Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 12/15 pp. 14-17
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Rika Daraja “Abin da Allah Ya Hada”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 12/15 pp. 14-17

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Kafin ni da matata muka zama Shaidun Jehobah, mun amince likitoci su cire ƙwan matata da maniyyina kuma su cakuɗe su ta wata irin fasaha domin ta yi juna biyu. Amma, an saka ƙwai da maniyyin da suka rage da sun riga sun zama tayi a cikin firiji don kada su mutu. Dole ne mu ci gaba da ajiye su ko mu zubar da su?

▪ Wannan ɗaya ne kawai cikin batutuwa masu muhimmanci game da ɗabi’a da ma’aurata suke fuskanta idan suka zaɓi su yi juna biyu ta wajen fasahar da ake kira in vitro fertilization (IVF). Wannan fasaha ce da ake haɗa maniyyi da ƙwai don su zama tayi a waje kafin a saka tayin a cikin macen, kuma ya ci gaba da girma. Hakkin ma’aurata ne su yanke wa kansu shawarar abin da ya kamata su yi. Amma, yana da kyau su san abin da wannan fasahar ta ƙunsa.

A shekara ta 1978 ce aka sami mace ta farko a ƙasar Ingila da ta haihu ta wannan hanyar. Wannan matar ba ta iya ɗaukan ciki da kanta domin tana da matsala a mahaifarta, wanda yana sa maniyyi ba ya iya shiga ya haɗu da ƙwan cikinta. Sai likitoci suka yi mata fiɗa kuma suka cire ƙwan cikinta, sa’an nan suka haɗa ƙwan da maniyyin mijinta kuma suka cakuɗe su. Bayan tayin ya ɗan yi girma, sai aka mai da shi a cikinta. Kuma ta haifi jaririya.

Babu bambanci sosai a yadda ƙasashe dabam-dabam suke amfani da wannan fasahar. Ga yadda suke yi: Da farko, ana ba mace magunguna da za su sa ƙwai su yi girma a mahaifarta. Mijin kuma yana bukatar ya fitar da maniyyinsa ta wajen yin wasa da al’aurarsa. Ana tsabtace maniyyin, sa’an nan a haɗa da ƙwan macen a ɗakin bincike. Wannan maniyyin yana iya sa ƙwai fiye da ɗaya su zama tayi kuma su soma girma. Bayan kwana ɗaya ko fiye da hakan, sai a bincika su tayin don a ga ko waɗanne cikinsu ke da lafiya sosai, da za su iya rayuwa a cikin macen. Kuma bayan kwana uku, sai a saka tayi biyu ko uku mafi kyau a cikin macen don ta yi juna biyu. Idan guda ɗaya ko biyu suka rayu, zai zama cewa macen ta yi juna biyu kuma za ta haihu.

To mene ne zai faru da su tayin da suka rage, watau waɗanda ba a saka a mahaifar macen ba domin ba su da lafiya? Idan aka bar su kurum, za su mutu. Saboda haka, ana ajiye su a wani ruwan magani a daskare. Me ya sa? Domin idan tayin da aka saka wa macen ba su rayu ba, sai a sake saka mata waɗannan da aka ajiye. A wannan loton, farashin ba zai yi tsada ba. Amma, akwai matsalolin da yin hakan ya ƙunsa. Kamar ma’auratan da suka yi wannan tambayar, wasu matsalarsu ita ce abin da za su yi da waɗannan tayi da suka rage. Wataƙila ba sa son su sake haihuwa, ko yanzu sun tsufa ainun ko kuma ba su da kuɗi. Wasu suna tsoron samun tagwaye ko fiye da haka.a Matsala takan taso idan ɗaya cikin ma’auratan ya rasu ko ya auri wata dabam. Shi ya sa wasu ma’aurata suna kashe kuɗi sosai don ajiyar tayin har tsawon shekaru da yawa.

Wani likita da ya ƙware sosai a wannan fasahar ya faɗa a jaridar New York Times cewa mutane da yawa sun rikice game da abin da za su yi da tayin da suka ragu. Jaridar ta ci gaba da cewa: “Aƙalla an yi ajiyar tayi guda 400,000 a asibitoci da ke ƙasar, kuma kowace rana ana ajiyar wasu . . . Idan aka yi ajiyar tayin da kyau, suna iya kai shekara 10 ko fiye da hakan. Amma idan ƙanƙarar da aka yi ajiyar su da shi ta narke, wasu za su mutu.” Hakan yana sa wasu Kiristoci su sake tunani da kuma la’akari da wannan fasahar. Me ya sa?

Ga wani yanayi da ya yi kama da wanda muka tattauna, kuma zai iya taimaka wa Kiristoci ma’aurata. Kirista yana da hakkin tsai da shawara ko yana son a tsawonta ran wani danginsa, wanda ke rashin lafiya kuma ba zai rayu ba sai da taimakon na’ura. Alal misali, na’urar da ke sa mutum ya ci gaba da numfashi don ya rayu. Kiristoci na gaskiya ba sa ƙyaliya game da batun jinya, domin suna daraja rai. Hakan ya ya jitu da abin da ke cikin Fitowa 20:13 da kuma Zabura 36:9. Mujallar Awake! na 8 ga Mayu, 1974 ta ce: “Kiristoci na gaskiya suna daraja rai kamar yadda Allah yake yi. Suna yin la’akari da lamirinsu kuma suna biyayya ga dokokin gwamnati. Suna rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Shi ya sa ba za su yadda a sa majiyyaci ya rasu da gangan ba.” A wasu yanayi, abin da za a iya yi kaɗai shi ne a yi amfani da na’ura don wannan majiyyacin ya rayu. Wajibi ne iyalin majiyyacin su yanke shawara ko za a ci gaba da yin amfani da na’urar ko a’a.

Wannan yanayin ya yi dabam da na ma’aurata da suka yi ajiyar tayi. Wataƙila, ana iya ba su shawara cewa a cire tayin daga ma’ajin don ƙanƙarar ta narke. Tayin za su mutu da sannu-sannu idan ba sa cikin ma’ajin. Ba wanda zai tsai da wa ma’auratan wannan shawarar.—Gal. 6:7.

Don ma’aurata sun yi amfani da wannan fasahar na yin juna biyu, zaɓinsu ne su ci gaba da biya don a ci gaba da ajiyar tayin ko kuma su sake yin amfani da shi a nan gaba. Wasu ma’aurata suna iya yanke shawarar su daina biya don a riƙa kula da tayin, domin a ganinsu tayin yana rayuwa ne kawai ta hanyar na’ura. Kiristoci da ke cikin irin wannan yanayin suna da hakki a gaban Allah na yin amfani da lamirinsu da Littafi Mai-Tsarki ya koyar. Ya kamata su yi burin ci gaba da kasancewa da lamiri mai kyau, kuma kada su sa wasu tuntuɓe.—1 Tim. 1:19.

Wani masani ya lura cewa yawancin ma’aurata sun rikice kuma sun damu ƙwarai game da abin da za su yi da tayinsu da aka ajiye. Kuma ya kammala cewa: “Kamar dai dukan ma’auratan sun rasa na yi.”

Babu shakka, ya kamata Kiristoci da suke son su yi amfani da wannan fasahar su yi la’akari sosai da matsalolin da ke tattare da ita. Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi cewa: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya: Amma wawaye sukan bi ciki, su sha wuya.”—Mis. 22:3.

Namiji da tamace da suke zama tare suna nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suna son su yi rajistan aurensu don su yi baftisma. Tun da yake, shi ba ɗan ƙasar ba ne, kuma gwamnati ba ta yarda da zamansa ba, ba yadda zai yi hakan. Shin ya dace ne su sa hannu a takardar yarjejeniya da ake kira Declaration Pledging Faithfulness sa’an nan su yi baftisma?

▪ Kamar dai yin hakan zai magance matsalarsu, amma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, zai dace idan ba su yi hakan ba. Don mu fahimci dalilin, za mu tattauna abin da takardar nan Declaration Pledging Faithfulness take nufi da kuma lokacin da za a iya amfani da ita.

Wannan takarda ce da namiji da tamace da suke zama tare za su sa hannu a gaban shaidu, kuma ya nuna cewa ba za su iya rajistar aurensu ba don dalilin da aka nuna a cikin sakin layi na gaba. Sa’ad da suka sa hannu a wannan takardar, sun yi alkawari a gaban Allah da kuma shaidu cewa ba za su ci amanar juna ba, kuma za su yi rajistar aurensu idan suka samu damar yin hakan. Idan suka yi hakan, ikilisiyar za ta ɗauke su a matsayin ma’aurata da suka yi aure bisa doka.

A wane lokaci ne ake amfani da takardar nan Declaration Pledging Faithfulness? Kafin mu ba da amsar, ya kamata mu fahimci yadda Jehobah yake ɗaukan aure da kuma kashe aure. Shi ne ya kafa aure kuma yana daraja shi. Ɗansa ya ce: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:5, 6; Far. 2:22-24) Ya daɗa cewa: ‘Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba [lalata], ya kuwa auri wata, zina ya ke yi: shi kuma wanda ya auri sakakkiyar, zina ya ke yi.’ (Mat. 19:9) Hakan ya nuna cewa “fasikanci” ko lalata ne kaɗai dalilin kashe aure da Littafi Mai Tsarki ya ambata. Alal misali, idan mutum ya yi jima’i da wata da ba matarsa ba, matarsa tana iya kashe aurensu idan ta so. Idan ta yi hakan, tana da ’yanci ta sake aurar wani.

A dā, wasu manyan addinai ba su amince da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kashe aure ba. Sun ce ba dalilin da zai sa a kashe aure. Har wa yau, malaman addinai a wasu ƙasashe suna da iko sosai da ya sa ana hana mutane su kashe aure, ko da ma saboda dalilin da Yesu ya bayar ne. A wasu ƙasashe kuma, dokar ta ba da izini a kashe aure amma ba shi da sauƙi a yin hakan. Yana iya ɗauka shekaru da yawa kafin a yi hakan. Waɗannan addinai ko kuma gwamnati suna hana mutane yin abin da Allah ya ƙyale a yi.—A. M. 11:17.

Alal misali, tamace ko namiji suna iya kasance a ƙasar da ba zai yiwu su kashe aurensu bisa ƙa’ida ba, ko kuma yin hakan yana iya kasance da wuya sosai duk da yake suna da ’yancin yin hakan a gaban Allah. Ba a shirya wannan takardar don ƙasashe da yake da sauƙi a kashe aure ba, ko ma idan yin haka yana da ɗan wuya ko kuma tsada. Ikilisiyar Kirista ta yi wannan shirin ne domin ƙasashen da kashe aure bisa doka yake da wuya ainun.

Waɗanda suke zama a irin waɗannan ƙasashe sun son su sa hannu a takardar don ba sa son su kashe kuɗi ko kuma ɓata lokaci, amma hakan ba dalilin da ya sa aka shirya wannan takardar ba.

Bari mu yi la’akari da wannan tambayar da aka yi. Wannan namiji da tamace da suke zama tare suna son su yi aure bisa ga doka, kuma ba su da wani aure dabam. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ba su ’yancin yin aure. Yanayinsu ya yi dabam da na waɗanda suka yi aure kuma suna son su kashe auren, amma dokar ƙasar ta hana su yin hakan. Saboda haka, ba za su iya sa hannu a wannan takardar ba. Matsalarsu ita ce, gwamnati ba ta amince da zaman mutumin a ƙasar ba, kuma ba za ta ƙyale su su ɗaure aure ba. (A ƙasashe da yawa, gwamnati tana barin mutane su yi aure ko idan namijin ko mace ko kuma dukansu ba su da izinin zama a ƙasar.) Mene ne waɗannan za su yi? Suna iya zuwan wata ƙasa don su yi aure bisa doka. Zai yiwu su yi aure a cikin ƙasar da suke idan mutumin ya samu izinin zama a ƙasar.

Hakika, namijin da tamacen suna iya yin gyara da ake bukata don su yi biyayya ga dokokin Allah da kuma na Kaisar. (Mar. 12:17; Rom. 13:1) Idan suka yi aure bisa doka, suna iya yin baftisma.—Ibran. 13:4.

[Hasiya]

a Idan tayin da ke girma a cikin macen yana da ɗan matsala ko kuma tayin suna da yawa fa? Idan ta kashe tayin da gangan, hakan zubar da ciki ne. Wannan fasahar tana da nata matsaloli. Matsala ta ɗaya ita ce tayi fiye da ɗaya suna iya girma a cikin macen. Ta biyu, tana iya haifar bakwaini. Ta uku ita ce matsalar zuban jini. Ana iya ce wa macen da take da tayi da yawa a cikinta ta “rage” su ta wajen yarda a kashe wasu. Yin hakan zub da ciki ne da gangan, kuma wannan kisa ce.—Fit. 21:22, 23; Zab. 139:16.

[Bayanin da ke shafi na 14]

Kiristoci da ke cikin irin wannan yanayin suna da hakki a gaban Allah na yin amfani da lamirinsu da Littafi Mai-Tsarki ya koyar

[Akwati a shafi na 15]

WASU HANYOYIN YIN JUNA BIYU TA WANNAN FASAHAR

Yin amfani da wannan fasahar ya sa aka samo wasu hanyoyin yin juna biyu da suka saɓa wa koyarwar Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ana iya cakuɗe ƙwan mace da maniyyin wani mutum da ba mijinta ba ne. Sai a saka mata tayin a mahaifarta. (A wasu lokatai, ’yan maɗigo suna amfani da wannan hanyar.) Ko kuma za a iya cakuɗe maniyyin mijin da ƙwan macen da ba matarsa ba ce. Bayan hakan, matar za ta iya amince a saka tayin da aka cakuɗe da maniyyin mijinta da ƙwan wata mace cikin jikinta.

A wani yanayi dabam, ana saka wa mace tayin da aka cakuɗe da ƙwai da kuma maniyyin wasu dabam. A wani yanayin kuma, ma’aurata za su ba da ƙwai da maniyyi don a cakuɗe. Bayan haka, sai a saka tayin a cikin wata mace dabam da za ta haifa musu jaririn.b

Bayin Allah ba sa amfani da waɗannan hanyoyin yin juna biyu domin wannan umurnin: “Ba za ka ba da maniyyinka ga matar maƙwabcinka don kada ka ƙazantar da kanka.” (Lev. 18:20, 29, NW; Mis. 6:29) Idan ma’aurata suka yi amfani da tayi daga ƙwai ko maniyyin wasu dabam, Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lalata, wato, por·nei’a, da Helenanci. Waɗannan hanyoyin yin juna biyu ba su dace ba don sun ƙunshi yin amfani da al’aura a hanyar da ba ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba.—Mat. 5:32; 1 Kor. 5:11; 6:9, 18; Ibran. 13:4.

[Hasiya]

b Awake! na 8 ga Maris, 1993, shafuffuka na 26-27 ya tattauna game da ɗaukan ciki a madadin wata mace.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba