Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 1/1 p. 28
  • Cika Farillar Allah da ke Kanmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Cika Farillar Allah da ke Kanmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Koyar Da Zuciyarka Ta Ji Tsoron Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • “Kaunar Allah Ke Nan”
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Me Ya Sa Za Ka Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kaunar da Ke Tsakaninmu da Allah Za Ta Kasance Har Abada
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 1/1 p. 28

Ka Kusaci Allah

Cika Farillar Allah da ke Kanmu

KA TAƁA tunanin, ‘Ko mece ce manufar rayuwa?’ Jehobah ya halicce mu a hanyar da za mu iya yin irin wannan tambayar, da kuma ɗokin sanin amsar ta. Abin godiya, Allahnmu mai ƙauna bai bar mu cikin duhu ba. Amsar da muke ɗokin sani tana cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ka yi la’akari da kalmomin Sarki Sulemanu da ke Mai-Wa’azi 12:13.

Sulemanu ya ga abubuwa dabam-dabam na musamman a rayuwarsa. Hakan ya sa ya faɗi yadda za a samu farin ciki da kuma yin rayuwa mai ma’ana. Domin Allah ya albarkace shi da hikimar da babu mai irinta, arziki da kuma ikon sarauta, hakan ya sa ya yi bincike a kan abubuwan da ’yan Adam suke biɗa, har da biɗar arziki da suna. (Mai-Wa’azi 2:4-9; 4:4) A ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki, ya taƙaita bincikensa, da cewa: ‘Ƙarshen duk zancen da aka riga aka yi, shi ne: Ka ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.’ Waɗannan kalmomin sun nanata abubuwa mafi amfani da kuma gamsarwa da mutane za su iya biɗa.

“Ka kiyaye dokokinsa.” Tsoron Allah yana sa mu yi masa biyayya. Yin biyayya ga Jehobah tafarki ne mai kyau. A matsayinsa Mahaliccinmu, ya san yadda za mu yi rayuwa a hanyar da ta fi dacewa, kamar yadda wanda ya ƙera wani abu ya san hanya mafi inganci na yin amfani da abin da ya ƙera. Ƙari ga haka, Jehobah yana son mu more rayuwa mafi kyau. Yana son mu kasance masu farin ciki, kuma ya tsara dokokinsa ne domin amfaninmu. (Ishaya 48:17) Manzo Yohanna ya bayyana batun kamar haka: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo.” (1 Yohanna 5:3) Biyayyarmu tana nuna cewa muna ƙaunar Allah, kuma dokokinsa sun nuna cewa yana ƙaunar mu.

“Wannan kaɗai ne wajibin mutum.” Waɗannan kalmomin sun nanata muhimmin dalilin da ya sa za mu ji tsoron Allah kuma mu yi masa biyayya. Yin haka farilla ce a gare mu. Jehobah ne Mahaliccinmu, saboda shi ne muke wanzuwa. (Zabura 36:9) Ya kamata ma mu yi masa biyayya. Sa’ad da muka yi rayuwa a hanyar da yake so, muna cika farillarmu.

To, mece ce manufar rayuwa? A taƙaice, ita ce: Mun wanzu ne domin mu yi nufin Allah. Babu wata hanya wadda ta wuce wannan wadda za ta sa rayuwarka ta kasance mai ma’ana. Me zai hana ka ƙara yin bincike game da nufin Jehobah da kuma yadda za ka sa rayuwarka ta jitu da yin nufinsa? Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka ka yi hakan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba