DAGA TARIHINMU
Sun Yi Tsayin Daka a ‘Lokacin Gwaji’
YAƘIN DUNIYA na Ɗaya da ya ɓarke a shekara ta 1914, ya sa aka san cewa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba sa saka hannu a yaƙi. (Isha. 2:2-4; Yoh. 18:36; Afis. 6:12) Mene ne bayin Allah da ke ƙasar Biritaniya suka yi?
A shekara ta 1916, an kafa doka a ƙasar Biritaniya cewa duk namijin da bai yi aure ba kuma yana tsakanin shekara 18 zuwa 40 ya shiga soja. Amma, dokar ta ƙyale waɗanda suka ƙi yin hakan saboda addini ko kuma imaninsu. Gwamnati ta zaɓi rukuni da za su riƙa ba da wannan ’yancin ga waɗanda suke ganin sun cancanta.
Kafin a ce kwabo, an saka Ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda 40 a fursunan soja, kuma an tilasta wa guda 8 su je bakin daga a ƙasar Faransa. Wannan rashin adalcin ya sa ’yan’uwa da ke Biritaniya suka rubuta wasiƙa zuwa ga Firam Minista Herbert Asquith. Wasiƙar tana ɗauke da takardar da mutane dubu biyar da ɗari biyar suka sa hannu, don nuna rashin yarda da lamarin.
Sai aka samu labari cewa za a harbi ’yan’uwa takwas da aka kai Faransa don sun ƙi su yi yaƙi. Amma, a daidai lokacin da ake son a yi hakan, sai aka canja hukuncinsu zuwa ɗaurin shekara goma. An tura su fursuna na ’yan farin hula da ke ƙasar Ingila.
Sa’ad da yaƙi ya yi tsanani, sai dokar ta shafi maza da suke da aure. Ɗan’uwa Henry Hudson wanda likita ne ya kāre kansa a kotun da ke birnin Manchester a ƙasar Ingila. Amma, a ranar 3 ga Agusta 1916, kotun ya hukunta cewa yana da laifin ƙin halartar shari’ar. An ci masa tara kuma aka bar shi a hannun soja. Sai aka yi wani shari’a a birnin Edinburgh, a ƙasar Scotland, kuma aka ce wani majagaba James Frederick Scott, wanda ɗan shekara 25 ne bai yi laifi ba. Kotun Crown ya kai ƙara ga kotu na gaba, amma shari’ar bai yiwu ba. Me ya sa? Domin a lokacin ne ake wa ɗan’uwa Herbert Kipps shari’a, kuma an kama shi da laifi. Sai aka ci masa tara, kuma aka bar shi a hannun soja.
A watan Satumba na 1916, ’yan’uwa 264 ne suka rubuta wasiƙa don neman ’yanci daga aikin soja. An ba ’yan’uwa 5 cikinsu ’yanci, an sanya 154 su riƙa “gyaran hanyoyi da tonon ma’adinai da dai sauransu.” An kuma tura ’yan’uwa 23 su riƙa yin ayyukan sojoji da ba su ƙunshi yaƙi ba. An bar 82 cikinsu a hannun sojoji, sai suka yi musu shari’a kuma suka saka wasu a fursuna don sun ƙi bin umurnin soja. Gwamnati ta mai da ’yan’uwanmu fursunan ’yan farin hula don mutane da yawa ba su amince da yadda aka wulakanta su a fursunan soja ba.
Edgar Clay da Pryce Hughes, waɗanda suka zama masu kula da reshe a Biritaniya sun yi aiki a dam da ke birnin Wales. Herbert Senior yana cikin mutane takwas waɗanda suka dawo daga Faransa, kuma an tura shi fursunan da ke birnin Wakefield a jihar Yorkshire. Wasu kuma sun yi aiki a cikin yanayi mai wuya a fursuna da ke yankin Dartmoor. Sun zama rukuni mafi girma na waɗanda suka ƙi yin yaƙi.
Ɗan’uwa Frank Platt ya yarda ya yi ayyukan soja da ba su ƙunshi yaƙi ba, amma an gana masa azaba sosai sa’ad da aka tura shi bakin dāga. Atkinson Padgett ya zama ɗan’uwa jim kaɗan bayan ya shiga soja, kuma hukumar sojoji sun gana masa azaba sosai don ya ƙi yin yaƙi.
A wannan lokacin, wataƙila ’yan’uwanmu ba su da cikakken fahimi na dalilin da ya sa suka yi ba-ruwanmu da yaƙi ba, amma sun yi niyyar su faranta wa Jehobah rai. Waɗanda aka ambata sunayensu a wannan rahoton sun kafa misali mai kyau na yin ba-ruwanmu da sha’anin yaƙi, musamman ma a ‘lokacin gwaji.’ (R. Yoh. 3:10, Littafi Mai Tsarki)—Daga tarihinmu a Biritaniya.