Ka Tuna?
Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
• Mene ne Allah yake nufi sa’ad da ya gaya wa Lawiyawa: “Ni ne rabonka”?
Sauran ƙabilar Isra’ila suna da gādon ƙasa, amma Lawiyawa suna da Jehobah a matsayin ‘rabonsu.’ (Lit. Lis. 18:20) Ba za su samu gādon ƙasa ba, amma za su samu gatar hidima ta musamman. Duk da haka, Jehobah yana kula da bukatansu na zahiri. A yau, waɗanda suke da gatan yaɗa abubuwan Mulki za su iya kasance da gaba gaɗi cewa za a tanadar da bukatunsa.—9/15, shafuffuka na 7-8, 13.
• Mene ne zai iya taimaki Kirista ya tsai da shawara ko nishaɗin da ya zaɓa zai amfane shi ko a’a?
Don sani ko nishaɗi zai amfane mu kuma ya faranta wa Allah rai, yana da kyau mu yi waɗannan tambayoyi na gaba: Wane irin nishaɗi ne? A wane lokaci ne zan yi nishaɗin? Su waye ne abokaina?—10/15, shafuffuka na 9-12.
• Ta yaya bayanin da ke Misalai 7:6-23 zai iya taimaka mana mu guji kallon hotunan batsa?
Ayar ta ba da labarin wani saurayin da ya wuce ta hanyar da wata karuwa take zama. Sai ta rinjaye shi. A yau ma, ya kamata mu guji dandalin yanar gizon da ke ɗauke da hotunan batsa, kuma yana da kyau mu nemi taimakon Allah kafin ma mu ga irin waɗannan hotunan a Intane.—11/15, shafuffuka na 9-10.