga zuciyarmu. (Zab. 19:1, 2) Muna da gatan girmama Jehobah da yaba masa don shi ne ya halicci dukan abubuwa.—1 Tim. 1:17.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba