Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/1 pp. 12-15
  • Matsalolin da Iyalan Rana Suke Fuskanta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matsalolin da Iyalan Rana Suke Fuskanta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • SHAWARA GA IYAYE
  • SHAWARA GA MATA IYAYEN RANA
  • SHAWARA DON KYAUTATA DANGANTAKA TSAKANIN IYAYE DA IYAYEN RANA
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/1 pp. 12-15

ABUBUWAN DA KE KAWO FARIN CIKI A IYALI

Matsalolin da Iyalan Rana Suke Fuskanta

MARGARET,a WATA MAHAIFIYAR RANA A OSTARELIYA: “Tsohuwar matar mijina ta faɗa wa yaranta cewa kada su riƙa jin maganata, ko da ɗan shawara ce kamar ‘Ku goge haƙoranku.’” A ra’ayin Margaret, hakan ya haifar da matsaloli a gidan sabon mijinta.

Iyalan rana suna fuskantar ƙalubale sosai a dangantakarsu da iyalinsu na farko.b Ya zama wajibi wa yawancin matac iyayen rana su yi hulɗa da mahaifiyar yaran maigidansu a batutuwan ziyara, ba da horo, da kuma kuɗi don biyan bukatun yaran. Alal misali, idan wani ya sake aure, abokai da dangi ba sa saurin amincewa da macen da aka auro zuwa cikin iyalinsu. Bari ku yi la’akari da yadda shawarar Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa iyalinku su shawo kan waɗannan matsalolin.

DANGANTAKA TA 1: SHA’ANI DA MAHAIFIYAR YARAN MAIGIDA

Wata mahaifiyar rana a ƙasar Namibia mai suna Judith ta ce: “Mahaifiyar yaran maigidana, wato, matarsa ta dā ta taɓa gaya wa yaranta cewa ni sabuwar matar babansu ne kawai kuma yarana ba za su taɓa zama ƙannen su ba. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai don ina ƙaunar yaranta kamar nawa.”

Masana sun amince cewa hulɗa tsakanin iyayen rana da ainihin iyayen yara bai da sauƙi kuma zai iya jawo rashin jituwa a cikin iyali. A yawancin lokaci, ana samun saɓani tsakanin ainihin mahaifiyar yaran da mahaifiyar rana. Mene ne zai iya taimaka musu?

Abin da zai sa ku yi nasara: Ku kafa dokokin da suka dace. Idan maigida yana hana matarsa ta dā, wato, mahaifiyar yaransa, hulɗa da yaran, hakan zai jefa yaran cikin wani irin hali.d Iyayen yaro, wato, waɗanda suka ‘haife shi’ suna da tasiri sosai a rayuwarsa. (Misalai 23:22, 25) A wani ɓangaren kuma, idan maigidan yana yawan tuntuɓar matarsa ta dā a kan batutuwan da suka shafi iyalinsa, hakan zai ɓata ran matar da yake tare ita yanzu. Saboda haka, ya kamata maigida ya kasance da basira wajen kafa dokokin da suka dace don kāre aurensa daga haɗari yayin da yake ba wa matarsa ta dā haɗin kan da bai wuce ƙa’ida ba.

SHAWARA GA IYAYE

  • Sa’ad da kuke tattaunawa da matarku ta dā, ku mai da hankali a kan batutuwan da suka shafi yaran a maimakon yin magana game da wasu abubuwa. Alal misali, za ku iya ce idan zai yiwu ku shirya lokaci da rana don yin magana ta waya. Hakan zai fi dacewa maimakon ku riƙa kiran juna ta waya ba zato ba tsammani ko kuma da daddare sosai.

  • Idan yaranku suna zama tare da matarku ta dā ne, wato, mahaifiyarsu, za ku iya yin magana da su a kai a kai ta waya ko ta aika musu wasiƙu ko kuma imel. (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Wasu ma suna magana da juna ta wani tsarin na’urar sadarwa da ke nuna hoton mutum da ake kira videoconferencing. Idan kuna magana da yaranku a kai a kai, za ku gane halayen yaranku duk da cewa ba sa tare da ku kuma hakan zai sa ku iya taimaka musu idan bukata ta kama.

SHAWARA GA MATA IYAYEN RANA

  • Ku nuna ƙauna ga mahaifiyar yaran maigida ta wajen gudun yin abubuwan da zai nuna kamar kuna ƙoƙarin ƙwace matsayinta ne. (1 Bitrus 3:8) Idan ku ne masu rainon yaranta, ku riƙa gaya mata abubuwan da yaran suke yi, musamman ma abubuwa masu kyau. (Misalai 16:24) Ku nemi shawararta kuma idan ta bayar, ku gode mata.

  • Kada ku riƙa yawan wasa da yaran a gaban mahaifiyarsu. Wata mahaifiyar rana a ƙasar Amirka mai suna Beverly ta ce: “Yaran maigidana sun ce za su riƙa kirana Mama. Muka amince cewa hakan yana da kyau sa’ad da muke cikin gida, amma kada su kira ni Mama a gaban mahaifiyarsu Jane, ko kuma a gaban iyalinta. Hakan ya ƙara kyautata dangantakata da mahaifiyarsu Jane. Har ma daga baya, ni da ita muka haɗa kai wajen taimaka wa yaran a wasannin makaranta da kuma yawon buɗe ido.”

SHAWARA DON KYAUTATA DANGANTAKA TSAKANIN IYAYE DA IYAYEN RANA

  • Kada ku yi baƙar magana a gaban yaran a kan mahaifiyarsu. Yana da sauƙi mutum ya soma irin wannan baƙar magana, amma hakan zai sa yaran baƙin ciki sosai. Ƙari ga haka, ba za ku san lokaci da kuma yadda za a maimaita maganar da kuka yi ba. (Mai-Wa’azi 10:20) Idan yaronku ya gaya muku cewa mahaifiyarsa ta yi baƙar magana a kan ku, ku mai da hankali ga yanayin yaron. Za ku iya ce: “Ban ji daɗi cewa an yi wannan maganar a gabanka ba. Mahaifiyarka tana fushi da ni, kuma a wani lokaci, mutane sukan yi baƙar magana idan ransu ya ɓace.”

  • Ku yi ƙoƙari ku bi tsarin da kuka kafa a iyalinku da kuma a yadda kuke hulɗa da mahaifiyar yaran. Idan hakan ba zai yiwu ba, ku bayyana ra’ayinku ga mahaifiyar yaran cikin ladabi. Ka yi la’akari da tattaunawar da ke gaba:

    Mahaifiyar rana: Tim, don Allah, ka je ka kwashe kwanukan da ka ci abinci da su.

    Tim: A gidan Mamarmu, ita take kwashe mana kwanuka kuma ta kai kicin.

    Mahaifiyar rana (da fushi): Ai tana ɓata ku ne kawai.

    Wataƙila wannan amsar da ke gaba zai fi tasiri:

    Mahafiyar rana (cikin natsuwa): To na ji. A nan, mu muke kwashe kwanukan da kanmu.

  • Ku guji shirya wani abin yi a lokacin da ya kamata su tattauna da mahaifiyarsu ko kuma su kai mata ziyara. (Matta 7:12) Idan akwai wani abin da za ku yi a wannan lokacin kuma ba za ku iya tura zuwa gaba ba, ku nemi izinin mahaifiyarsu kafin ku gaya wa yaran game da abin.

KU GWADA WANNAN: Ku ɗauki waɗannan matakan da ke gaba sa’ad da kuka haɗu da mahaifiyar yaran maigida:

  1. Ku haɗa ido ta ita kuma ku yi murmushi. Ku guji yin tsaki, kallon raini ko kuma ɗaure fuska.

  2. Ku nuna ladabi sa’ad da kuke gai da ita. Alal misali, za ku iya ce, “Ina kwana Maman wane” (ku ambaci sunan ɗanta).

  3. Idan kuna cikin taɗi a cikin jama’a, kada ku yi banza da ita.

DANGANTAKA TA 2: SHA’ANI DA ’YA’YA DA SUKA MANYANTA

An yi ƙaulin wata mata a cikin wani littafi mai suna Step Wars, tana bayyana yadda maigidanta yake goyon bayan ’ya’yansa da suka manyanta kuma ba ya bi da ita cikin ladabi. Matar ta ce: “Wannan yanayin yana ɓata mini rai sosai.” Waɗanne matakai ne za ku ɗauka don kada yadda kuke hulɗa da yaran maigida da suka manyanta ya ɓata aurenku?

Abin da zai sa ku yi nasara: Ku nuna cewa kun damu da su. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kada kowa shi biɗa ma kansa, amma abin da zai amfani maƙwabcinsa.’ (1 Korintiyawa 10:24) Ku yi ƙoƙari ku fahimci yanayin mutumin. Wataƙila, yaran maigida da suka manyanta suna gudun wani yanayin da zai ɓata ran mahaifiyarsu ne. Ko kuma suna ganin cewa idan suka amince da matar mahaifinsu, tamkar sun ci amanar mahaifiyarsu. A wani ɓangaren kuma, iyaye za su ga kamar idan suka yi wa yaran faɗa, yaran za su guje su.

Ku kyautata zumuncin da ke tsakanin ku da yaran maigida a hankali maimakon ku riƙa matsa musu. A zahiri, tilasta abokantaka tsakaninku ba zai yi tasiri ba. (Waƙar Waƙoƙi 8:4) Ku riƙa nuna haƙuri da kuma sanin yakamata don kyautata zumunci tsakaninku da ’ya’yan maigida.

Ba a kowane lokaci ba ne za ku riƙa bayyana ra’ayinku game da abubuwa, ko da an ɓata muku rai ne. (Misalai 29:11) Sa’ad da wata matsala ta tashi kuma ba za ku iya kame kanku ba, ku yi addu’a kamar yadda Sarki Dauda ya yi, sa’ad da ya ce: “Ka sa tsaro a bakina, ya Ubangiji: Ka tsare ƙofar leɓunana.”—Zabura 141:3.

Idan kuna zama ne a gidan da aka yi rainon yaran, kada ku yi mamaki cewa yaran ba za su so waɗansu canje-canje da za ku yi a gidan ba. Saboda haka, kada ka yi canje-canje ya wuce gona da iri, musamman ma a ɗakunan da suka zauna a ciki tun suna ƙanana. A wani yanayi ma, za ku iya yanke shawarar ƙaura zuwa wani gida dabam.

KU GWADA WANNAN: Idan yaran maigida da suka manyanta suna yi muku rashin kunya ko kuma ba sa girmama ku, ku bayyana ra’ayinku wa maigida kuma ku kasa kunne ku saurari abin da zai faɗa. Kada ku matsa masa ya yi wa yaran horo. A maimakon haka, ku yi ƙoƙari ku fahimci juna da maigida. Muddin tunaninku “ya zama ɗaya,” za ku haɗa kai don ku inganta yanayin.—2 Korintiyawa 13:11.

DANGANTAKA TA 3: SHA’ANI DA SAURAN DANGI DA KUMA ABOKAI

Wata mahaifiyar rana a ƙasar Kyanada mai suna Marion ta ce: “Iyayena sukan ba wa ɗan da na haifa kyautai amma ba sa ba wa yaran maigidana. Muna ƙoƙarin ba wa sauran yaran kyauta a duk lokacin da hakan ya faru, amma a wasu lokuta, yana fin ƙarfinmu.”

Abin da zai sa ku yi nasara: Ku saka bukatun iyalinku na yanzu kan gaba. Ku gaya wa danginku da abokanku cewa iyalinku na yanzu yana da muhimmanci a wajenku. (1 Timotawus 5:8) Gaskiya ne cewa ba zai dace ku ɗauka cewa dangi da abokai za su ƙaunace ’yan iyalinku na yanzu nan da nan ba, za ku iya gaya musu su nuna ladabi da kuma adalci a sha’aninsu da iyalinku na yanzu. Ku bayyana yadda yaran suke ji sa’ad da aka yi watsi da su ko kuma aka ƙi yi musu alheri.

Ku yi ƙoƙarin tabbata cewa akwai zumunci tsakanin iyayen matarku na dā da yaranku. Wata mahaifiya a ƙasar Ingila mai suna Susan ta bayyana cewa: “Shekara ɗaya da rabi bayan mutuwar maigidana, na sake yin aure, iyayensa ba su karɓi sabon mijina da hannu bibiyu ba. Amma sa’ad da muka riƙa tuna da su a al’amuranmu kuma muka sa yaran su riƙa musu waya suna nuna godiya saboda goyon bayansu, hakan ya kyautata zumuncin da ke tsakaninmu.”

KU GWADA WANNAN: Ku yi tunanin wani abokinku ko kuma danginku wanda sha’ani da shi yana da wuya sosai kuma ku tattauna da maigida yadda za ku inganta dangantakarku da wannan aboki ko dangi.

Waɗanda suka sake yin aure sukan sami matsala a dangantakarsu da dangi da kuma abokai. Amma bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai iya sa iyalinsu ta sami albarka da aka ambata a Misalai cewa: “Ta wurin hikima a ke ginin gida: Ta wurin fahimi kuma ake kafa shi.”—Misalai. 24:3.

a An canja wasu sunaye.

b Don samun ƙarin bayani a kan yadda za ku shawo kan wasu matsalolin da suka shafi sake yin aure, ku duba jerin talifofin nan, “Secrets of Successful Stepfamilies,” da ke mujallar Awake! na Afrilu 2012 a Turanci, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

c A wannan talifin, an mai da hankali a kan mata saboda sauƙin fahimta, amma ƙa’idodin sun shafi maza har ila.

d Idan matarka ta dā tana yi wa iyalinka barazana, zai dace ka ɗauki mataki don kāre iyalinka.

KU TAMBAYI KANKU . . .

  • Ta yaya zan kyautata dangantakata da mahaifiyar yaran mijina, wato, matarsa ta dā?

  • Ta yaya za mu taimaka wa dangi da abokai don kada su ɓata zumuncin da ke iyalinmu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba