Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 2/15 pp. 22-24
  • Ka Yi Hattara da Nufe-Nufen Zuciyarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Hattara da Nufe-Nufen Zuciyarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TA YAYA ZA KA SAN NUFE-NUFEN ZUCIYARKA?
  • TA YAYA ZUCIYARKA ZA TA IYA YAUDARARKA?
  • ZAI YIWU MU YI GYARA KUWA?
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehobah Da Zuciya Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Samu Zuciya Da Jehovah Yake So
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Kiyaye Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kana Da “Zuciya Wadda Za Ta San” Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 2/15 pp. 22-24

Ka Yi Hattara da Nufe-Nufen Zuciyarka

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya ta fi komi rikici, cuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya.” (Irm. 17:9) Idan zuciyarmu tana sha’awar wani abu sosai, za mu iya neman hujjar yin abin da take so.

Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, alfasha.” (Mat. 15:19) Zuciyarmu za ta iya ruɗan mu kuma ta sa mu yi abin da ya saɓa wa nufin Allah. Kuma wataƙila sai bayan mun yi wani laifi ne za mu ankara cewa mun yi kuskure. Kafin mu yi laifi, mai zai taimaka mana mu san nufe-nufen zuciyarmu?

TA YAYA ZA KA SAN NUFE-NUFEN ZUCIYARKA?

Ka karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma ka yi bimbini.

Manzo Bulus ya ce: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa mararrabar rai da ruhu.” Kalmar Allah “tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibran. 4:12) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki da bimbini, za su taimaka mana mu san nufe-nufen zuciyarmu. Saboda haka, yana da muhimmanci mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma muna bimbini a kan abin da ya ce, kuma hakan zai sa mu kasance da ra’ayin Jehobah.

Idan muka yi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, zai koyar da lamirinmu. Lamirinmu yana nan kamar murya, domin zai iya gaya mana abin da bai da kyau kuma zai sa mu guje wa yin laifi. (Rom. 9:1) Akwai misalai da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da za su iya zama “gargaɗi garemu.” (1 Kor. 10:11) Idan muka yi koyi da waɗannan misalan, za mu guji tsai da shawarar da ba ta dace ba. Me ya kamata kowannenmu ya yi?

Ka roƙe Allah ya sa ka san nufe-nufen zuciyarka.

Jehobah mai “auna zukata” ne. (1 Laba. 29:17) Kuma “ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka.” (1 Yoh. 3:20) Ba za mu iya ruɗan Jehobah ba. Idan muka gaya masa matsalolinmu da yadda muke ji da kuma ra’ayinmu a cikin addu’armu, zai taimaka mana mu san nufe-nufen zuciyarmu. Za mu kuma iya roƙe Allah ya ba mu “zuciya mai-tsabta.” (Zab. 51:10) Addu’a kuwa tana da muhimmanci don sanin nufe-nufen zuciyarmu.

Ka riƙa saurarawa sosai a taro.

Idan muna sauraron jawabin da ake gabatarwa a taronmu, zai taimaka mana mu san nufe-nufen zuciyarmu. Ba a kowane taro ba ne muke koyon sabon abu. Amma, idan muna halarta a kai a kai, za mu fahimci ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki da kuma tunasarwa masu amfani da za su taimaka mana mu san nufe-nufen zuciyarmu. Furucin da ’yan’uwanmu suke yi a taro zai taimake mu sosai. (Mis. 27:17) Za mu raunana idan ba ma halartar taro kullum. Kuma hakan zai sa mu riƙa biɗan ‘muradin kanmu.’ (Mis. 18:1) Saboda haka, zai dace mu tambayi kanmu, ‘Ina halarta da kuma saurara a dukan taro kuwa?’—Ibran. 10:24, 25.

TA YAYA ZUCIYARKA ZA TA IYA YAUDARARKA?

Zuciyarmu za ta iya yaudarar mu a hanyoyi da yawa. Bari mu tattauna hanyoyi huɗu da hakan zai iya faruwa. Biɗan abin duniya da shan barasa da abokanmu da kuma irin nishaɗin da muke yi.

Biɗan abin duniya.

Babu bil Adama da ba ya bukatar abinci da tufafi da kuma wurin kwana. Yin sha’awar waɗannan abubuwan ba laifi ba ne. Amma, Yesu ya ja mana kunne cewa kada mu saka waɗannan abubuwan kan gaba a rayuwarmu. Ya ba da kwatancin wani mawadaci da ya cika rumbunansa da hatsi. Domin hakan, bai samu wurin ajiye amfanin gonarsa na baɗi ba. Saboda haka, ya so ya faɗaɗa rumbunansa. Sai ya ce wa kansa: “Nan zan ajiye hatsina da wadata duka. In ce wa raina kuma, Ya raina, kana da wadata mai-yawa a ajiye da za ta kai shekaru dayawa; yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annishuwa.” Amma, akwai wani muhimman abu da wannan mawadacin bai tuna ba. Zai iya mutuwa a daren ranar, kuma duk aikinsa ya zama banza.—Luk 12:16-20.

Hakan ma zai iya faruwa da mu. Sa’ad da muka soma manyanta, za mu iya soma alhini a kan samun isassun kuɗi da za mu kashe sa’ad da muka tsufa. Hakan zai iya sa mu soma neman kuɗi ƙarfi da yaji kuma mu riƙa fasa halartar taro da yin wa’azi da kuma wasu ayyuka na ikilisiya a kai a kai. Ko kuma wataƙila mu matasa ne kuma mun san cewa hidimar majagaba ce sana’a mafi kyau. Amma, muna iya yin tunani cewa zai fi kyau mu fara yin aiki kuma mu tara kuɗi sosai kafin mu soma hidimar majagaba. Shin kana da irin ra’ayin nan kuwa? Kada ka manta cewa yanzu ne lokaci mafi kyau da za ka yi iya ƙoƙarinka a hidimar Allah. Babu kowannenmu da ya san ko zai mutu gobe.

Shan barasa.

Misalai 23:20 ya ce: “Kada ka kasance kana cikin masu-shayeshaye.” Idan mutum yana son barasa sosai, zai iya riƙa sha kullum kuma ya riƙa ba da hujja. Zai iya cewa: ‘Ina shan giya ne kawai don zuciyata ta kwanta, ba don na bugu ba.’ Idan sai ka sha giya ne zuciyarka take kwantawa, to lallai ka binciki kanka. Kada ka ƙyale zuciyarka ta yaudare ka.

Abokanmu.

A kowace rana, muna kasancewa tare da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah. Hakan zai iya faruwa a makaranta ko a wajen aiki ko kuma sa’ad da muke wa’azi. Amma, ba zai dace mu riƙa kasancewa tare da su ba kullum ko kuma su zama abokanmu ba. Shin muna neman hujjar yin abokantaka da su ta wajen cewa suna da halaye masu kyau? Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Kor. 15:33) Idan ruwan kwata ya ɗan ɗiga cikin ruwa mai tsabta, zai ɓata ruwan baki ɗaya. Hakan ma yake idan muna abokantaka da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah. Da sannu-sannu, za mu iya soma yin tunani da ado da magana kamar su.

Irin nishaɗin da muke yi.

Fasaha tana sa ya kasance da sauƙi a samu nishaɗi iri-iri. Amma, yawancinsu ba su dace da Kirista ba. Manzo Bulus ya ce: Kada a ambata “fasikanci, da dukan ƙazanta, ko sha’awa” a cikinku. (Afis. 5:3) Idan muna sha’awar kallo ko kuma jin abu mai ƙazanta fa? Za mu iya ba da hujja cewa kowa yana bukatar ɗan shaƙatawa, kuma mutum ne zai zaɓi yadda zai shaƙata. Ya dace mu riƙa bin gargaɗin Bulus, kuma kada mu kalla ko saurari kowane irin abu mai ƙazanta.

ZAI YIWU MU YI GYARA KUWA?

Ko da zuciyarmu ta yaudare mu kuma mun nemi hujja don laifin da muka yi, ba mu wuce yin gyara ba. (Afis. 4:22-24) Ka yi la’akari da misalai biyu.

Miguela ya daidaita ra’ayinsa game da abin duniya. Ya ce: “A ƙasarmu, mutane suna ɗaukan samun na’ura mafi kyau da kuma wanda ake yayinsa da muhimmanci sosai. Saboda haka, akwai wani lokaci da na soma sayan kusan dukan abin da ake yayinsa. Ina tunani cewa ba zan zama mai son abin duniya ba. Amma daga baya, na san cewa ina yaudarar kaina ne kawai. Sai na yi addu’a ga Jehobah game da ra’ayina da kuma nufe-nufen zuciyata. Na gaya masa cewa muna son mu bauta masa da dukan zuciyarmu a matsayin iyali. Sai muka yanke shawara cewa za mu sauƙaƙa salon rayuwarmu kuma za mu ƙaura zuwa inda ake bukatar masu wa’azi sosai. Ba da daɗewa ba, muka soma hidimar majagaba. Mun fahimci cewa ba ma bukatar mu tara abin mallaka kafin mu yi farin ciki.”

Misalin wani mai suna Lee ya nuna yadda bincike kansa sosai ya taimaka masa ya yi watsi da mugun tarayya. Ya ce: “Ina yawan cuɗanya da baƙi daga wasu ƙasashe saboda yanayin aikina. Ina jin daɗin halartar wannan taron, duk da yake na san cewa za a yi maye a wurin. Na kusan buguwa sau da yawa, amma bayan hakan, na yi da-na-sani. Sai na bincike kaina sosai. Abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da shawarar da dattawa suka ba ni, sun taimaka mini na san cewa ina tarayya da mutanen da ba sa ƙaunar Jehobah. Yanzu, na rage yawan haɗuwa da waɗannan mutanen kuma ina yawan tattauna batun kasuwanci ta tarho.”

Muna bukatar mu faɗa wa kanmu gaskiya kuma mu binciko ainihin nufe-nufen zuciyarmu. Ta yaya za mu iya yin hakan? Za mu iya yin addu’a ga Jehobah wanda “ya san asiran zuciya.” (Zab. 44:21) Kalmarsa ma za ta iya taimaka mana. Idan muna karanta ta, za ta zama mana kamar madubin da ke sa mu ga ainihin siffarmu. (Yaƙ. 1:22-25) Shawarwari da tunasarwar da ake mana a taro da kuma littattafanmu za su iya taimaka mana. Waɗannan abubuwan za su taimaka mana mu kiyaye zuciyarmu kuma mu ci gaba da yin nagarta.

a An canja wasu sunaye.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba