Abin Da Ke Ciki
15 Ga Mayu, 2013
© 2013 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.
NA NAZARI
1-7 GA YULI, 2013
Ka Yi Aikin da Aka Ba Ka na Mai-bishara
SHAFI NA 3 • WAƘOƘI: 103, 102
8-14 GA YULI, 2013
Kana da ‘Himman Yin Nagargarun Ayyuka’?
SHAFI NA 8 • WAƘOƘI: 108, 93
15-21 GA YULI, 2013
Ku Ƙarfafa Aurenku ta Wajen Tattaunawa Sosai
SHAFI NA 14 • WAƘOƘI: 36, 87
22-28 GA YULI, 2013
Iyaye da Yara, Ku Tattauna Cikin Ƙauna
SHAFI NA 19 • WAƘOƘI: 88, 3
29 GA YULI, 2013–4 GA AGUSTA, 2013
Ka Kiyaye Gādonka ta Wajen Yin Zaɓi Mai Kyau
SHAFI NA 26 • WAƘOƘI: 14, 134
TALIFOFIN NAZARI
▪ Ka Yi Aikin da Aka Ba Ka na Mai-bishara
Mene ne zama mai bishara yake nufi? Wannan talifin ya amsa tambayar kuma ya nuna dalilin da ya sa mutane suke bukatar bishara. Ya kuma bayyana yadda za mu cim ma aikinmu a matsayin masu bishara.
▪ Kana da ‘Himman Yin Nagargarun Ayyuka’?
Wannan talifin ya tattauna hanyoyi biyu da yin “nagargarun ayyuka” zai sa mutane su soma bauta wa Allah. (Tit. 2:14) Hanya ɗaya ita ce ta yin wa’azi. Ta biyu kuma ita ce halayenmu masu kyau.
▪ Ku Ƙarfafa Aurenku ta Wajen Tattaunawa Sosai
▪ Iyaye da Yara, Ku Tattauna Cikin Ƙauna
Idan ma’aurata suna son su kasance da farin ciki kuma su ji daɗin zamansu tare a matsayin iyali, yana da muhimmaci su riƙa tattaunawa da juna. Talifi na farko ya bayyana halayen da za su taimaka mana mu riƙa tattaunawa da iyalinmu da kyau. Talifi na biyu kuma ya nuna abin da ya kamata mu yi don mu shawo kan abubuwan da suke hana tattaunawa tsakanin iyaye da yara.
▪ Ka Kiyaye Gādonka ta Wajen Yin Zaɓi Mai Kyau
Wane gādo ne muke da shi a matsayin Kiristoci? Mene ne za mu koya daga misalin Isuwa game da gādonmu? Waɗanne matakai za su taimaka mana mu yi zaɓin da suka dace game da gādonmu? Wannan talifin ya amsa waɗannan tambayoyin..
A FITOWAR NAN
13 Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
24 Abin da Ya Sa Rayuwarmu Take da Ma’ana Sosai
BANGO: Wasu ’yan’uwa mata a arewancin Landan, suna wa wani mai shago wa’azi da mujallun yaren Gujarati
LANDAN, INGILA