Ka Riƙa Gafarta Wa Mutane
“Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna.”—KOL. 3:13.
MECE CE AMSARKA?
Me ya sa ya kamata mu riƙa gafarta wa mutane?
Ta yaya Yesu ya kwatanta amfanin gafarta wa mutane?
Wace albarka ce za mu samu idan muna gafarta wa mutane?
1, 2. Me ya sa ya kamata ka kasance a shirye ka riƙa gafarta wa mutane?
KALMAR ALLAH tana sa mu san yadda Jehobah yake ɗaukan zunubi da yadda yake ji sa’ad da muka yi zunubi. Ta kuma bayyana yadda yake gafarta mana zunubanmu. A talifin da ya gabata, mun tattauna abin da ya sa Jehobah ya gafarta wa Dauda da Manasseh. Jehobah ya gafarta musu domin sun tuba, kuma sun duƙufa cewa ba za su ƙara ba. Saboda haka, Jehobah ya nuna musu jin ƙai.
2 Yanzu za mu tattauna yadda za mu gafarta wa mutane. Da yaya za ka ji da a ce wani danginka yana cikin waɗanda Manasseh ya kashe? Da za ka gafarta wa Manasseh kuwa? Wannan tambayar ta dace domin muna cikin duniya da ke cike da mugunta da rashin da’a da kuma son kai. Me ya sa Kirista zai riƙa gafarta wa mutane? Idan ka fuskanci rashin adalci, mene ne zai taimake ka ka kame kanka kuma ka yi abin da zai faranta wa Jehobah rai?
DALILIN GAFARTA WA MUTANE
3-5. (a) Wane kwatanci ne Yesu ya yi don ya nuna muhimmancin gafarta wa mutane? (b) Wane darasi ne muka koya daga kwatancin Yesu da ke cikin Matta 18:21-35?
3 Yana da muhimmanci mu gafarta wa waɗanda suka yi mana laifi ko su Shaidu ne ko a’a. Hakan zai sa mu yi zaman lafiya da waɗanda suke cikin iyalinmu da abokanmu da ’yan’uwanmu da kuma Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya dace mu riƙa gafarta wa mutane ko so nawa ne suka yi mana laifi. Yesu ya ba da misalin wani bawa da maigidansa yake bin sa bashi, domin ya nuna mana cewa yana da muhimmanci mu riƙa gafarta wa mutane.
4 Bawan ya ci bashi da zai bukaci ya yi aiki na kwanaki miliyan sittin kafin ya biya, amma maigidansa ya yafe masa bashin. Amma, ashe akwai wani bawa da ya ci bashi a wajen wannan bawan da aka gafarta masa. Bashin nawa ne ya ci? Ya ci bashin da zai bukaci ya yi aiki na kwanaki ɗari ne kawai. Ya ƙi ya gafarta wa bawan kuma ya ce ya biya shi bashinsa. Bawan ya ce ya ɗan ba shi lokaci, amma bawan da aka gafarta wa ya maƙure masa wuya kuma ya sa aka jefa shi a kurkuku. Wannan ya sa maigidansa fushi sosai. Sai ya ce: “Ba ya kamata gareka ba kai kuma ka jiƙan abokin bautanka, kamar yadda ni na jiƙanka? Ubangijinsa kuwa ya yi fushi, ya bāshe shi ga masu-wulakantawa, har shi biya dukan abin da ke kansa.”—Mat. 18:21-34.
5 Wane darasi ne Yesu yake so mu koya daga wannan labarin? Ya ce: “Hakanan kuma Ubana na sama za ya yi muku, idan cikin zuciyarku ba ku gafarta wa ’yan’uwanku.” (Mat. 18:35) Kwatancin Yesu a bayane yake. Tun da yake mu ajizai ne, ba zai yiwu mu riƙa yi wa Jehobah biyayya tuttur ba. Duk da haka, yana a shirye ya gafarta mana baki ɗaya kamar ba mu taɓa yin laifin ba. Ya kamata mu riƙa gafarta wa mutane idan muna so mu zama abokan Jehobah. Yesu ya bayyana wannan a Huɗuba da ya yi a kan Dutse, ya ce: “Idan kuna gafarta wa mutane laifofinsu, Ubanku na sama shi ma za ya gafarta muku. Amma idan ba ku gafarta wa mutane laifofinsu, Ubanku kuma ba za shi gafarta naku laifofin ba.”—Mat. 6:14, 15.
6. Me ya sa yake wa mutane wuya su gafarta wa wanda ya yi musu laifi?
6 Amma, kana iya cewa, faɗe-faɗe ba yi ba ne. Domin mukan yi fushi sosai sa’ad da mutane suka yi mana laifi. Saboda haka, muna iya ganin ya dace a yi wa mutumin horo ko kuma a sa ya sha wahala. Wasu suna iya jin cewa ba za su taɓa gafarta wa wanda ya yi musu laifi ba. Idan kana jin hakan, mene ne za ka yi don ka riƙa gafarta wa mutane yadda Jehobah ya ce mu yi?
ME YA SA KA KE JIN HAKAN?
7, 8. Mene ne zai taimake ka ka riƙa gafarta wa mutane sa’ad da suka yi maka laifi?
7 Muna iya yin fushi sosai, sa’ad da aka yi mana laifi ko kuma muna ganin an yi mana laifi. Da akwai lokacin da wani matashi yi fushi kuma ya bayyana yadda ya ji, ya ce: “Na bar gida kuma na ce ba zan sake dawowa ba. A ranar sai na bi wata hanya ni kaɗai, sa’ad da nake tafiya a wannan hanyar, sai na soma hucewa. Na koma gida, ina da-na-sani.” Idan ka huce yadda wannan mutumin ya yi, hakan zai sa ka yi tunani sosai game da yanayin, maimakon ka yi abin da zai sa ka yi da-na-sani.—Zab. 4:4; Mis. 14:29; Yaƙ. 1:19, 20.
8 Idan ka huce amma abin da ya faru yana damunka kuma fa? Ka yi tunani a kan dalilin da ya sa ka yi fushi. Kana ganin cewa an cuce ka ne? Ko kuma kana ganin cewa mutumin da gangan ya ɓata maka rai? Abin da ya yi yana da tsanani ne sosai? Za ka san ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimake ka ka kame kanka, idan ka san abin da ke sa ka fushi. Hakan zai sa ka yi abin da Jehobah yake so. (Karanta Misalai 15:28; 17:27.) Yin hakan zai sa ka kasance a shirye ka riƙa gafarta wa mutane. Ko da yin hakan yana da wuya, Kalmar Allah za ta taimake ka ka bincika ‘tunanin zuciyarka da nufe-nufenta,’ don ka riƙa gafarta wa mutane yadda Jehobah yake yi.—Ibran. 4:12.
YA KAMATA KA YI FUSHI?
9, 10. (a) Wane mataki ne za ka ɗauka idan kana fushi? (b) Yaya za ka ji idan ba ka saurin fushi, kuma kana shirye ka riƙa gafarta wa mutane?
9 Da akwai abubuwa da yawa da za su iya sa mu fushi. Alal misali, mene ne za ka yi idan kana tuƙi, sai wata mota ta kusan buge ka? Wasu direbobi sukan yi fushi sosai har su soma faɗa da direban. Amma, ba zai dace Kirista ya yi haka ba.
10 Zai fi dacewa ka yi tunani, kafin ka ɗauki mataki. Wataƙila kai ma kana da laifi, domin ba ka mai da hankali ba sa’ad da kake tuƙi. Ko kuma wataƙila motarsa ta lalace. Idan muna yin la’akari da mutane, hakan zai taimaka mana mu rage yin fushi. Ya dace mu yi hakan domin zai sa mu riƙa gafarta wa mutane, tun da yake ba mu san ainihin dalilin da ya sa suka yi kuskuren ba. Littafin Mai-Wa’azi 7:9 ya ce: “Kada ka yi garaje a ranka garin yin fushi; gama wawa ke riƙe da fushi cikin zuciyarsa.” Bai kamata mu riƙa saurin fushi ba. Muna yawan jin cewa da gangan aka ɓata mana rai, amma hakan ba gaskiya ba ne tun da yake mu ajizai ne. Ka tuna cewa ba za ka iya sanin ainihin dalilin da ya sa wani ya yi ko kuma ya faɗi wani abu ba. Ka kasance a shirye ka ƙaunaci mutumin kuma ka gafarta masa, don hakan zai sa ka farin ciki sosai.—Karanta 1 Bitrus 4:8.
‘BARI SALAMARKA TA KOMO MAKA’
11. Mene ne ya kamata mu yi, idan mutane ba su saurari saƙonmu ba?
11 Yaya za ka kame kanka idan wani ya yi maka baƙar magana sa’ad da kake wa’azi? Sa’ad da Yesu ya tura almajiransa saba’in su yi wa’azi, ya gaya musu cewa su yi wa masu gida fatar salama. Ya kuma ce: “Idan ɗan salama yana nan, salamarku za ta zama a kansa: in ba shi, sai ta komo muku kuma.” (Luk 10:1, 5, 6) Muna farin ciki sa’ad da mutane suka saurari wa’azinmu, domin hakan zai sa su amfana. Amma a wani lokaci, mutane ba sa sauraronmu. Mene ne ya kamata mu yi idan hakan ya faru? Yesu ya ce mu kasance da salama. Hakan yana nufin cewa, ko da mai gidan ya yi mana baƙar magana, ya kamata mu bar gidan da kwanciyar hankali. Idan muka yi fushi, ba za mu kasance masu salama kamar yadda Yesu ya ce ba.
12. Mene ne Bulus ya ce mu yi a littafin Afisawa 4:31, 32?
12 Ka riƙa kasancewa da salama a dukan yanayi, ba sa’ad da kake wa’azi kawai ba. Gafarta wa mutane ba ya nufin cewa ka amince da mummunan abin da suka yi ko kuma ka yi kamar abin da suka yi bai ɓata wa mutane rai ba. Amma, yana nufin cewa ba za ka ci gaba da yin fushi ba, za ka yi ƙoƙari ka kasance da kwanciyar hankali. Wasu mutane ba sa mantawa da abin da aka yi musu, kuma hakan yana hana su yin farin ciki. Kada ka yi hakan, domin ba za ka yi farin ciki ba idan kana fushi da mutane. Saboda haka, ka riƙa gafarta wa mutane.—Karanta Afisawa 4:31, 32.
KA YI ABIN DA ZAI SA JEHOBAH FARIN CIKI
13. (a) Ta yaya Kirista yake tara wa maƙiyinsa “garwashin wuta” a kai? (b) Wane sakamako za ka samu idan ba ka yi fushi da wani da ya ɓata maka rai ba?
13 Wani da ba Mashaidi ba ne zai iya ɓata maka rai a wani lokaci. Amma, za ka iya koya masa abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Manzo Bulus ya rubuta: “Idan maƙiyinka yana jin yunwa, ka cishe shi; idan yana ƙishi, ka ba shi sha; gama garin yin haka, za ka tara masa garwashin wuta a kansa. Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.” (Rom. 12:20, 21) Idan ka kasance da halin kirki sa’ad da mutane suka ɓata maka rai, suna iya canja halinsu kuma su yi maka alheri. Idan kai mai fahimi ne kuma kana nuna wa wanda yake ɓata maka rai juyayi, hakan zai iya sa ya koya Littafi Mai Tsarki. Ko da mene ne sakamakon, idan ka kasance da kirki da alheri, hakan zai iya sa mutumin ya yi tunani a kan halinka na kirki.—1 Bit. 2:12; 3:16.
14. Sa’ad da wani ya ɓata maka rai, me ya sa ya kamata ka gafarta masa?
14 Da akwai wasu mutane da bai dace mu yi cuɗanya da su ba. Alal misali, waɗanda aka yi musu yankan zumunci domin sun yi zunubi mai tsanani kuma sun ƙi su tuba. Zai yi wuya ka gafarta wa wannan mutumin, idan kai ne ya yi wa laifi. Wataƙila har bayan ya tuba, abin da ya yi yana ci maka rai. Idan kana cikin irin wannan yanayin, ka ci gaba da roƙon Jehobah ya taimake ka ka gafarta wa mutumin. Hakan yana da muhimmanci domin ba ka san abin da ke cikin zuciyarsa ko kuma yadda yake ji ba. Jehobah ne kaɗai ya sani. Yana bincika zuciya kuma yana haƙuri da mutane da suka yi zunubi. (Zab. 7:9; Mis. 17:3) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta. Ku yi tattalin al’amura na girma a gaban dukan mutane. Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku. Kada ku ɗauka wa kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce wa fushi: gama an rubuta, ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” (Rom. 12:17-19) Shin ya dace ne mu hukunta mutane? A’a. (Mat. 7:1, 2) Amma, ya kamata ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi hukuncin da ya dace.
15. Mene ne zai taimaka mana mu daina fushi da wanda ya ɓata mana rai?
15 Idan wani da ya ɓata maka rai ya tuba, amma duk da haka, yana maka wuya ka gafarta masa, ka tuna cewa shi ma yana da nasa matsaloli. Shi ma ajizi ne kamar ka. (Rom. 3:23) Jehobah yana tausaya wa ’yan Adam domin dukansu ajizai ne. Saboda haka, ya dace mu riƙa addu’a a madadin wanda ya ɓata mana rai. Da ƙyar mu ci gaba da yin fushi da mutum da muke wa addu’a. Yesu ya nuna dalla-dalla cewa bai dace mu riƙe mutane da suka ɓata mana rai a zuciya ba. Ya ce: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a.”—Mat. 5:44.
16, 17. Me ya kamata ka yi idan dattawa suka tsai da shawara cewa wanda ya yi zunubi ya tuba, kuma me ya sa?
16 Jehobah ya ba dattawa ayyuka da yawa a cikin ikilisiya. Ɗaya cikin waɗannan ayyuka shi ne su yanke shawara ko mutum da ya yi zunubi mai tsanani ya tuba ko a’a. Waɗannan ’yan’uwan ba su san abin da ya faru dalla-dalla ba, amma sai Jehobah. Duk da haka, ruhu mai tsarki yana taimaka musu su yanke shawarar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa shawararsu ta jitu da ƙa’idodin Jehobah domin dattawa sun yi addu’a kafin su tsai da shawarar.—Mat. 18:18.
17 Ya kamata mu kasance da aminci a irin wannan yanayin. Shin za ka gafarta wa waɗanda dattawa suka tsai da shawara cewa sun tuba kuma ka ƙaunace su? (2 Kor. 2:5-8) Hakan zai yi maka wuya, idan zunubin ya shafe ka ko kuma wani danginka. Amma, idan ka dogara ga Jehobah da kuma yadda yake magance matsaloli a cikin ikilisiya, za ka yi abin da ya dace. Idan ka yi hakan, za ka nuna cewa kana a shirye ka riƙa gafarta wa mutane.—Mis. 3:5, 6.
18. Yaya za ka amfana idan kana gafarta wa mutane?
18 Za mu amfana sosai idan muna a shirye mu gafarta wa mutane. Za mu samu kwanciyar hankali kuma mu more dangantaka na kud da kud da mutane. Amma, idan ba ma gafarta wa mutane, hakan zai sa mu riƙa ciwo kuma ba za mu samu wartsakewa ba. Yana iya sa ya yi mana wuya mu yi cuɗanya da mutane. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, zai sa mu ƙulla dangantaka mai kyau da Ubanmu Jehobah.—Karanta Kolosiyawa 3:12-14.
[Hoto a shafi na 27]
Wane darasi ne muka koya daga wannan kwatancin da Yesu ya yi?
[Hoto a shafi na 30]
Wajibi ne Kiristoci su riƙa gafarta wa mutane