Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 1/15 pp. 17-21
  • Ka Ci Gaba da Kusantar Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci Gaba da Kusantar Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • FASAHA
  • LAFIYAR JIKI
  • KUƊI
  • FAHARIYA
  • KADA KA NISANTA KANKA DAGA JEHOBAH
  • Za Ka Iya Yin Tsayayya da Shaidan Kuma Ka Yi Nasara!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Za Ka Iya Kuɓuta Daga Tarkon Shaiɗan!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Kada Ka Ƙyale Kome Ya Nisanta Ka Daga Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Kasance Da Ra’ayin Nassi Wajen Kula Da Lafiyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 1/15 pp. 17-21

Ka Ci Gaba Da Kusantar Jehobah

“Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.”—YAƘ. 4:8.

ZA KA IYA BAYYANAWA?

  • Ta yaya za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da fasaha da kuma lafiyar jiki?

  • Ta yaya za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi da kuma fahariya?

  • Ta yaya za mu ci gaba da kusantar Jehobah?

1, 2. (a) Mene ne ‘makiɗan’ Shaiɗan? (b) Mene ne zai taimake mu mu kusaci Allah?

JEHOBAH ALLAH ya halicci ’yan Adam don su ƙulla dangantaka na kud da kud da shi. Amma, Shaiɗan yana son mu ga cewa ba ma bukatar Jehobah. Kuma yana ƙoƙari ya sa ’yan Adam su gaskata da wannan tun lokacin da ya yi wa Hauwa’u ƙarya a lambun Adnin. (Far. 3:4-6) Tun lokacin, mutane da yawa suna ganin ba ma bukatar Allah.

2 Ba ma bukatar mu faɗa cikin tarkon Shaiɗan, domin “ba mu cikin rashin sanin makiɗansa ba.” (2 Kor. 2:11) Shaiɗan yana ƙoƙari ya nisanta mu daga Jehobah ta wajen sa mu yi zaɓi marar kyau. Amma, kamar yadda talifin da ya gabata ya nuna, muna iya yin zaɓi da ya dace game da aiki da nishaɗi da kuma biyan bukatun iyali. Wannan talifin zai nuna yadda Shaiɗan yake yin amfani da fasaha da lafiyar jiki da kuɗi da kuma fahariya don ya gwada mu. Amma, idan muka yi zaɓi mai kyau za mu ‘kusaci Allah.’—Yaƙ. 4:8.

FASAHA

3. A waɗanne hanyoyi ne mutum zai iya yin amfani da kwamfuta da kuma wasu na’urori?

3 Mutane da yawa suna amfani da kwamfuta da na’urori dabam-dabam a faɗin duniya. Waɗannan ƙere-ƙere suna da ban taimako idan aka yi amfani da su da kyau. Idan ba haka ba, za su hana mu bauta wa Ubanmu na samaniya. Alal misali, da kwamfuta ne aka wallafa da kuma buga wannan jaridar da kake karantawa. Kwamfuta za ta iya taimaka mana mu yi bincike da aika wa mutane saƙo da kuma nishaɗi. Amma, idan muna son kwamfuta sosai, muna iya ɓata lokaci wajen yin amfani da su. Masu talla suna sa mu ji kamar an bar mu a baya idan ba mu saya sabon yayin na’aura ba. Wani saurayi yana son wata irin kwamfuta da ake kira Tablet sosai da har ya sayar da ƙodarsa a ɓoye don ya saye ta. Wannan wauta ce!

4. Ta yaya wani ɗan’uwa ya magance mugun hali na yawan yin amfani da kwamfuta?

4 Ya ma fi muni mutum ya ɓata dangantakarsa da Jehobah don yawan yin amfani da na’urori. Wani Kirista ɗan shekara 28 mai suna Jonaya ce: “Na san cewa Littafi Mai Tsarki ya ce mu ‘rifta zarafi’ don abubuwan da suka shafi bautarmu ga Jehobah, amma ba abin da ya fi cin lokacina kamar kwamfuta.” Jon yana amfani da Intane har tsakar dare, kuma ya ce: “Duk da cewa na gaji tikis, ba shi da sauƙi na daina taɗi a dandalin ko kuma kallon bidiyo, kuma wasu cikinsu ba su dace da Kirista ba. Mene ne Jon ya yi don ya magance wannan matsalar? Ya sa kwamfutar ta riƙa kashe kanta idan lokacin barcinsa ya kai.—Karanta Afisawa 5:15, 16.

5, 6. (a) Mene ne iyaye za su yi wa yaransu? (b) Ta yaya iyaye za su tabbata cewa yaransu suna da abokan kirki?

5 Iyaye ba sa bukatar su sa ido a kome da yaransu suke yi, amma ya kamata su riƙa kula da yadda suke amfani da kwamfuta. Kada ku ƙyale su su riƙa shigan dandalin da ake lalata da mugun wasanni da sihiri da kuma mugun tarayya. Idan kuka kasance da halin ko in kula, yaran za su riƙa ganin cewa abin da suke yi ya dace. A matsayin iyaye, kuna da hakkin kāre yaranku daga kowane abin da zai nisanta su daga Jehobah. Ko dabbobi ma suna kāre ’ya’yansu daga haɗari. Ka yi tunanin abin da karen daji zai yi idan wani yana son ya ɗauki ’ya’yansa!—Gwada Hosiya 13:8.

6 Ku taimaka wa yaranku su yi tarayya da Kiristoci manya da ƙanana masu halin kirki. Ku tuna cewa yaranku suna bukatar ku kasance tare da su! Saboda haka, ku nemi lokaci ku yi dariya da wasa da kuma aiki tare da su. Hakan zai taimaka muku ku ‘kusaci Allah’ tare da yaranku.b

LAFIYAR JIKI

7. Me ya sa dukanmu muke son kasancewa da ƙoshin lafiya?

7 Sau da yawa, mukan tambayi mutane, ‘Yaya jiki?’ Hakan ya nuna cewa ba wanda ba ya rashin lafiya, domin iyayenmu na farko sun bar Shaiɗan ya nisanta su daga Jehobah. Shaiɗan yana farin ciki idan muna rashin lafiya, domin hakan zai sa ya yi mana wuya mu bauta wa Jehobah. Kuma idan muka mutu, ba za mu iya bauta wa Jehobah ba sam. (Zab. 115:17) Saboda haka, muna iya ƙoƙarinmu don mu kasance da ƙoshin lafiya. Kuma ya kamata mu riƙa kula da lafiyar ’yan’uwanmu.

8, 9. (a) Ta yaya za mu daina yawan damuwa game da lafiyar jikinmu? (b) Me ya sa yake da kyau mu riƙa farin ciki?

8 Amma, bai kamata mu riƙa tunani game da lafiyar jikinmu kawai ba. Wasu suna yawan magana game da wani irin abinci da hanyar jinya ko kuma magunguna fiye da wa’azin bishara game da Mulkin Allah. Suna iya ganin cewa suna taimaka wa mutane ne. Duk da haka, bai dace ba mu mai da Majami’ar Mulki da na manyan taronmu ko kuma taron gunduma wajen sayar da magunguna ko kuma tallar wasu hanyoyin jinya. Me ya sa?

9 Muna halartar taro don mu tattauna Littafi Mai Tsarki kuma mu samu farin cikin da ruhu mai tsarki na Allah yake bayarwa. (Gal. 5:22) Manufar taronmu ba don tattauna hanyoyin jinya da magunguna ba ne, ko da wani yana son ya yi magana game da su. Yin hakan yana iya hana wasu farin ciki. (Rom. 14:17) A bar mutane su tsai da shawara game da yadda za su kula da lafiyar jikinsu. Babu wanda zai iya warkar da dukan cututtuka, har da likitoci ma. Likitan da ya fi ƙwarewa ma yana ciwo, ya tsufa, kuma daga baya ya mutu. Yawan damuwa game da lafiyarmu ba zai taimaka mana ba. (Luk 12:25) Maimakon haka, “zuciya mai-jin daɗi magani ce mai-kyau.”—Mis. 17:22.

10. (a) Waɗanne halaye ne suke sa mutum ya yi kyau a gaban Jehobah? (b) A wane lokaci za mu samu cikakken ƙoshin lafiya?

10 Hakazalika, ya dace mu kula da siffarmu. Amma, ba ma bukatar mu kashe kanmu wajen neman mu kawar da alamun tsufa. Waɗannan alamun suna nuna cewa mun manyanta kuma suna sa a daraja mu. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Furfura rawanin daraja ce, idan an iske ta cikin hanyar adalci.” (Mis. 16:31) Jehobah yana ɗaukan mu hakan, kuma ya kamata mu kasance da wannan ra’ayin. (Karanta 1 Bitrus 3:3, 4.) Saboda haka, ba ma bukatar mu sa ranmu cikin kasada ta wajen yin jinya ko kuma fiɗa wai don muna son mu kyautata siffarmu. “Farinciki na Ubangiji” shi ne ainihi yake sa mutum ya yi kyau, ba shekarunsa ba. (Neh. 8:10) A cikin sabuwar duniya ce kawai za mu samu ƙoshin lafiya kuma mu koma ƙuruciya. (Ayu. 33:25; Isha. 33:24) Kafin lokacin, muna bukatar mu yi zaɓin da suka dace kuma mu dogara ga alkawuran Jehobah. Hakan zai taimaka mana mu ji daɗin rayuwarmu a yanzu kuma ba za mu riƙa damuwa ainun game da lafiyar jikinmu ba.—1 Tim. 4:8.

KUƊI

11. Ta yaya kuɗi zai iya zama mana tarko?

11 Yana da kyau mu yi kasuwancin da zai sa mu samu kuɗi don biyan bukatunmu. (M. Wa. 7:12; Luk 19:12, 13) Amma, “son kuɗi” zai iya nisanta mu daga Jehobah. (1 Tim. 6:9, 10) “Ɗawainiyar duniya” wato, damuwa ainun game da samun abin biyan bukatu zai iya hana mu bauta wa Jehobah. Hakan ma yake da “ruɗin dukiya” wato, ra’ayin cewa kuɗi zai sa mu farin ciki da kuma samun kwanciyar rai. (Mat. 13:22) Yesu ya bayyana sarai cewa “ba wanda” zai iya bauta wa Allah da kuma dukiya a take.—Mat. 6:24.

12. A waɗanne hanyoyi ne mutane suke ƙoƙarin samun kuɗi mai yawa, kuma ta yaya za mu guji yin hakan?

12 Kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da kuɗi zai iya sa mu yi abin da ba shi da kyau. (Mis. 28:20) Wasu sun sayi katin caca ko kuma sun shiga kasuwanci inda ake samun matsayi na hawa bisa hawa, har sun yi wa wasu a cikin ikilisiya alkawari cewa su ma za su yi kuɗi sosai idan suka shiga. A wasu lokatai, ’yan’uwa sun gaya wa ’yan’uwansu a cikin ikilisiya su ara musu kuɗi da alkawari cewa za su biya da riɓa mai yawa. Kada ku bar haɗama ya sa ku yi hasarar kuɗi mai yawa. Saboda haka, ku mai da hankali, domin da ƙyar mutum zai iya zama mai kuɗi dare ɗaya.

13. Yaya Jehobah yake son mu ɗauki kuɗi?

13 Idan muka ‘fara biɗan mulki da adalcin’ Jehobah, zai albarkaci aikinmu kuma za mu samu na biyan bukatunmu. (Mat. 6:33; Afis. 4:28) Ba ya son mu riƙa gyangyaɗi a taro domin mun yi aiki mun gaji tikis ko kuma mu je Majami’ar Mulki muna tunanin kuɗi. Mutane da yawa a duniya suna ganin ya dace su nemi kuɗi ƙarfi da yaji, don kada su sha wahala sa’ad da suka tsufa. Kuma sukan gaya wa yaransu su bi misalinsu. Amma, Yesu ya nuna cewa irin wannan ra’ayin bai dace ba. (Karanta Luka 12:15-21.) Wannan ya tuna mana da Gehazi, wanda yake ganin zai iya zama mai haɗama kuma ya ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci.—2 Sar. 5:20-27.

14, 15. Me ya sa bai dace mu yi tunanin cewa kuɗi zai sa mu samu kwanciyar rai? Ka ba da misali.

14 Wasu gaggafa sun mutu a cikin ruwa domin sun kama kifin da ya fi ƙarfinsu amma sun ki sakewa. Hakan yana iya faru mana idan muka nemi kuɗi ruwa a jallo. Wani dattijo mai suna Alex ya ce: “Ba na wasa da kuɗi ko kaɗan, idan na zuba shamfu da yawa, nakan ɗura sauran a gora.” Amma, Alex yana ganin idan ya ƙara kuɗi zai bar aikinsa kuma ya zama majagaba. Sai ya soma saya da sayar da hannayen jari kuma ya zuba duk kuɗinsa a kasuwancin. Ya ma ari kuɗi don ya sayi hannayen jari da yawa. Amma, kafin ya ankara, sai farashin ya sauka. Alex ya ce: “Na ƙudura niyya na samu kuɗin da na kashe. Ina ganin idan na ɗan jira, farashin hannayen jari da na saya zai haura kuma.”

15 Alex ya yi watanni da yawa yana tunani a kan hannayen jarin da ya saya. Ya yi masa wuya ya mai da hankali ga hidimarsa ga Jehobah, kuma ya ƙasa yin barci. Amma, farashin jarin bai sake haurawa ba. Alex ya yi hasarar duk kuɗinsa har ya sayar da gidansa. Ya ce: “Na sa iyalita cikin matsala.” Amma ya koyi darassi mai muhimmanci. Ya daɗa cewa, “Yanzu na sani cewa duk wanda ya dogara ga duniyar Shaiɗan zai yi da-na-sani.” (Mis. 11:28) Idan muka dogara ga kuɗinmu ko kuma iyawarmu a kasuwanci, muna dogara ainihi ga Shaiɗan wanda shi ne “allah na wannan zamani.” (2 Kor. 4:4; 1 Tim. 6:17) Alex ya sauƙaƙa salon rayuwarsa tun da daɗewa “sabili . . . da bishara.” Hakan ya sa shi da iyalinsa farin ciki kuma ya taimaka musu su kusaci Jehobah.—Karanta Markus 10:29, 30.

FAHARIYA

16. A wace hanya ce fahariya take da kyau, kuma mene ne zai faru idan muna ganin mun fi kowa?

16 Ba laifi ba ne mu yi alfahari a kan abubuwan da suka dace. Alal misali, ya kamata mu yi alfahari cewa mu Shaidun Jehobah ne. (Irm. 9:24) Shi ya sa muke ƙoƙari mu tsai da shawarwari masu kyau kuma mu bi ƙa’idodin Allah. Amma, ya kamata mu mai da hankali kada mu zama masu fahariya ainun kuma mu ga cewa mun fi Jehobah, domin hakan yana iya nisanta mu da shi.—Zab. 138:6; Rom. 12:3.

17, 18. (a) Ka ambata misalai na masu tawali’u da masu fahariya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (b) Mene ne wani ɗan’uwa ya yi don kada fahariya ta nisanta shi daga Jehobah?

17 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da mutane masu fahariya da masu tawali’u. Sarki Dauda ya nemi ja-gorar Jehobah, kuma Jehobah ya albarkace shi. (Zab. 131:1-3) Amma, Jehobah ya kunyantar da Sarki Nebukadnezzar da Belshazzar domin fahariyarsu. (Dan. 4:30-37; 5:22-30) A yau ma, wasu yanayi za su iya gwada ko mu masu tawali’u ne. Akwai wani mai suna Ryan da ya ƙaura zuwa wata ikilisiya, bayan ya yi shekara 32 yana hidima a matsayin bawa mai hidima. Ya ce: “Dā ina ganin ba zan daɗe kafin na zama dattijo ba, amma shekara ɗaya ya wuce ba a naɗa ni ba.” Shin Ryan ya yi fushi ne, yana ganin cewa dattawa ba sa daraja shi? Shin fahariya ta nisanta shi daga Jehobah da kuma mutanensa, kuma ta sa ya daina halartan taro? Da a ce kai ne, da mene ne za ka yi?

18 Ryan ya ce: “Na yi bincike a kan yadda mutum zai iya jimrewa idan ba a biya muradinsa nan da nan ba. (Mis. 13:12) “Sai na fahimci cewa ina bukatar in yi haƙuri kuma in zama mai tawali’u. Ina bukatar in bar Jehobah ya horar da ni.” Ryan ya soma taimakon mutane a cikin ikilisiya da kuma waɗanda ya yi wa wa’azi. Ba da daɗewa ba, ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Sai ya ce: “Amma, bayan shekara ɗaya da rabi sai aka naɗa ni dattijo. Hakan ya sa ni mamaki sosai domin a lokacin, na ma daina damuwa game da wannan gatan domin na shagala sosai a yin wa’azi.”—Karanta Zabura 37:3, 4.

KADA KA NISANTA KANKA DAGA JEHOBAH

19, 20. (a) Ta yaya za mu tabbata cewa biɗe-biɗe na yau da kullum ba su nisanta mu daga Jehobah ba? (b) Waɗanne misalai ne za su iya taimaka mana mu ci gaba da kusantar Jehobah?

19 Dukan fannoni bakwai da aka tattauna a waɗannan talifofi biyu suna da amfani sosai a rayuwarmu. Muna fahariya don mu bayin Jehobah ne. Muna iya jin daɗin iyalinmu da kuma ƙoshin lafiya. Aiki da kuɗi suna iya taimaka mana mu biya bukatunmu. Nishaɗi yana iya sa mu samu wartsakewa kuma na’urori suna da amfani. Amma, ya kamata mu tuna cewa idan mun yi su a lokacin da bai dace ba kuma idan sun ci dukan zarafinmu ko kuma mun yi su a hanyar da ba ta dace ba, muna iya nisanta kanmu daga Jehobah.

Kada ka bar kome ya nisanta ka daga Jehobah!

20 Shaiɗan yana son ka daina bauta wa Jehobah. Amma, kana iya hana hakan faruwa da kai da iyalinka! (Mis. 22:3) Ka kusace Jehobah kuma ka ci gaba da yin hakan. Muna da misalan mutane da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suka yi hakan. Anuhu da Nuhu sun yi “tafiya tare da Allah.” (Far. 5:22; 6:9) Musa ya ci gaba da bauta wa Jehobah “kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” (Ibran. 11:27) Yesu ya yi abin da ke faranta wa Jehobah rai a ko da yaushe, kuma ya albarkace shi. (Yoh. 8:29) Ka yi koyi da irin waɗannan misalan. “Ka yi murna kullum: ka yi addu’a ba fasawa; cikin kowanne abu ka bada godiya.’ (1 Tas. 5:16-18) Kuma kada ka bar kome ya nisanta ka daga Jehobah!

a An canja sunayen.

b Ka duba talifin nan “Yin Renon Yara Don Su Zama Nagargaru” a fitowar Hasumiyar Tsaro ta Yuli-Satumba 2010, shafi na 18-20.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba